← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 36

Sashe 2

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

ꨄ Tsaye Matashiyar matar da kai tsaye zamu iya ƙiranta da ƴar kimanin shekaru ashirin da biyu, take gaban Madaidaicin mirrorn ɗakinta me kyau da tsari, wanda yake a gyaren da kallon farko zakama ɗakin da wacce take tsaye gaban mirrorn ka tabbar da cewar me tsafta ce, tun daga yanayin yadda ɗakin nata ke a tsaftace tsaf, jikinta kuma na ɗaure da wani blue towel se faman shafe shafe take yi kyakkyawar fuskanta, wacce take ɗauke da zallar farin cikin fitanta aiki na farko yau da zata fara, wanda kai da ganin yadda take cikin farin cikin zaka tabbatar da cewar lallai wannan aikin nata me girman matsayi ne a cikin ranta, soson powdern dake hannunta take sake goggawa chocolate ɗin fatar fuskanta, wacce ta zarta mu ƙirata da baƙa sedai bata kai mu ƙirata da fara ba kuma, wannan dalilin yasa muka bata chocolote ɗin kai tsaye. Lipstick ta sake ɗauke tana gogoma lips nata wanda take suka ɗauki shining na kyau da sheƙin abinda aka goga musun, eyeliner ta sake ɗauka tana gyara eyelashes nata again kuma tana ci gaba da gyara duk abinda be mata ba, har zuwa dogon wuyanta shima da take sake gyareshi da soson powdern. Ta ɗan ɓata lokaci me nisa a nan tsaye a wurin, kafin ta miƙe ta nufa gaban wedrop nata me shida, irin me madubi da katifar nan ba laifi suma sun yi kyau babu ƙarya, kayan ta shiga bi da ita tana research da idanunta na wanda ya kamaci ace ta saka, haka har idanunta suka sauƙa akan wata lafiyayyar abayarta black, wacce take ta cikin kayan lefenta ce kuma bata taɓa sakata ba, don haka kai tsaye takai hannunta tana tare kayan dake ƙasa da sama kasancewar rigan itane a tsaƙiyan kaya, ahankali ta janyota bayanta ta ɗan gyaggyara kayanta da suka zamo wosu kuma suka yi ciki. Zame towel ɗin dake jikinta tayi bayan ta zira wata sitred riga daga jiki linor, kana ta ɗora abayar tare da komawa gaban madubi tayi Rolling kanta da vail ɗin da bai kai ya kawo ba na abayar, tsaf kuwa tayi kyau ta kuma karɓu cikin shigan daya mata wani kalan kyau na musamman. Turaren dolcy nd gabbana ta feshe ilahirin jijinta dashi, kana ta wuni nufi ƙofa tana taku ɗay ɗay kamar bata taka ƙasa ba, tin kafin takai ƙofar parlourn ta take famar kwala ƙiran.

"Baby!Baby!!Baby!!!"

Tana ci gaba da tunkarar ɗakinsa tana sake tunkaro ƙofar bedroom nashi, tana ci gaba da mitar ta "Haba Baby har yanzun baka tashi bane mun makara fa?" Tayi maganar tana wani ɗan zazzaga parlourn irin a matse ɗin nan take, "To wllh sedai ka biyo napep don Wllh nidai tafiyana zan yi....." Takai ƙarshen zancen nata tana kaiwa zaune saman kujerarta me kyau, ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani jijjiga jiki. Babu jimawa sega takun tafiyarsa nan na tunkaro inda take zaunen, zama yayi kusa daf da ita yana ɗan kishin gida daga zaunen da yakai, fuskansa da murmushi sosai ya ce. "Kai My luv yanzun duk wannan zumuɗin fara aikin ne haka?, to yanzun dai a taimakeni da abinci don yunwa nake ji...." Fuskanta ta saki kaɗan tana miƙewa,babu jimawa se gata ta dawo hannunta riƙe da cooler na abincin data yi tin farar safiya, ajje musu tayi tana buɗe cooler'n kai tsaye ƙamshin couscous ɗin data ma lafiyayyen haɗi na dukar hancinan su. Wani ɗan lumshe idanunsa yayi yana sake jin ƙaunar matar nasa na sake bebeye shi, ta iya komai na cikin rayuwa tin daga kama kan kula da kanta, Mijinta, cikinsa, haƙƙinsa, da duk wasu al' amura nashi. Saƙƙowa yayi yana me furta. "ALLAH yama Meenoh na albarka, ya saka miki da gidan aljannarsa mafi tsada..." Wani kallo ta masa wanda ya saka shi kusan sarƙewa da yawun da ya taho kai tsaye daga cikin maƙoshinsa, don shi kaɗai yasan iriyar masifar ƙaunar da yake ma wannan baiwa tashi, gaba ɗaya jinta yake a ko ina na jikinsa, jinsa yake daga kanta ya gama aure IN SHA ALLAHU, domin duk abinda yake so yi masa take kai tsaye babu shamaki, a natse sukaci abincinsu cike da ƙaunar junansu... ruwan swan suka sha me sauƙin sanyi kasancewar ita da kanta ta saka musu dokar hana shan ruwa bame sanyi ba sosai, daga nan ya miƙe yana ce da ita _just 15 minutes_ kanta ta ɗaga mishi tana sakar masa murmushin daya kusan kashesa da ransa, da yar sassarfa ya nufi bedroom nata don babu jimawa kuwa se gashi ya dawo sanye cikin tattausan shigar shadda brown color, wacce ta masifar amsar nasa jikin, don sosai daga ita har shi suke da wani irin sahihin kyau me sanyi da nutsuwa, ba wai irin me ɗaukar hankalin nan... Kallonta yayi daga sama zuwa ƙasa ganin yacce ya tafi ya barta haka take, don haka yace "Baby ya naga ke baki shiryo bane?" Kallonsa tayi ta kuma kalla shigar dake jikinta tana miƙewa tsaye, tsadaddar wayarta me ƙirar _TECNO POP 9_ ta ɗauka tana cewa. "Kaga muje don ALLAH Ya Ahmad lokaci na ƙurewa kaga wannan shi ne karo na farko kar inji a makare...." Tayi maganar tana ƙoƙarin ficewa a parlourn, hannunta ya ɗan jawo yana dawo da ita baya, cikin komawa seriously nashi yace. "Yanzun don ALLAH Meenoh ke idan na ƙyaleki seki fita a hakan?" Cikin yanayi na ɗan fusatuwar data soma tace. "So what idan na fita a hakan Ya Ahmad?, kalla ka gani a suturce nake fa!, ko kuwa illa ka gani tattare da shigan dake cikina?, ya zaka fara abu kamar wani wanda be waye ko ya shiga class ba?" Ta ƙarasa maganar tana fita a ɗan kamar fusace, da sauri ya biya yana bama zuciyarsa hakuri akan cewar wannan ɗin ba komai bane sharrin shaidan ne. Lokacin da yake fitowar kuwa har me gadi na ƙoƙarin buɗe mata get zata fita ta tara napep, saurin dakatar dashi yayi yana isa ya kamo hannunta cikin nasa yana kallar tsaƙiyan cikin idanunta yaje... "Oya les't go!, ko in na barki kin fita ke kaɗai kinsan hospital ɗin ne?, kuma wurin wane zakije?..." Se ya ɗan shiru daidai lokacin da yake buɗe mata gefen me mazan banza a motar, shi kuma yana komawa driver sit ya zauna, Ahankali yakai hannunsa yana lakatar dimple nata da yake gefe guda yana cewa. "Bestien Besty rigima..." Daga haka yaja motar tasa me ƙirar GLK bugun 2025/2026 suna barin harabar gidan, hannunsa na cikin nata ɗaya yake driving ɗin wa'azin Marigayi *SHEIKH MUHAMMAD AUWAL NASEER ALBANY ZARIA* Na tashi a cikin motar me suna *IN KASAN WATA* Sabo da sosai yake son wa'azin Malamin, sabo da matuƙar feɗe gaskiyar sa da yake yi.... Haka har suka isa katon private Hospital ɗin da anan ne yayi duk wasu cuku cuku ya nema mata aikin nata, tin da suka shigo cikin harabar asibitin take kallar tsari da yanayin ta aka tafiyar da ginin wurin kawai na yi mata hundred percent. Ci gaba da bin komai da ido tayi a cikin zuciyarta tana ayyana lallai Ahmad na manyan mutane yana kuma da hannu da manyan, in banda hakan ta yaya ita AMEENERH SHEHU USMAN ta taɓa zata ko tsammatar cewar zata taɓa aiki a ko me kama da wannan asibiti ne, amma se gashi sanadiyyar Mijin nata yau wai ita ce da aiki a wannan tsadaddar asibitin da a da sedai ta hangeta daga nesa nesa, wanda koda a tunani bata taɓa kawo cewar zata zama ɗaya daga cikin ma'aikatan asibitin ba, don ta san cewar ko aikin zatayi tofa sedai ta ƙare a na gwamnati, wanda inta sama aikin ana gwamnatin ma kenan ita nata yayi kyau, amma se gashi yau ata sanadiyyar Mijin nata yau gata a matsayin ma'aikaciyar asibitin, Ikon ALLAH fa kenan, Lallai ta sake yarda cewan Ikon ALLAH shi ne gaba da komai. Wata doguwar ajiyar zuciya ta kawo lokacin da yake farkar da ita daga tunanin data ɗan shilla. Ƙafanta dake cikin wani vk shoe ta fara zirowa me laushi sosai plat me kalan jikin miski, kafin ta fito a natse tana buɗe kofofin hancinta ta shaƙi iskan cikin asibitin da kyau idanunta a lumshe, zagayowa yayi daga mazaunin nasa yana dawowa ta setin da take, tare da kama murfin motar ya zuba mata kyawawan idanunsa, wani numfashi ta ɗan shaƙa tare da buɗe idanunta tar kuwa se akan Babyn nata, wata iska me ɗan nauyi ya fesar yana sarƙe hannunsa a ƙirji tare da sakar mata da wani tsadadden murmushinsa me kyau. "Les't go idan DR. Meenerl ta gama abinda take yi...?" Taji muryan mijinta abin sonta da bata taɓa haɗa shi da kowa, wanda suke yau kimanin watanni Bakwai kenan da aure, amma idan ka kallesu zaka iya shan cewa sun kai irin fin shekarun nan ne a auren, bawai don zaka gane hakan bane ata siffar jikkunansu, A ahhh sedan ta iriyar shaƙuwar dake tsakanin nasu, amma kai idan har ta suffar jikkunan nasu ne tsaf zaka iya ƙiransu ma budurwa ne da samrayinta. Fitowa tayi suna jerewa a tare suka soma tafiya suna ƴar firarnsu suna ƙaramar dariya ƙasa ƙasa, duk wanda suka haɗu dashi a hanyar kuwa seya sake waywayensu koda ya wuce, don yanda suka matuƙar dace da juna. A gaban wani babban office suka tsaya yana zaro wayarsa ƙirar iphone ya saka ƙira a wata number, wayar second yayi yana datse ƙirar, babu jimawa sega wata nurses ta ƙaraso tana musu iso, gaba tayi suka take mata baya har zuwa babban parlourn dake cikin office ɗin, ruwa da lemu ta kawo musu tana ajjewa gabansu bayan ta sake gaidasu, fita tayi ta wata ƙofan daban can kuma babu jimawa sega wani hamdsome guy ya fito sanye cikin labcoat na likitoci sky color, wuyansa rataye da Patient screening hannunsa cikin handglov kansa da surgical cap, zama yayi kujeran dake fuskantar su fuskansa da murmushi sosai, "Barka da zuwa abokina, na ɗan ɓata muku lokaci ko?" Yayi maganar yana miƙa masa hannu tare da sake cewa yayi hakuri wata Surgery ce ya shiga ta gaggawa, "Ba komai DR BILAL" yace masa yana dawo da dubansa kan Meenal. gáidashi a mutumce tayi duk da bawai ta san shi bane ko ta taɓa ganinsa da mijin nata, bayani ya masa game da cewar ita ce Meenal ɗin. Kansa ya ɗan shafo yana cewa "Okay to Ma sha ALLAH, zamu duba mu gani duk dai takaddun nata da kyau, amma duk da aka zan sake gwada ta ko na mako guda ne. Kuma daga gobe In sha ALLAHU zata fara zuwa, yanzun kuma za'a mata interview ne..." Yay maganar yana jan landline ta parlourn ya saka ƙiran wata babbar likita, babu jimawa wata gaggaɓar mata ta iso, nuni ya mata da Meenal yana ce da ita, "Dr pooja jeki da Meenal zaki mata interview a fannin surgery...." Cikin harshen turanci ya mata bayanin kasancewarta Christian ce, fuskanta da yanayin da murmushi me kyau ta kama hannunta cewa "les't go My freind!" Murmushi ta nata tana mara mata baya suka fita, shi kuma suna yin hannu yace zai je wurin aikinsa don har kamar ma yayi late. Har parking car's ɗin DR BILAL ya raka AHMAD....
Chapter 2 · 0% Book details