← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 36

Sashe 10

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana zaune duk a parlourn ya gaza tabuka komai, ko ta kan ƙiranta be bi ba duk da cewar yaga miss call nata wajen uku, amma se bi ba, ga zuciyarsa dake bugawa time to time da tsananin karfi. Yana nan a zaunen wayar ya sake shigo masa, lokacin ma an ɗan ja lokaci sosai akan baya, don haka ya rarrashi zuciyarsa ya ɗaga din tana daga zaunen, sedai jin muryan wani da daban saɓanin Meenal ɗin ne ya saka shi furta "Lafiya kuwa?" Daga ta can ɓangaren aka ce "Kai ne Mijin me wannan wayar ne?" Cike da tsantsan tashin hankali ya ke cewa... "Ehhh ni ne wllh ni ne wani abu ya faru da ita ne?, accident ta samu ne....?" Daga ta can aka sake ce dashi dama mun kwaci matar kane hannun wasa yara a gefen titi sunyi mata fyaiɗe...... Yanzun haka tana kwance a asibitin da take aiki...." Wani kalan zabura yayi yana ja da baya ya miƙe ya na cewa.... "Eyeeee Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³ fyaiɗe???...." Kafin ɗif ɗif ya datse ƙirar wata juwa da jiri na kwasar shi da Hajijiya....

*Around 4:20 Pm*

Ahankali slowly ta shiga buɗe idanunta da taji sun mata nauyi loƙaci guda, ɗan lumshesu ta sake yi tana ƙoƙarin saita kanta da dawowa cikin sense nata, ga wani nauyin da taji kanta da idanunta nayi na bala'i, gaza ƙarasa buɗe idanun nata tayi, sakamakon ahankali ahankalin da ababuwa suka soma yowa zeroying brain nata. Highlighting abinda ya faru da ita ta shiga yi tana ƙiran _Hasbinallu wani'imal wakeel_ adai cikin zuciyar nata taci ga da cewa _ba gaskiya bane wannan mafarkine baze taɓa yiwuwa ba na sani?, tabbas ba gaskiya bane hakan bazai taɓa faruwa dani ba...., Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!" Kalaman da take ta famar nanatawa kenan da muryarta wacce ke rawa ba kuma ta fita sosai, wanda ya saka hankalin Shareefah dawowa gare ta dake zaune se famar ɗauke kwalla take, don ita kaɗai ce a wurinta, Yaya Sadeeq yace babu ruwansa da duk abinda ya faru da ita. Ganin yacce take ne ya saka ta saurin miƙewa ta nufa fita don ƙirar Dr pooja da tace data farka ta ƙirata, se dai suna shigowa bata ko numfashi alamun ta sake somewar kenan, don haka kai tsaye wasu nurses ta kira suna turata a gadonmarassa lafiya....Direct emergency room aka wuce da ita domin abin nata na nemar fin ƙarfin tunaninsu suma, daga ta farfaɗo seta kuma suma tun kafin wani lokaci.

After 20mn.

Gaba ɗaya hankalin Shareefah ya sake tashi tun da aka shiga da Yayar tata take ta famar safa da marwa a bakin ƙofar emergency room ɗin, daga can gefe kuma Ya Ahmad ɗin ne da shi ɗin ma yake tsayen ya gaza tafiya, sedai baya kusantar inda take amma kuma ya gaza tafiya ya barta. Inda kowannensu da irin abunda yake saƙawa acikin rai da zuciyarsa.saidai banda ita da tunani da kuma nutsuwar zuciyarta suka kau, don sun jima da barin jikinta suna tafiya wani wuri na daban, wanda take cike da tarin fargaba acikin ranta dangane da makomar auren yayar nata, wanda indai zata tuna hakan ne ke sanadiyyar saka hawayen dake cikin idanunta kasa tsayuwa.

Around 6:30 pm.

Har zuwa wannan lokaci suna tsaye bakin emagency room ɗin, sunƙi matsawa ko ina bayan sallarn da shi yaje masallaci yayi ita kuma tayi anan dandanin wurin. Haka kuma har zuwa wannan lokacin doctors ɗin dake cikin emergency room ɗin, suma basu fito ba suna can suna kokarin saita tunani da natsuwarta da se sun samu kamar zata dawo daidai seta sake birkice musu,
duk yanda suka so control matsalan amma abun yaci tura, Ganin abun na ƙoƙarin fin ƙarfinsu ne kuma ya saka su yanke hukuncin wucewa ita ICU kaitsaye, saboda acanne zata fi samar kulawa fiye da nan ɗin ma, gashi daɗi da ƙari ko babu komai yau Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ na cikin asibitin, wanda a da ita ce wacce zata yi aikin, rashin ta ya saka dolen dole Dr pooja ma Dr Bilal waya ta sanar duk abinda ake ciki, shi kuma baya gari lokacin yaje wata interview ta manyan Dactor's, don haka kai tsaye ya ƙira gida ya sanarma Abban MAJEED ɗin ana son ganinsa maza maza a cikin asibitin, wanda kai tsaye yasan in ba hakan ya masa ba bazai taɓa zuwa ta sauƙi ba, kuma har lokacin yana cikin ICU ɗin.

Acan ɓangaren Shareefah kuwa har zuwa lokacin tana wajen emergency room ɗin a zaune tayi jigum ta manna
kanta da jikin bangon ginin, daga ta can kasar raunatacciyar zuciyarta kuwa sunayen ALLAH kawai take ta famar ambatowa, cike da saka duk wani fata da kuma burin ta akan Yayar nata,
Kan zuwa yanzun kuwa kan kuma zuwa lokacin da abin ya faru ta zubar da hawaye masu yawan gasken da basa da adadi, har saida cikin idanunta sukayi jajur suna mata wata kalan zogi da kuma zafi, fyaiɗe ba?, fyaiɗen ma wa Matar aure?, shin tayaya mutane zasu ringa tunanin duniyarmu zata zauna ƙalau, alhalin kuma ɓarna a ban ƙasa tayi yawar da bata da adadi ko iyaka?...... Tana nan zaune har bata san iyaka adadin da ta sake ɗauke ba taji kamar motsin buɗe kofa, wanda ya saka ta ɗagowa hakanan taji zuciyarta na bugawa, wannan dalilin yasa ta tsurama ƙofar fitowan rinannun idanuwanta, wanda kai tsaye ganinta na sauƙa akan *Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ*, dake ta famar wani kalan bala'i yana yima Dr pooja tsawa ran nan a matuƙar ɓace, fuskarnan da dama take ɓaka ta sake rinewa, amma fa bawai baƙi irin na muni ba, irin na hasalin masu jin daɗi da kuma kwanciyar hankalin da suka gama ratsawa, haka ya wuce wanda ya saka Dr pooja ɗin jan burki a gaban Shareefah ɗin. Tana me ƙoƙarin zare handgloves ɗin dake hannunta... "Dr yaya jikinta ?, ta farfaɗo?bata dai sake somewar ba ko???" Haka Shareefah'n keta famar jeroma Dr ɗin tambaya, cike da fargaban kada agaya mata cewar har yanzun bata a daidai nata bata cikin sense nata. Ajiyar zuciya me ɗan zurfi Dr pooja ɗin ta sauƙe, kana cikin son kwantar mata da hankali tace....
"Jikinta yayi worst sosai ne, wanda firgicin abinda aka mata ne ya sakata sumewar da tayi, har hakan ke ƙoƙarin taɓa brain nata amma In sha ALLAHU zata sama sauƙi da izinin Ubangiji....
Ta kai ƙarshen maganan tana me kallon Shareefah'n dake ɗibar kamanni sosai da Meenal da ta tsare ta da idanunta sosai tana kallonta, dukansu shiru sukayi gaba ɗayansu, yayin da itama gefen Dr pooja ɗin tsananin tausayi da ƙaunarta ke mugun kamata.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka sake gangaroma Shareefah'n daga cikin idanunta, zuwa kan ƙuncinta, cike da raunanta haɗi da rashin ƙwarin zuciya ta koma ta sake jingina jikinta da bango... Rashin Ammeynsu na dawo mata sabo fil, ta tabbata da ace tana raye da tuni tana nan rungume da kan Meenal ɗin suna raba ciwon tare...

Da sauri tayi hanzarin ɗago kanta jin kamar an sake buɗe ƙofar da aka shiga da Yayar nata, wasu nurses mata ne guda biyu suka fito da yayar nata a gadon marasa lafiya.Ganinsu da tayi ne kuma yasa har kamar a ɗan zabure tayi kansu, saidai kasancewar kuma suna sauri sosai ne, yasa ta kasa cimmusu saboda dakatar da ita da ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi, bisa dole haka ta tsaya akan ƙafafunta dake rawa, daga can nesa tana zubawa fuskar Mijin Yayar nata ido, da har lokacin ya gaza tafiya shima,sedai dishi dishi take kallonsa saboda ruwan hawayen da suka cika mata idanu. A cikin zuciyarta take sake jin tsananin tausayin Yayar nata acikin zuciyarta, sai takejin cewa tamkar Yayar tata zata rasa damar ci gaba da kasancewa a karkashin inuwar Mijin nata, tana jin ya zatayi da irin wannan rayuwar da take shirin fuskantar ta a cikin rayuwar auren ta?,
Haƙiƙa ta sani cewar Yayar nata mutum ce wacce take kamar tinzirarriya, wacce idan aka hanata abu to ita kuma kamar a lokacin ne ma ake ingiza ta gashi wannan abin ɗin, Hakan kawai da take hasasowa ne ke saka karya mata zuciya, hakan yasa ta sake damƙe hannunta ɗaya dake cikin ɗaya a bayyane cikin raunin murya tace....

"Allahumma La sahala illama ja’altuhu sahala, wa’anta taj alul hazna iza shiyta hasla, Yah ALLAH ka taimake mu!, Ya ALLAH ka kawo mana ɗauki da agajinka ka kawo mana mafita a cikin wannan halin da muke ciki, ka dubemu da idon rahama ya Rahman ya Arrahaman Rahimin!!!......" Ta ƙare maganan tana kuka hadi kuma da ware idanunta, cikin wani kalan damuwar dake sake shigarta take cewa....
"Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!" Tana kamar zata shiɗe daidai da isowar Ya Sadeeq daya biyo bayanta, don bai zata abin ze kai haka ba, kuma dama shima yana da zafin zuciya da kuma riƙe abu a zuciya.
"Shareefah!"
Ya ƙirayi sunan ƙanwar nasa cike da damuwa da tashin hankali, yana tallafo fuskarta dake ɗauke da tsananin damuwan halin da yayar nata take a ciki, yanda yaga hawaye caɓa caɓa akan fuskarta ne ya sake tashin hankalin sa. Kafin a sanyaye ta ɗago cikin muryan kukan dake ƙoƙarin sake kufce mata ta kamo hannun yayan nata, kafin cikin sigan bayyana tsananin rauni da damuwarta tace.

"Ya Sadeeq ka taimakeni banason in rasa Yaya Ameenatou......"
Chapter 10 · 0% Book details