← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 36

Sashe 35

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Akwai mutanen dake kewaye dani amma babu wanda ke fahimtar irin kaɗaicin dake cikin zuciyata, ina murmushi ne kawai don kar a tambayeni amma har cikin zuciya hawayene ke kwarara ba tare da tsayawa ba. Na koyi zama ni kaɗai na kuma sake yarda da wasu ke cewa, wasu mutanen daga nesa suke burgeka saika haɗa hulɗa dasu zaka yi nadama. Wasa wasa se gashi har gashi har mun shiga wata na huɗu cikin wannan matsalar, wanda ya kama watanmu tara da aure kenan, tuni kuwa har wasu ƙananun maganganu sun fara fita waje har zuwa can cikin anguwarmu, wai Miji da kishiyoyi nacin ubana suna soya min aya a hannu, duk lokacin da zanji makamantan zantukan kalan hakan nakan yi murmushi ne kawai kamar yadda na saba, murmushin na lulluɓe duk wani miƙin dake cikin zuciyar tawa... Yau dake girkin tane da wuri ta kammala shirinta, don yau itama ta tanaji kalaman fara dawo dashi kan daidai ɗinsa, da huri ta isa lokacin ɓangaren nasa tin kafin ya shigo, amma se da ta tabbatar me girkin ta fita kuma Maman Abeed ce wato Raƙabiya. Ɗakinsa ta fara gyara masa tsaf kana ta fito parlour ta kunna kallo, tana zaune sega Maman Abeed ɗin ta shigo kamar wacce tayi mantuwa, bata ko kalla inda take ba har ta gama juye juye da aune aunenta ta kama hanya ta fice bayan ta mata tsaki, amma in ta tankatama ai ta sama arziƙi... Babu jimawa kuwa se gashi ya shigo ɓangaren nasa, sedai turus yaja ya tsaya yana kallarta da take cikin shigar kayan bacci masu kyau. Zaune ta tashi fuskarta ba yabo ba fallasa, sannu da zuwa ta masa lokacin da yake kaiwa zaune saman kujera. Gaidasa tayi a natse ya amsa yana jin duk babu daɗi da abinda yake mata, Se dai babu yacce ya iya ne dole ne saboda ya na son bata kariya.... Se dai be san da wanne bakin ze mata magana ba, be kuma san da wanne idon ze dube taba, wata ajiyar zuciya ya sauƙe yana kamo tafin hannunta cikin nasa, lumshe idonsa yayi yana jin kamar zuciyarsa zata fashe da tsananin ƙaunarta da tausayinta. Ahankali ta zame hannunta daga cikin nashi tana kaiwa ƙasa cikin rawan murya tace... "Daddy'n Nusaimah don ALLAH ka yi hakuri idan na baka wani abu ne ba tare da sani naba,kasan duk inda ɗan Adam yake azijine wllh ban san kome na maka ba, na kuma duk iyaka yi na amma ban gano daga inda matsalar take ba... Daddy'n Nusaimah
Me ya sa kake ƙoƙarin sanjawa daga yadda na sanka?, Me ya sa kake ƙoƙarin daina bani kulawanka?, Me ya sa ka daina jin tausayina?, Me ya sa a yanzu bana gabanka?, ka dena lallashina. Me ya sa ka sanja min cikin ƙanƙanin lokaci haka?, Me ya sa?, Me na maka?....." Tayi maganar muryanta na rawa sosai... Hannunta ya kamo tare da ɗago ga yana share mata hawayen fuskarta cikin taushin murya yace. "Baki min komai ba Ameenatou!,babu abinda kika min wllh, kawai ina jin kamar ba daidai nake ba, ina kuma jin kamar ban chanchanta inci gaba da zama dake irin haka ba, sedai na rasa akan me akan kuma wane ne..... Wani kuka ta fashe dashi tana me furta. "Tabbas na fara zargin kaina da cewar ko ababuwan dana aikata ne ALLAH be gama yafe min, amma nima a cikin raina inajin kamar cewa tabbas wata rana zaka rasani, sannan zakai kewata ba don nafi kowa ba, ba kuma don na zarta sauran matan kaba, A ahhh se dan kawai na san ranar zata zo maka wata rana, kuma idan wannan ranar tazo, kada ka kira shi da ƙaddara, ka ƙira shi da sakamakon abinda ka aikata!!!, tun da na tambayeka laifi na kace ban maka komai ba, haka kawai zuciyarka ta tsara maka fara tsanata sabo da binciko tsoffin laifukana na baya shi ne ka fara ɗora alamar tambaya akai na ka kuma dena SO da TAUSAYINA, wanda dama nasan su suka huce maka gaba wajen auren na...." Daga nan ta kwace jikinta a nashi ta fice daga ɗakin a guje tana riƙe bakinta da kuka ke son kwace mata...Ahankali kuma taɗan buɗe idanunta wanda cikinsu ya cika da ruwan hawaye, ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, tare da ƙoƙarin shanye ruwan hawayen nata, dan batajin zata iya barinsu sukai ga sauƙa akan fuskar

_MAJEED DAWOUD_

zaune yake saman sofar dake gaban gadonsa, system na shi ajiye saman desk se wasu ƙananun glass cup yana opreting wasu files na asibitin daya ziyarta na Young pharmacy and private clinic...tshirt ce mai gajeran hannu a jikinsa sai dogon wandon ta masu taushi. Idanunshi a sakaye cikin farin glass ya zuba su akan system ɗin da yake ta famar aikinshi akai. Daga gefen sa kuwa Ayla ce kwance ta dora kanta saman jikinsa,kanta babu scaf anyi saima space buns ɗin da aka mata irin na Babyn nan, wanda suka mata kyau sosai gwanin birgewa... Duk da kasancewar aikinsa yake gudanarwa amma kuma ƙasan zuciyarsa mamakin abinda ya gani yake, amma duk da haka cikin ƙarfin halin danne abu a zuciya da kuma yanayin sa na rashin bama abu mahimmanci da basarwa ya ture tunaninta a ransa, se kuma yayi saurin istighfari a ƙasan zuciyarsa yana sakin wata ajiyan zuciya, abinda ya danne ƙirjin nasa na ɗan lafa masa yana jin ɗan sassaucin ba kamar ɗazun ba. Shiru kawai yay yana lumshe idonsa tare da jingina bayansa da jikin gadon, kafin ya sauƙe idonsa ahankali akan Ayla dake lafe a jikinsa tana bacci hankalinta kwance, sake lumshe lumsassun fararen idanuwansa yayi yana ɗan tafiya wata duniya... Wani gauron numfashi ya kawo kuma jin numfashinsa na shirin fiffizgewa , alaman tunanin daya tafi me ɗan zurfi ne. Da Ayla ya tashi a jikinsa kai tsaye Part na Ummiensa ya nufa, kai tsaye ya kwantar da ita a gadon ummie bata ɗakin, peck ya bata a goshi kana ya fice yana komawa room nashi. Zaune yake dafe da kansa ya ɗan jima a hakan kafin yayi kundin balar miƙewa adda'a ɗauke a bakinsa, zare kayan dake jikinsa ya shiga yi wannan asalin lafiyayyar chocolote skin ɗin nashi na bayyana tana ɗaukan ido, saboda samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau da yake amfani dasu. Kai tsaye bathroom ya faɗa tare da sa karma kansa shower yana lumshe idanuwansa ruwan na sauƙa akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna sanyaya jikinsa a hankali.
Ya jima sosai sosai a ruwan yana wankan, kafin ya fito ɗaure da babban towel me ɗan kauri white har wani miski miskin blue yake, jikinsa na fidda ƙamshin shower Soap ɗinsa na Ocean seaweed. Hannun sa ɗaya na riƙe da wani mini clean blue towel ɗin daban yana tsane jikinsa a natse. Pyjamas farare ya zira yana kallar agogon bangon dake ɗakin nasa. Ganin se yanzu ne ma sha biyu ke bugawa ya sanya sake ɗaukan system nashi, akan wata arniyar ɗunƙulalliyar kujera ya zauna yana fesar da hucin numfashi,
Ci gaba da ayyukansa yayi har zuwa wajen ɗaya, iska ya zuƙa ya kuma fesar yana jan idanunsa ya lumshe ganin ya kammala aikin nashi, Goran ruwan dake a Centre table ɗin dake gaban gadonsa ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin, yana ambatar ALHAMDULILLA a bayyane.......

★

Zaune takai akan gefen gadonta tana haɗe kanta da gwiwwarta ababuwa na nemar fasa kanta ,idanunta sunyi wani irin jajir ɗin kaiwa maƙura a ɓacin rai da tashin hankali, daga inda take cakuyen take me roƙon ALLAH inama ya bata damar fashewa da gursheshen kuka. Se dai tayi duk yacce za ta yi amma ina kukan nan yaƙi iyuwa ya, tabbas se a yau take sake yarda wani kukan ma rahama ne, lallai kuma ta sake yarda da zancen nan na mutane da suke cewa idan baƙin ciki yay baƙin ciki kukan ma baya taɓa yiwuwa, Shin me rayuwa take nufi da ita ne wai har haka?, hannunta na dafe da kanta ta buɗe idonta, se kuma ta ware duka hannuwanta guda biyun tana me furta.....
Chapter 35 · 0% Book details