Sashe 29
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zaune suke a lafiyayyan palourn gidan nasu kusan dukansu , tin daga kan Ikleemerh Ummiensa,Daddy se Dr Bilal shima, kusan tin da suka zaune kowa shi kaɗai ake jira ya fito su fara dinner, amma haka suka share fiye da fin 30 minutes a zaunen da suke zamar jiransa, ita kanta Ayla ta gama matsuwar Papa'n nata ya fito, sedai hakan be sa ya fito ɗin ba, wanda har ƙiransa a waya se da Bilal yayi amma wayan a kashe, don haka Daddy kawai ya basu umarnin su fara cin abincin nasu kawai, Ɗan saurin kallon Daddy'n Ummiensu tayi jin yace su fara cin abincin wai, wacce take sanye cikin wani mayen lace ruwan ƙasa, an masa zane zane da sky sak mai matuƙar tsadar gaske wacce ta haska farar fatar ta, wanda kallo ɗaya zaka mata kasan cewar ita ɗin ba baya bace wajen tattali da kuma tsaftar jikinta, wacce zata kai shekaru 45/47 haka, Amma jikin ta bai nuna ba saboda tana da jiki nai kyau ga kuma uwa uba kulawar da yake samu, wanda kai tsaye ma ba ka isa cewar ita ne ta haifa wannan zabgegen matashin magidancin kamar Majeed ba. Shima kallonta Daddy'n yayi yana sakar mata murmushi mai cike da SO ɗin nan, "Afwan ummien Majeed, wato nace kar mu jira shalalenki shi ne kike wani tsare ni da ido" yayi maganar yana kallonta da itama take sake mayar masa da martanin murmushin tai tana masa wani kallo na ƙasan ido. Wayarsa ya ɗauka kai tsaye yana dokama Majeed ɗin ƙira, kai tsaye ya bashi umarnin ya fito ƙasa shi kaɗai suke jira, wani yamutse fuskarsa yayi shi fa badon Daddy bane da kansa ya ƙira shi wllh da babu inda yay niyar zuwa, bare wani cin abincin da sun san ba woni ci sosai yake ba, don ze iya fita yaje ya dawo ma ba tare dako ruwa yasha ba kaɗan kenan daga cikin aikinsa. Tamkar wanda yake gabansa haka Daddy'n ya gyaɗa kai kawai yana maida kallonsa ga ummien yace "Se a dai na min wani gani gani kuma ko Hajiya na ƙira Shalelen naki" ba'a ɗau wani lokaci mai tsayi ba kuwa suka fara jiyo takunsa daya ratso palourn, don haka tamkar wani bako ko wanda basu taɓa gani ba gaba ɗayansu suka zubama ƙofar shigowa palourn ido duk da kuwa sun san ko waye zai shigo ɗin kuwa.
Cikin takun dake nuna ko a jikinsa ya shigo palourn, yana sanye da riga da wando masu taushi brown colour, saidai rigar irin armless ɗin nan ce ga ta kuma ya ɗan buɗe botir na gaban rigar guda uku, wanda hakan ya bayyana ƙirjinsa a waje, ƙafarsa sanye da versace slipper's masu taushi irin room parlourn nan, cikin takun jarumta ya karaso tsaƙiyar palourn bayan ya cire takalmin sa daga bakin grass carpet ɗin dake tsaƙiyar dining ɗin, binsa da kallo ummie tayi tana girgiza kanta ganin yanayin da har zuwa yanzun yake a cikin bame kyau bane, a natse yakai zaune kan farar chiar ɗin data saura yana me furta. "Evening Daddy" ba tare daya jira amsar saba ya juya ga ummien nasa ita ma yace "Evening Ummiena" kana Ikleemerh da Ayla suka shiga rige rigen fara gai dashi, ɗan hararansa Dr Bilal yayi yana kallon Daddy yace..
"Wato ni ka gama rainani nine ba zaka gaida ba ko?, Daddy Don ALLAH ban fi wannan yaron ba???." Dr Bilal ɗin ya faɗi yana wani turo bakinsa gaba, wanda yake ɗan gidan yayan Daddy'n ne, sedai iyayensa basa Nigeria suna Istanbul..... Wanda shi kuma kishin Majeed ɗin ne yasa yafi son zaman nan ɗin fiye da can, Wani kallo Majeed ɗin ya wurga masa kafin ya shiga motsa bakinsa kamar wanda ke tsoron yin maganar yace... "Koma dai miye ni ban yarda ba, sabo da karka manta ni har budurwar Ƴa gareni ƴar five year's wacce take ƙoƙarin shiga ta 6, ga kalla kuwa ta ina zan yarda cewan ka fini???.... Kuma ai ko makaho ya laluba yasan daidai, dan ubanka Yayan Fahaad shi ne Sa'a na bama Abdul-maleek..." Yayi maganar yana wani yamutse fuska kamar yaga kashi, kana ya shiga duba apple watch ɗin dake ɗaure a tsintaiyar hannun sa na hagu ganin pass 9 na ƙoƙarin shigowa ya kalla Daddy'n nasa da su har sun riga sun fara cin abincinsu yace "Zan iya tafiya?" Bayan yasha apple juice kawai. Shi dai Bilal in banda aikin hararansa babu abinda yake. Girar sa ta hagu ya ɗan sosa jin Daddy'n yace babu inda zai tafi sau yaci abinci, gwalo Bilal ya masa daya saka Majeed ɗin ɗaukan robar da yasha apple juice ɗin ya jefe shi da ita, kare jifar yayi da hannunsa yana dariya yana cewa ai ba shi yakar zomon ba... Da kyar ya iya cin kaɗan don a cunkushe yake jin jikin nasa kana yasha ruwa ya mike bayan yama Ayla peack a goshi, don yau itama ko ƴan maganar bata samu ba, wanda itama yarinyar ta san duk wani motsi nashi don haka se baya woni takura masa ba.... Kai tsaye ya mike ya nufa samar sa. Binsa da kallo cike da tausayawa ummien tayi, a ranta tana adda'ar ALLAH ya kawo ma ɗan nata mafita da ɗaukinsa.... Ayla da har ta fara bacci Ikleemerh ta ɗauketa suka wuce dakinsu, sallama Dr Bilal ya musu shima yana nufar nasa ɓangaren da yake guda shima.
MAJEED
Drectly yana isa ɓangaren nasa yakai zaune kan wata ƙerarriyar silver chiar. Yana kwantar da kansa da jikin kujerar, lallausar rigar amrless ɗin dake jikinsa ta wani lafe a dark shiny skin nashi, wanda kai tsaye ke bayyanar da asalin hutu da luxurious life ɗin da yake cikinsa. Fuskar nan kai tsaye dake bayyanar da kwantacciyar damuwar da yake a cikinta, tin daga lokacin daya fara ɗora idonsa a kanta. System ce a gabansa ya zuba mata fararen idanuwansa, wanda a zahirin gaskiya bawai kallon system ɗin yake ba ya tafi ne duniya irin ta tunani.Wani zazzafan numfashi mara sauti ya fesar jin,yanda zuciyarsa ke ci gaba da sake karta masa a karo na ba adadi. Gaba ɗaya kansa nemar juye masa yaje da tunanin Ameenatou ɗin sa, wacce har gaban abada yake jin bazai taɓa iya haɗa sonta dana ko wacce mace ba, duk wata macen da zai so to ta biyo bayanta.
Duk da cewar Ƙaddara ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar ƙaddararsa, ta raba su rabuwa kuma irin ta har gaban abada ɗin nan , Wani gauron numfashi ya kawo yana sake zubama laptop nashi farare ƙal ɗin idanuwansa. Pisc na ameenatou ne tare dashi da sukayi a Goa bakin wani gaɓar ruwa, ga ɗan ƙaramin matashin cikin tanan daya bayyana tana sanye da wata faffaɗar rigar slik fara me kyau, da wando ash me faɗi shima kanta da farar hura daya zame sosai, ganan kwantaccen baki wulik ɗin gashinta ya bayyana da yake har gaban goshinta. Farar fuskarta me kyau ɗauke da murmushin da baya taɓa mantawa dashi, wanda suna shan ice cream ne ta shanye nata shi kuma yana cikin shan nashi ta warce masa tana masa gwalo fuskanta ɗauke da wadataccen murmushin ta me kyau, da komai da komai kalan nata ne Ayla ta ɗauko,duhun fatarsa ne kawai kega yarinyar farin ne kawai na uwar bata dauko ba, se maganan da suke sakk irin nashi da baki bakinta.... Pisc ɗin yake kalla a cikin laptop nashi idanuwansa har kalan bala'i bala'in yaji suke mai na tsananin damuwar da yake son cusama kansa, yasha zama irin haka idan abun duniyar suka ishe sa har kusan saɓo yake wani sa'in, amma kuma idan yay duba da yadda Ubangiji ke juya
lamuransa daga kyawawa zuwa munana se ya sake jinjina lamari na ubangijin da babu kamarsa a duniya, dan kuwa shine kaɗai wanda ya isa yayi abinda babu wanda ya isa juya hakan. dan yana da tabbacin idan wani na juya ƙaddarar wani da tuni ya jima da fara juya nashi ƙaddarar, yasan kaf cikin duniyar nan ya tabbata babu abinda ya rasa a rayuwarsa se ita, se sauran mataye biyun da suka bayanta ma wato Ramlah da kuma Fareedah. Se dai wannan maganar ta *TUN RAN GINI* da tsarin ƙaddararsu ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wanne bawa nashi, amma duk da haka bazai gajiya ba wajen kaima ALLAH kukansa kan kawo masa mafitarsa cikin wannan hali da yake ciki. Janye fararen idanuwansa da sukai ja yayi a kan laptop ɗin a sanyaye kuma ya maida ya rufe yana sauƙe numfashi me zafin gaske, kana ya nufa bathroom,wanka yayo yayi nafila kana ya kwanta zuciyarsa cike da sake saken ababuwa.... Har besan lokacin da wani nannuya wahaltaccen bacci yin gaba da shi ba....
Meenerl....