Sashe 22
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunanin wannan police É—in ya dakata ne daga lokacin da wannan macen police É—in take fitowa da Meenal É—in,
ɗago ƙananun idanuwansa da suke a matse kamar na ƴan Japanese yayi, yana sake tsayar da kallonsa akan Meenal ɗin da lokaci guda harta sanja saboda mummunar halin da take a ciki, ga yunwa da ƙishin da suka gama wajigata. Wata nannauyar ajiyar zuciya police ɗin yayi ganin kamar Wada damar ce ALLAH ya kawo musu, masu ƙarfin ikon faɗa da nera biyu sun haɗu akan case guda ɗaya, se yake jin a ransa cewar hakan ma kamar dama ce ALLAH ya kawo musu ta yanda zasu jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu a wannan gaɓar. Da wurin zama ya mata nuni yana sassauta zuciyarsa akan tsananin son abin duniyar da yake da. Zama tayi a inda ya nuna mata ɗin tana ta baza idon taga ta inda Mijinta ko Yayanta a cikinsu wani zai ɓallo, don tasan kaf duniyar babu masu zuwa wurinta daya zarta su. Se dai zama da kamar 30 minutes ɗin da tayi bata ga kowannensu daga cikin su ne ya sakata ɗaga kanta ta kalla police ɗin dake tsaye, mamakin Mutumin da kuma jin kansa na sake kashe sa, ehhhh mana ai dole yace jin kai mana yace a fito masa da yarinya kuma ta fito sama da 30 minutes be ce mata komai ba. Ta buɗe baki kenan da niyar tambayarsa a ina wanda ke ƙirar nata ya wani ɗago kansa yana wurgama Police ɗin wani mugun kallon da ko be buɗe baki yayi magana ba, idanunsa kawai sun isa isar da hukuncinsu ga mai laifi, don haka tin kafin ya furta masa wota magana ya bar wurin. Don kai tsaye ya gane spece or balance yake nema daga gare shi. Gabanta sosai taji yayi mummunar wata bugu da ganinsa kawai, me ya kawoshi wurinta?, miye kuma haɗinta dashi?, ama ina yasan tana nan ɗin, ko kuwa ya sake biyota har nan ɗin ne don ya sake wulaƙantata kamar ranar?. Maganar sa ce da wannan No nonsense muryan nashi ya sakata dakatawa cak daga tunanin nata.
"Me ya sa kika biyosu?, bayan mijinki da yayanki sun yi ƙoƙarin baki kariya?"
Haka maganar nashi ya sake dakar tsakar kanta da yake mata wani kalan mugun ciwon da take jin har kamar zai tsage gida biyu. Komai bata ce masa ba saima saka hannunta da tayi ta dafe goshinta da nufin ko zata ji sassaicin abinda ya riƙe mata kan, amma kuma sai taji ciwon kamar a tsakiyar kan yake, wanda taji kamar ma ba ciwon yake ba, kamar wuta ce ake hurawa a cikin kan nata da zafin ta yake saka gumi tsiyayowa daga cikin gashin kanta zuwa fuskar da ilahirin jikinka. Ba ciwon kan ne ya fi damunta ba, ciwon da zuciyarta ke mata ne yafi addabarta fiye da komai, se kuwa zafin kalamansa da tambayar daya mata ke sake taso mata, suna son wargaza sauran jarumtar da take jin tana da. Wani irin zafi take ji na taso mata daga cikin ƙarƙashin tsakiyar ƙirjinta irin mai kama da ƙaiƙayin nan, gashi tana lullube a ƙirjinta dan haka babu damar ta sosa ta bare tayi tsammanin samun sassauci daga suka da ƙaiƙayin da take matan. Don haka ta saka ɗayan hannunta ta dafe zuciyar tare da yin ajjiyar zuciya da nufin ko zata sama sassauci ko wani rangwame daga azabar da zuciyar ke mata amma sai taji tamkar kara kaikayin ne ma tayi....
A matuƙar jigace ta mike tsaye tana dafe da kan nata ta dube shi tare da cewa. "Stop it!, da duk wata baƙar maganar data saura wacce baka gama gaɗamin ma, domin a yanzun wannan zuciyar ba zata taɓa iya ɗauka ba ka temaka ka tafi ka barni Please!!!...."
Shima tsayen ya miƙe ba tare daya kalla inda taken ba ya wani gumtsi iska ya kuma fesar duk a lokaci guda kafin ya wani furta. "Damn it!" ya fada da karfi
sannan ya koma ya zauna a inda ya tashi yanzun. Kafin a natse ya dubeta tare da magana kai tsaye akan case ɗin da take cikinsa. Wani irin hope taji ya sake ratsa zuciyarta da jikinta don haka kai tsaye tace bata buƙatan taimakonsa yaje ya riƙe abin sa, amma ita a wurin mahaliccinta take nema, Ganin kamar zata bashi wahala ne yasa shi faɗa mata wata baƙar maganar da dolen dole yake da tabbacin seta amayar masa har fiye da abinda yake buƙatar ji daga gare ta, don yaga za tayi mugun taurin kai yarinyar. "Kar kiyi tunanin zan tsaya ɓata lokacina ne akan mace mara kima da daraja irin ki, me take dokokin ALLAH data aurenta, ki sani na shigo cikin maganar ne domin kawai a cikin asibitina case ɗin kisar ta faru, badon haka ba ke kin ma isa ki tsaya ko inuwar dana tsaya balle har kiyi tunanin raɓarta? IDIOTS....." A lokacin daya gama yaɓo mata maganar kuwa har bata san lokacin da jikinta ya soma rawa ba, duk yanda taso jurewa kuwa gazawa tayi ga hannunta ɗaya daya soma rawa. Ta riƙe hannun da ɗaya hannun da niyyar bashi kariya amma sai suke rawar a tare. Wannan ya saka ta haɗesu duk biyun ta rungume a ƙirjinta tare da jan dogayen numfashi sau uku ta hancinta, tana sakin ajiyar zuciya da niyyar calming nerves ɗin ta down ko dan ta sama damar ce masa yaje ta amsa hakan za kuma taci gaba amsar kowanne irin hukunci daga mahaliccin tane. Idanunta ta runtse tare da kokarin goge hawayen da kai tsaye taji sun zobo mata, wanda a daren jiya tayi tayi ya zuba yaƙi, se a cikin zuciyarta ya dinga kwarafniya, fara goge hawayen tayi amma wasu suna sake yin replacing ɗin kan su gare ta.... Abinda kawai take hangoma kanta a cikin idonta shi ne girman laifinta ga mahaliccinta da kuma Mijinta, fuskar Ya Ahmad da Ya Sadeeq ɗin ta kawai take hangowa a yadda ta baro su a tsakiyar compound na gidanta, don haka take jin ba zata taɓa barin zuciyarta ta yaudareta akan wani daban ba kuma, shi dama bata gama sanin ko shi waye ba?, daɗi da ƙari Ita Matar Aure ce babu hurimin wani yace zai shige mata gaba akan lamarin da ya faru da ita. Don haka cikin kwarin gwiwa ta soma tafiya ta barshi, Saboda aganinta hakan shi ne dai dai, hakan shi ne zai fi alkhairi gare su, barin ma data shafa cikin jikinta da
shi ne silar komai,wanda zata iya rantsewa kamar motsinsa taji a karon farko ya mata....
Kuɗi sosai ya bama tarin police ɗin a matsayin na belinta da yayi har zuwa lokacin da za'a yi shari'an ba tare da sanin taba, kana yace idan har wani abu ya sameta koda kwarzanene se yayi sanadiyar rasa aikinsa, rasawa kuma ta har gaban abada kamar dai yacce Dpo ya tsammata ɗin kuwa. Daga nan ya wuce babu jimawa se ga Ya Sadeeq da Dr BILAL ya sanar dashi inda take ya kuma je anyi belinta. Lokacin tsaƙiyar ranace don irin sha biyu da rabi ɗin nan ce, gashi kuma ba laifi an tashi da ranar. A karo na biyun da akace ta fito cewa tai ta yafe ko waye. Har seda wannan mummunar baƙin police ɗin ya bayyana a gabanta kana ta nutsu ta kuma fito, ganin yayan tane ya sakata shigewa jikinsa kawai tana sakin kuka. Lallashinta ya shiga yi kafin ya jata ya zaunar kan wani plat chiar dake wurin, ruwa ya ɓalle ya bata da kuwa ta kafa kai bata janye gorar ba har se da ruwan ya ƙare, kana ya bari ta nutsu sosai kafin ya sama napep su wuce gida kai tsaye, ganinta ya kwantar da hankalin Baffa ba kaɗan ba nan Baffan yasa Bilkisu ta dafa mata ruwan wanka me ɗumi, har ban ɗakin dake tsakar gidan ta kai mata ruwan bayan ta dafa mata, wanko tayo sosai da gasa jikinta da kyau, kayan Shareefah ta saka jallabiya se kuwa gashi tudun cikin ya ɗan bayyana ta cikin rigar. Haɗe kanta da jikin gadon kawai tayi tana jin yadda zuciyarta ke tsanar cikin dake jikin nata kai tsaye da kuma ƙaunarsa na kasancewar a jikinta yake, haka duka abu biyun suka haɗe mata tsana da ƙaunar cikin jikinta,wanda ita dai ko a tarihin rayuwa bata taɓa jin SO da TSANA sun dirarma mutam lokaci guda ba se a kanta, shigowar mahaifinta dakin ne ya sakata sese ta natsuwarta tana zama daga ƙasan wurin. Cikin taushi da kuma lausasa murya ya dubeta cike da wani kalan matsanancin tausayinta me girma a gareshi, domin kusan ze iya cewa ita ce zuciyarsa kai tsaye. Don haka komai da zai shafi rayuwarta yake jinsa me girma na kuma daban a cikin rayuwarsa. Ahankalin cikin taushin murya yace.....