← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 36

Sashe 25

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se dai kuma ya dakata ne da maganar a lokacin da nutsatsestsiyar muryan wanda zata bata zatansu ya karede ilahirin kotun, "Ina da ja nima yame Shari'a....." Cikin nutsatstsen kamala da wani kalan kwarjinin da yake da miƙe, tare da ɗan rausayar da kansa gefe yana me furta "SUNANA LAWYER MAJEED DAWOUD ISHAQ!, Lawyer me kare mutumcin Dr MAANAL, Me kuma kare Kima da darajar asibitin 4 4...." Tirƙashi!, wannan fa shi ake ƙira da tashin hankalin da ba'a sa masa rana, haka zuciyoyin mutane da yawa dake zazzaune a wurin suka fara furtawa, na kawai ganin MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin a matsayin wanda zai jagoranci shari'an, su kansu iyayen Sameer ɗin seda ƙirajensu ya buga da ganin bayyanuwar nashi, don kuwa a lokacin da suka ganshi a cikin asibitin se suka shiga taytayi da hankalinsu, wannan dalilin ya sanya suka sanja akalan wasar nasu zuwa kan Meenal ɗin ita kaɗai, wanda suke da tabbacin indai suka ce zasu buga wasar tare da shi ta hanyar tsomo asibitin sa ciki, to kuwa ba za su taɓa nasara akan case ɗin...

Amma duk da hakan se suka fara karfafama kansu gwiwa, tun da suna da tabbacin bawai sanin ainihin takamaimain case É—in yayi ba, amma kuma se sukaji woni zance na daban bama wanda sukay hasashen bane....
"15/9/2025 Itace rana mafi munin da Mr MAANAL SHEHU USMAN ba zata taɓa mantawa da ita ba, domin kuwa itace rana mafi munin da ta munana rayuwarta tun daga farkon ginata har zuwa wannan lokacin da nake tsaye a gabanka ya me Shari'a!!..... Se kuma ya fesar da iska daga bakinsa yana kuma sassauta teayneck ɗin dake wuyarsa kana yaci gaba da furta... "A lokacin ta sama ƙirar gaggawa daga cikin asibitin 4 4 akan wata tiyatar taimakon gaggawar da zata shiga!, wanda da farko ma har taki amsa ƙirar ne, sabo da kusan 4 months kenan data dena fita aikin nata, amma bisa maganar da Mijinta Ahmad Ibrahim Shareef da yayi ya sakata fitowa ba dan taso ba..." Alƙalin ne ya dakatar dashi yace yana buƙatan ganin Mijin Dr Meenerl.. wanda ya mike take yana fitowa, bayan ya risinar da kansa yace..." Tabbas anyi haka yame Shari'a!, domin kuwa ni ne da kaina na ɗaukota na kawota har cikin asibitin bayan na bata baki akan ta taimaki rayuwar dake cikin hatsari, kasanwar abokiyar aikinta Dr pooja ta ƙirata akan ta taimaka ga wata operation ta gaggawar data taso musu..." Shima daga nan Alƙalin ya dakatar dashi yana cewa ya koma inda yake, idan da buƙatar sake ganinsa ze masa magana, kana Dr pooja ta fito daya bukaci ya ganta itama, amma kafin nan se lawyer Ibrahimul-khaleel ya miƙe yana rusuna kansa yace....

"Ya me girma me Shari'a!, ba kwana kwana ce da bada labarai ya tara mu anan wurin ba, domin kuwa a ƙa'idar Shari'a babu kwana kwana ko wani dogon labari, kawai a tafi cikin shari'an daya tara mu kai tsaye..." Daga haka ya risinar da kansa yana komawa zaune, "uyhmmmm zaki iya magana" Alƙalin ya bama Dr pooja damar magana, wacce idonta ya cika taf da ruwan hawaye...

"Kwarai Sir haka ne, kasancewar ranar babu da yawan Dactor's, Dr Bilal baya ƙasar, shima Dr Majeed daya kasance me asibitin baya ƙasar, ni kuma dake banyi ƙarfi sosai a fannin tiyatar ba ya saka sau da dama bana kasadar yinta, indai bata ɓangaren haihuwa bace!!!. Dake inda na karanta ɓangaren Radiology ne, shi yasa ban cika ganganci akan kowacce tiyatane, don haka na ƙira ta, kasancewarta kwararra a fannin ita, amma se tace min nayi hakuri ta ajje aikin ne kawai, wannan ya saka ni ƙiran Dr BILAL da baya ƙasar na sanar masa, wanda shi kuma ya ƙira mijinta kai tsaye daje aminin sane, shi ne dalilin daya kayo ta, wanda ni AYSHA wacce a da nake amsa sunan Dr Pooja Raju na musulunta, saboda wasu kalmomi na Yayanta Sadeeq da suka ratsani lokacin da yake mata nasiha...."

Daga nan ta koma mazauninta ana sake buƙatan ganin lawyer Majeed. Se da ya sake risinar da kansa kafin yaci gaba da faɗin. "A lokacin data shiga tiyata room ɗin da niyar fara tiyatar wanda idanuwanta suka gane mata ne ya sakata sakin kayan aikinta, ta fito ranta ɓace ko ganin gabanta bata yi saboda ainihin abinda idanun nata suka ganar mata, ba kowa bane ba kuwa face Sameer Garba Aliyu na Yaya, Mutumin daya keta mata haddinta da daraja da martabar aurenta ta hanyar mata fyaiɗe...." Daga haka ya dakata yana kawar da kansa gefe, don bazai iya ci gababa kuma daga nan, ga wata irin hayaniyar da cikin kotun ya ɗauka. Wanda ya saka lawyer Ibrahimul-khaleel datti miƙewa a matuƙar fusace yace.

"Tayaya akasan cewar Sameer yama Dr Meenerl Shehu Usman fyaiɗe?, ko dan kawai anga baya raye?, shi ne ake son renama alkalai da masu Shari'a hankali ta hanyar kirkiro ƙagaggen labari?, da wannan hujjar nake son wannan kutu me adalci tayi duba domin kawar da zargin da ake ma wannan yaro" yay maganar yana ɗan dukan table ɗin da yake kai.... "Saboda ina da shaidar hakan...." Lawyer Majeed ya sake faɗi shima daidai da lokacin da wannan shegen tight security ɗin nashi ke shigowa da zaratan samari har su uku..., wanda ya saka iyayen yaran da suka zo domin marama abokinsu Sen Garba Aliyu na Yaya baya suka miƙe ciki da kiɗimar uban me zai kawo yaransu kuma cikin shari'an... Alƙali ne ya bada umarnin ya tare su wurin da ake tsare masu laifin... Gaba ɗaya sun yi wujiga wujiga sedai babu alamar duka wa ko wannensu. "Waɗan nan sune shaidar yame Shari'a" Majeed ya faɗi yana isa har inda yaran suke, kana yaci gaba da cewa, "Nasan duk wanda yama Sameer Garba Aliyu na Yaya farin sani, to kuwa tare da waɗan nan yaran ne ya san shi, sabo da sune yaran dake mara masa baya wajen aikata kowanne kalar ɓarna..., Wannan sunan sa MUJAHEED, wannan kuma TAREEQ,shi kuma wannan CLEVER BOY..." Yakai ƙarshen maganar da rusunar da kansa bayan yace su ne zasu bada cikakkiyar shaidar komai daya faru a lokacin.... Nan suka shiga zayyano komai tin daga lokacin da suka taho bayan sun bugu a motarsu daga club ɗin da suka kwana, kawai sun zo gitta hanyar suka ganta tsaye alamar wani taimako take nema, har sanda suka isa gare ta da lokacin da shi Sameer ɗin ya musu inkiyar su zubar masa da ita, har zuwa kan magiyar data ringa musu tana kuka da kuma sumewar da tayi, wanda ada duk su huɗu suka so afka mata amma ganin bata numfashi ne ya saka suka gudu, gashi kuma gefen titi suke wani ka iya kamasu....

Tun daga lokacin da suka fara bada labarin suke kuka suna cewa wllh shi kaɗai yayi banda su ana tambayeta, don ALLAH a musu sassauci a sake su su tafi, har lokacin daya sama accident ɗin suka kaishi cikin asibitin da nan ne mafi kusa, abin mamakin kuma da ya sake bama kowa mamaki be wuce cewar da suka yi, daidai wurin da abin ya faru dai dai wurin sukayi accident ɗin, kuma shi kadai ya raunata, amma su duk basu yi komai ba... Haba sega ido yana fara rena fata, basu sake tsinkewa ba har se lokacin da Majeed ya bada umarnin sake shigo masa da wasu daga cikin jami'an da suka ringa barazana ga rayuwar Meenal ɗin, wanda wannan kuma duk aikin Haj Madina ne bama tare da sanin Mijin nata, har mutane ukun dake cikin wannan Black Bentley car ɗin data biyo bayansa suma.... Nan fa kowa yayi ɗifff an rasa me bakin magana, Se Haj Madina data mike tana rusa uban kuka tana cewa wannan duk cikin shirin Majeed ɗin ne, nan kuwa yace yana da wata hujjar ma, ya bama Alƙali CCTV footage ɗin dake yankin room's ɗin da komai ya faru, don dama ko ina da akwai, nan kuwa plash ta fara haska musu tin daga farkon kawo shin da su Muhajeed ɗin da suka yi, da shigar Meenal ɗin da fitowar, da zuwan Haj Madina ɗin, da irin maganganun da suka gayama juna, ciki kuwa har sanda Haj Madina ɗin ta fara bama Meenal ɗin bakin cewar ta taimaka ta fara duba mata yaronta in yaso koma miye ɗin ya biyo baya da bayyanuwar mijinta bayan da ALLAH yama Sameer ɗin cikawa.... Shike nan ƙurunƙus kan ɗan ɓera, don kuwa dai babu zance na gare kai yanzun... Alƙalin yayi gyaran murya da nufin yanke hukunci, amma suka sake tsinkayar muryan Meenal wacce tin da aka fara gudanar da shari'an kanta ke duke, Baffan tama haka tare da Ya Sadeeq.... "Ya me Shari'a ƙarar bata ƙare ba ai....." Tayi maganar tana bayyuwa gaban kotun, wanda ƙirjin Ahmad yayi wani kalan bugawa, don yasan maganar cikin ne za ta yi, shi kuma be shirya rabuwa da ita, be kuma shirya sake shirya amsar tozarci gaban dubban mutane ba, don kuwa zancen cikin nan da zata furta daidai yake da shi kuma fitar numfashinsa..... Kafin kiftar ido ya isa gabanta yana tin kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar cewa. "A ahhh Meenoh ba muyi haka dake ba, Pls don't forget kamar yacce na faɗa miki...." Raba jikinta da nasa tayi tana me furta. "A yanzu haka Ya me girma mai Shari'a sanadiyyar fyaiɗen da la'antaccen mutumin ya min ina ɗauke da cikin da yake daidai da lokacin da abin ya faru, wato wata huɗu da kwanaki 23 uku yau, wanda a ranar da accident ɗin ya faru dashi a ranar Dr pooja data bani taimakon gaggawa bayan sumewar da nayi bayan farfaɗowa na take cemin ina ɗauke da cikin wata huɗu da kwanaki biyar....." Wanda wata kalan hayaniya ta karaɗe cikin hol ɗin, ita kuma jikinta na ɗaukan wata wata tsuma, "Wanda Cutarwa da muzancin da wannan mutumi ya mi nake jin ba zan taɓa yafe masa ba!, Na so ace rayuwarsa bata ƙare ta cikin sauƙi da sassauci haka ba, naso ace se duniya ta gama wulaƙanta shi shi da macuta ma'intan iyayensa, ALLAH shi ne zai mini sakayya domin dama ni shi na barwa hakan tin faruwan abun..."
Chapter 25 · 0% Book details