← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 36

Sashe 36

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"YA ALLAH!, kai ne ka ƙaddara min wannan daddaɗar jarabawar taka kuma na amsa da hannu bibbiyu, haka kuma kai ne ka ƙaddara min duk kan abinda zai faru dani a yau ɗina har dama gobena!. Haka kuma komai a cikin ikon ka da yardarka suke ci gaba da tafiya, Ya ALLAH kaci gaba da zama gatana!, YA ALLAH a koda yaushe cikin gode maka nake akan duk abinda ka jarabceni dashi a cikin duniyar, ka kuma bani juriya da hakurin ibadarka, domin kuwa UBANGIJINA ka fini sanin daidai, Komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurarka, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddarar sane, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas nan dake takan iya sanjawa. Ya ALLAH ka fini sanin daidai na, ka mini maganin dukkan matsalolin da suke kewaye da wannan rayuwar tawa!, ka Zama gatan Mara gata... Ya ALLAH na amshi wannan rayuwar data zo min a wani irin hagunce, Hakan da ka tsara min na gode Ya Rabb, Tabbas wata rayuwar ba tamu ba, kamar yadda wata wata ƙaddarar ba sakacinmu ba ne, domin kuwa ƙaddara ba canki in canka bace bare kace zaka zaɓarma kanka kalar rayuwar da kake so ba, Ya ALLAH bana da iko ko halin da hukuncin ka, amma ka yanke min duk abinda yake ba alkhairi na bane..... Mafita ALLAH!, mafita ya ALLAH...." Tayi maganar jikinta na wani kalan tsuma, ji tayi kamar ana fuskarta zuwa baya don haka idanunta suka fara ganin xbibbiyu numfashinta kuma na gwamewa.... Se dai be kai ga rabuwa da gangar jikin nata ba wannan dai hayaniyar data gudonmawa na sake iskota har zuwa nan sashen nata, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un take ambata tana jin inama a yanzun ba sai anjima ta mutu tabar duniyar, wannan wanne kalan ƙalubale da jarabawa ce haka, me ta tare ma Hajiya Ana surukuwarta kuma Uwar Mijinta?, me ta mata da zafi haka, don kawai ta auri ɗan ne?, ko kuwa kawai don akan wannan ƙaddarar ta taɓa faɗa mata ne? Ta na tsaka da wannan tunanin ne kuma burum taji an bugo mata ƙofar bedroom ɗin nata....

"Kina ina shegiya baƙar munafuka!, to wllh na gaji da zama dake a haka, gaba ɗaya tun da kika auri Yahaya na dena gane mishi, gashi zama yayi zama ace zama har shekara na ƙoƙarin wucewa amma ace ko ɓatan wata baki taɓa yi ba, to wllh da sake, A yau ba sai yanzun ba indai ni uwace ga Alƙali Yahaya Shehu Usmanu seya sake ki Aminan...."

Jikintane ya tsananta rawa sosai fiye da farko, amma babu ɗigon hawaye ko ɗaya a ƙwayar Idonta, shigowar Alƙalin kamar wanda aka kifo ne ya saka Meenerl ɗin saurin miƙewa tana nufarsa, don gani take a cikin wannan yanayin shi kaɗai ne Garkuwa da madogararta, hannunsa ta koma cikin kamar ta fice a hayyacinta tana jan shi gaban Hajiyar tasa suka zube, "Don ALLAH Hajiya kiji tausayina, ki tausayama maraicina kiyi hakuri ki janye kalamanki akan mu, wllh ba laifi na bane, Daddy'nsu kace wa Hajiyarmu nima zan haihu, kai nake ta jira wllh a shirye nake indai zaka bani cikin!!!, Nima ina son yaran Hajiya...." Cafe zancen yayi shima ta hanyar sake furta.

"Hajiya dan girman ALLAH, don Annabin Rahama Annabi Sallallahu alaihi Wasallam kiyi hakuri Hajiya, don wanda akai duniya dominsa lahira dominsa, aka yi wuta don maƙiyansa, aljannah kuma don masoyansa ki gafartamana ki mana sassauci wllh ina son Jaririyata, ina jin tsananin tausayinta, wllh ban san wanda ya haɗani dake ba cikinsu, amma kamar yanda kika shariɗanta min wllh tin daga wannan ranar ban sake kusantar ƴar shila ba gata nan ki tambayeta koba haka ma Meenal?..."

Wanda ita kuwa Meenal ɗin jin kalamansa na ƙarshe ne suka sake nemar gigita ƙwanyarta, me hakan ke nufi?, Hajiyar ce ta hana masa dena kusa tarta kenan da yayi tsayin watanni kusan har ukku kenan?, wanne laifin tama ALLAH ita kam da yake jarrabarta da ƙaddarori masu kwamanceceniya da juna?, ita kuwa Hajiyar se wani sake huhhura hanci sama take tana wani karkada ƙafafunta. "Ta yaya kake son inci gaba da yarda dakai Yahaya?, A gabana fa yanzun gashi nan kake ƙiranta da sunaye na fitsara da rashin mutumci har da wata ƴar shilarka, dan ubanka yau she ka fara farauta ban sani ba da har kake da wata ƴar shila?, kuma ni dai iyaka sani na baka taɓa sunkuyawa da kanka ka haihu ba bare na sake tabbar da cewar kana da jaririyar, ka sani idan har kaji bakina ya sake buɗuwa da nufin kowacce kalan magana to ka sani ta tsinuwace gare ka Yahaya....."

"Hajiya don alfarmarki da Sayyiduna Muhammadun Sallallahu alaihi Wasallama kuyi.....h......."

_ALHAMDULILLAH!,ALHAMDULILLAH!!, ALHAMDULILLAH ala kulli halin🙏 🙏!!!, Anan na kawo ƙarshen book One na KARSHEN ƘADDARA, sai kuma ALLAH ya haɗa mu da masu rabo a BOOK TWO nashi_

_Tofa masu karatu yaya take ne?, mike shirin faruwa?..._

_Shin ya kuke ganin za a kare tsakanin Alƙali Yahaya Shehu Ɗan Batta da kuma mata da mahaifiyarsa?...._

_Ku a naku gani da tunanin wannan sakin ze iyu kuwa?, Me kuma kalaman Hajiyar suke nufi da gasken kenan itace da kanta ta dakatar dashi ci gaba da mu'amulantar matarsa?, kai wannan cajin kai dai da yawa yake...._

~A tunaninku shike nan wasan zezo ƙarshe ne?, La la la..... Yanzu ne ma zamu ɗauki wani salon shima me zafi, kuma shima kakan nashi ƙalubalen daban shima~

_Domin kuwa a gobe ma da wani labarin, Kwarai kuwa haka Nie AMMEY LAYLERH'NKU É—in ku naceeee...._

_Wai hausawa suka ce ɓukatar maji hajji Sallah, karfa ku manta da hasashen Ahmad kar dai ya zame mana gaskiya jama'a, domin fa ance sunan littafin ƘARSHEN ƘADDARA karku manta, me bi kuwa akwai yiyuwar wasu aure auren bayan na Alƙalin dake kanta, wanda yake daf da rugujewa shima....🤸🤸🤸🤸_

_Amma fa kar FAN'S su ce na fiye zaƙewa nima a zaƙen nake da jin yadda zata kaya ɗin ne ai🤩_

_Tofa wata daban kuma wata sabuwa, wai ma waye wannan MAJEED DAWOUD ISHAQ É—in ne?, Baban AYLA kuma lawyer É—in daya tsaye ma AMEENERH SHEHU USMAN, har se da Shari'a ta bata gaskiya....?_

_Wai kuwa 👍 🙂 duk kun shirya bin AMMEY LAYLERH'NKU, don warwarar wannan ƙaddarar da daku?, kun shirya ayi tafiyar daku cikin labarin littafinta me SUNA KARSHEN ƘADDARA???_

_Hhhhh Hajiya ke dai nace bara nai shiru kar na cika masu karatu da tarin jawabai, domin kuwa tafe labarin yake da tarin gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon da ban taɓa yin irin saba na sani_

_HUMMM Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakuÉ—e cikin wannan littafin_

_Duk zamu samu amsoshin waɗannan tarin tambayoyi namu ne idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo ƙarshen BOOK 1 NA ƘARSHEN ƘADDARA Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin ƘARSHEN ƘADDARA 500 Hundred ne kacal babu yawa..._

_Ga duk mai son biya kai tsaye zai tuntuɓeni a wannan number_

👇
08104493215

Wanda suke sun biya zasu turo kuÉ—in su cikin wannan asusun bankin

👇
8104493215
Maryam Nasiru
Opay

Or

3206656358
Maryam Nasiru
First Bank

A turo shedar biya ta wannan number

08104493215

_Masoya na amana a nuna min kauna sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na KARSHEN ƘADDARA, daga AMMEY LAYLERH'NKU me ƘAUNARKU FAKA FAKA_🤸🤸🤸_

_Byee my FAN'S sai mun sake HAƊUWA a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuɗin ka saida rabonka littafin ƘARSHEN ƘADDARA ba hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo?...... To ai shikenan kawai A gimtse ɗinnn🤸🔏 🫰✊_

_MASU TAMBAYANA JERIN SUNAYEN LITTATTAFAINA TO GASU KAMAR YACCE NA MUKU ALƘAWARI ZAN LISSAFO MUKU...._

*KAREN BANA FREE*
*JALAAL AREEF FREE*
*ƘAUNA BIYU FREE*
*MIKIYA PAID ONLY 500 HUNDRED*
*TA DABAN ONLY 500 HUNDRED*
*DUNIYARMU ME CIKE DA TARIN ƘALUBALE ONLY 1K*
*SO DAN RAYUWA ONLY 500 HUNDRED*
*RAMIN KURA ONLY 1K*
*DUHU na DUKAN duhu ONLY 1K*
*SE KUMA SHI WANNAN ƘARSHEN ƘADDARAR shima 500 HUNDRED yazo muku*

Ku sani waɗan nan litattafan suna jerin sunayen littattafan nawa ngd👏👏👏....

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

ᴬᴹᴹᴱʸ ᴸᴬʸᴸᴱᴿᴴ🤫😶🤐😥😢😩👌✍️🙏👩👁️🤦🙅‍♂️🙋‍♂️🙆‍♀️.......

08104493215
Chapter 36 · 0% Book details