← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 36

Sashe 6

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ɗakinta ta nufa tana wani huhhura hanci sama,ita ala dole yayan nata ya ɓata ranta, kwanciya tayi saman lafiyayyen bed nata idanunta lumshe, tana son yaƙar zuciyarta akan ta ringa bijirema duk abinda take raya mata, ta sani sarai cewar ita bame sauki bace, ba kuma me ƙyaliya bace ga duk wanda ya shiga gonar ta, sedai in mutum yaga bata tankashi to lallai ya kai ya kawo girmansa take gani,mutumcinsa take gani ko na wani nasa, kamar dai Hajiyar Ahmad da ita ma nashi mutumci da albarkacin take ci da har take yaɓa mata duk maganar data gadama kuma ta kyaleta. Duk zuciyarta take jin a cunkushe badon an mata komai ba sai don kawai dawo mata da kuɗin da Ya Sadeeq yayi. Tana nan a haka har bata san Ahmad ɗin ya shigo har nan bedroom ɗin ba, sedai taji hannunsa a shoulder nata kana ta ankare, zaune ta tashi tana ɗora kanta akan kafaɗarsa bakin nan a tinzire kamar wata ƙaramar yarinya, "Meke faruwa da Rayuwar Ahmad Junaida Haris haka?, wanda me gangancin ne yayi ƙoƙarin taɓa farin cikinsa kuma?" Seda ta haɗiye abinta ke son ɓallo mata ruwa don se da Ya Sadeeq ɗin yace da ita, _Saura kuma in yazo kice masa ga abinda ya faru wacce bata iya kalmasa zance ko kalamanta ba...._. Makut ta sake haɗiye maganar tana tauneta da ƙarfin tsiya kana tace. "Ba kai bane kaki dawowa da wuri ba!, kuma ka dafa min shinkafa farar da kason ban fiye sonta hakan ba...." Jikinsa ya shigar da ita yana cewa. "Wannan shi ne dalilin?, shi ne kuma musabbabin fushin naki Bestie?" Se ya dakata tare da ɗan janye ta daga jikinsa yana kama kunnensa da kokarin sauƙa yayi kneel down, tayi saurin tarosa tana wani famar zazzare fararen idanuwanta. Kana ta kai hannunta samar bakinta tana me furta. "A ah Babyn Baby kayi haƙuri ka kuma rufamin asiri maza su kaini ba mata ba, in ma hukuncin ne ai ba irin wannan ya kamaci ace ka amsa ba, irin haka...." Tayi maganar tana ɗagosa ta kama gefen kuncinsa ta ɗan ciza kaɗan ba da yawa ba. Fuskanta ya ɗan tallafo ya mara marin wasa yana jijjiga fuskan suna sakin dariya kusan a tare. Bayansa ta juya tana ɗurƙusan dashi ta haye bayan wani shauƙin ta hau bayan mijin nata na kamata. "Ohhh Bea bayan yayan naki kikeson ɓallewa ya dena samar na moro ko?, ke baki san kin ƙara lukucewa bane halan...." Tam fa an taɓo ta, don ta tsani taji yace ta fara lukucewa tace masa yaka cewa ta fara zama ƴar duma duma kawai, amma ita ina take son wani girma. Dariya yayi yana cewa "Tuba nake wane ni inji kare da yaga kura maza hau bayan kine, da ma don inyi ta goyaki ALLAH ya min shi ne auki haka...." Gefen kunnensa ta kama ta ɗan ciza tana cewa, "ALLAH Ya Ahmad ɗin nan ka fiye tsokana, za kayi ta zaga gidan nan dani har nayi bacci a bayanka wannan shine hukun cin naka. Dan waro idonsa yayi da riƙe haɓa yace, "Nie kuma in kikayi baccin waye ze kula dani har inyi nawa baccin cikin salamar?" Seda ta cakulkuli wuyarsa kana tace. "ALLAH mana..." Ɗan sakin ta yayi kamar ze kayar ya ce "Naki wayon ban isa ba wllh, kin gama saƙƙo nayi missing ɗumin jikinki duk wunin yau... Se kuma ya wani haɗe rai kamar ba shi ba yana sake furta. "Gaskiya wannan aikin na son shiga haƙki nafa Baby, iyaka jiya da yau har kulawanki ya fara raguwa daga gareni anya zamu seta kuwa da wannan aikin?...." Yayi maganar yana fara tafiya da ita a jikinsa zuwa nasa ɗakin tana cakulkulinsa tana cewa babu abinda ya isa ya shiga ƙarkashin kulawan da suke bama junansu, har suka kai bedroom ɗin nasa, kafin su kai kuwa gaba ɗaya ta gama susuta jikinsa da ababuwan data ringa masa, ga hannunta ɗaya na cikin rigarsa data ziro bayan ɓalle boturan gaban rigan da tayi, don haka suna isa bedroom ɗin suka zube yana fara kunnata itama, duk dai dama a kunnen take, indai zata jita a jikinsa to kuwa lallai babu zaman lafiya a gangar jiki da ruhinta, har se sun ziyarci juna. Amma se ta fara masa rakin ita ya kyaleta ta gaji da yawa ƙafafunta sun yi tsami, ko ta kanta be bi ba yaci gaba da abinda yake har se da yaji shi ontop kana ya sarara mata yana janyota jikinsa ya shigar yana sauƙe mata numfashinsa me ɗumi a gefen wuyarta, ita kuma ganan shatin kwanciyar hawayen da suna dinga gangaro mata. Sedai suka jima sosai kafin su tashi su tsaftato jikinsu kana suka dawo suka kwanta, bayan sun san gyaggara gadon. Can gabanin asuba ya sake nemarta inda taso zamewa ta gudu amma ya sake nuna mata bata isa ba, haka ya sake biyar buƙatansa da ko Sallah yau ɗin ma wuce su tayi, karfe shida saura kana ya ja su Sallah'n. Aikuwa tayi kwanciyar ta taƙi fita musu dinner murmushi kawai yayi yana fita yaje ya soya musu bread da kwai. Da ruwan bunu, koda ya dawo seda ya fara yo wanka kana ya tadata yace ta fito suyi dinner karta makara. Wankan tayi itama sama sama kana ta fito cikin wata ash jallabiya ta mata, wacce ta amshi surar jikinta kwarai, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ta zauna sukayi dinnerh ɗin, seda suka kammala tsaf kana ya fuskanceta yace. "Yanzun yauma fisabilillahi Meenal yau ɗin ma haka zaki fita?, anya kuwa kina son ci gaba da fita wannan aikin naki?" Tsaye ta miƙe tana dubar shigar nata kana tace. "Haba Ya Ahmad mana, kar ka neda kanka wani ɗan kauye mana, yanzun miye laifin shigana don ALLAH? Se dai in kaine ba ka son zaman lafiyan...." Daga haka ta suri jakarta tayi waje fuuuuu.... Da wani kalan daskararren kallon mamaki al'ajabi rudu ya bita. Kafin yayi ƙarfin halin miƙewa tsayen shima ya bi bayanta, sedai me wayam babu ita har ma ta fice kenan?... Duk yacce zuciyarsa taso ingizo hasalarsa fili kin yadda da hakan yayi, yana ajje ta a matakin mata uziri ne kawai. Don haka yama motarsa key ya tashe ta yana fita daga haraban gidan. Sedai kome kama da ita a hanyar be gani ba don haka yayi wucewarsa gun nasa aikin tin da yasan ita ba yarinya bace, ta kuma san inda ta nufa, haka ya tafi yana ta tunanin sabbin halayenta daga ranar fara aikin nata zuwa wayewar yau da yake na uku a fara fitan nata, a cikin zuciyarsa yake ayyana lallai da akwai matsala kenan indai har tace a haka zasu ci gaba da tafiya. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauƙe yana karanto Hasbinallu wani'imal wakeen...
Chapter 6 · 0% Book details