← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 36

Sashe 4

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta wani ƙarashe maganar nata da tsawa tana korar ta a kitchen ɗin, wani abu me kama da ruwan hawaye ne taji sun ciko idonta, don haka babu musu ta fice, sa'an ta ɗaya Abba baya parlourn don haka ta shige ɗakin Fatima ta zauna a gefen gadon ta tana dafe kanta da hannayenta. Jin Shigowar Hajiyar har ɗakin Fatiman ne ya saka gabanta yayi wani irin faɗuwa, yawun bakinta na ƙafewa ƙaf, take taji kanta ya sara mata, don haka a cikin zuciyarta ta shiga nanata kalmar INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN... Tamkar sauƙar aradu haka taji muryan Hajiyar tana cewa. "Wllh³ bazan taɓa son ki ko na amsheki a matsayin surukuwata ba Meenal, sabo da na tsanake!, bana sonki!, bana ƙaunarki, gaba ɗaya so kawai kike ki haukatar min da yaro baya da aiki se naki,yanzun fa duba har aiki ya samo miki a asibitin *4&4 SPECIALIST HOSPITAL* wanda ni nan babu kalan roƙon da ban masa ba akan ya samowa Fatima amma yaƙi, se gashi ke dake ke kece ya samo miki tashin farko, ko shawartana beyi da maganar ba, sabo da ga makiyiyarsa se yanzun naji ya a faɗama ubansa ni ban kai ba, ban kuma isa ba...., To ki sani wllh se nayi duk me iyuwa na rabaki da Ahmad kamar yadda kike nemar rabani dashi kema....." Fuuuuu daga haka tasa kai tana ficewa har wani hucin bala'i da masifa take. Kuka tayi me rai da lafiya a wurin tana roƙon ALLAH ya ganar da Hajiyar Ahmad ta gane gaskiya, tana nan zaune har bayan sallar magrib amma hawayen be dena zubo mata ba, jin motsin kamar za'a shigo ne ya sakata saurin faɗawa toilet ɗin Fatima ta wanko fuskanta tana gyara yanayin ta sosai, don tasan Ahmad ne , tin da taji shigowar Fatima da kuma lokacin da Hajiya ta dakatar da ita daga shiga ɗakin ta aiketa makota. Idanunsa ya zuba mata da kallon farko ya gane cewar kuka tayi, zama tayi a sofar dake daf da gadon Fatiman kwara ɗaya, inda ya ƙaraso har wurin a natse daf da ita yana zama tare da janyo ta jikinsa. "AMEENERH?" Haka taji ya ambata sunanta da full name nata kafin ya sake jefa mata tambayar "lafiyanki kuwa? Ko wani abu akayi miki?" Tsaye ta miƙe
sannan calmly ta goge hawayen idonta da bayan hannunta daya sake zubo mata, kanta ta jinginar a jikinsa tace. "Babu abinda aka yi ya Ahmad bacci nayi, kuma kasan idan nayi bacci tsakanin sallar la'asar da magrib da ciwon kai yawanci nake tashi..." Ta faɗa da sanyin murya and I can swear I saw him relaxed. Kanta ya ɗago bawai don ya gama yarda ba wani abu Hajiyarsa ta mata ba, fuskar sa cike da concern ya furta. "Kin tabbata?" Yana saka idonsa cikin nata don sake tabbatar da hakan. Vail nata dake gefe a tashe ya ɗauko mata yana ɗora mata samar kanta yaje suje. Babu musu kuwa ta bi bayansa don dama hakan take ta jira tin ɗazun, koda suka fito babu kowa a parlourn don dama Abba be dawo ba, yasan kuma dama ba sosai ya fiye dawowa idan yayi sallar magrib ba se anyi isha'a yake dawowa gaba ɗaya. Hannunta ya kama ya nufa sashen Hajiyarsa da ita, wanda gabanta keta sake faɗuwa amma babu yacce ta iya ko tace ba zata ba, haka ta bishi tana zaune samar darduma suka isa, sallama yayi bata amsa ba taci gaba da laziminta, tsugunne yakai gabanta yana ce da ita zasu wuce. Da hannu ta masa alamar suje duk da beji daɗi ba amma haka yaja hannun Meenoh ɗin nashi suna wucewar su. Gidan gaba ya buɗe mata ɓangaren me zaman banza ta shiga ya rufe ya zaga ya shiga driver sit yana tada motar suka bar gidan. A wurin gashin wasu zabbi ya tsaya fita yayi babu jimawa se gashi ya dawo hannunsa ɗauke da ledoji biyu, ɗaya ta gashin zabbin ce, ɗayar kuma fruits ya sai musu kasancewar yaga kamar na gidan sun kusa ƙarewa. Sannu ta masa tana amsar ledojin ta miƙa ta baya, daga nan yaja suka wuce gida, be shigo gidan ba ya fita don baya son ya shigo beyi sallar isha'a ba, shima kusan irin Abban nasa ne, yafi gane idan yayi isha'a ɗin ya shigo gidan shima, ita ce ta shiga da ledojin ta ware fruits ɗin a fridge ta rage wasu zabbin ma ciki don tasan da safe ba sai ta musu girki ba, ta ware musu kuma wanda zasu ci idan ya shigo. Karfe tara saura ya dawo, wanka ta taya shi ya fara yi kafin su fito cikin shigar kayan shan iska, don itama tayi bayan tayi sallah'n isha'a. Se baza ƙamshinsu suke, a natse suka kammala cin nama da youghout ɗinsu kafin su zauna suna kallar Film na HAQ a tare a laptop nashi, don duk Film sabo daga fito yake sauke musu su kalla. Har wajajen sha biyu saura kana suka kammala suna ta mayar da yacce film ɗin yayi kyau, ya kuma tsaru, don ba ita mace ba ko shi kansa da yake namiji Film ɗin ya taɓa masa zuciya, gashi kuma akan addinin Musulunci aka yi Film ɗin, har yacce wasu mazan ke wulaƙanta matayensu na gida idan sun ƙara aure, da yacce Ƴaƴan wacce ake zalumta suke ƙin iyayensu maza, saboda kuntatama mahaifiyarsu da ake, haka dai sukayi ta maida yadda suka tsara Film ɗin. Ɗan kwantar da kansa a kan kafaɗarsa yayi, wanda ya saka Meenal ɗan juyowa ta kallesa, shima kallon nata yayi yana wani kashe mata idon daya sakata lumshe nata, matso da fuskansa daf da nata yayi zata ɗan koma baya kaɗan yakai hannunsa ya kama waist nata daya saka ta jin yirrrr, tsigan jikinta na tashi bakinta yama kissing yana cewa. "In sha ALLAHU bazan taɓa kasancewa miji irin Abbas ba, don zalumcinsa yayi yawa, ya kuma cuci Yami Ghautam da yawa tare da yaranta. Idonta ta sake lumshewa tana jin tabbaci akan duk maganganunsa akan ta, ta kuma yarda dashi samm bata da haufi akan mijin nata, daga nan ya tashi da ita suna wucewa bedroom nasu, don har ta fara bacci a jikinsa, kwantar da ita yayi shima yana kwanciyar gefen ta tare da janwota yana shigar da ita cikin jikinsa, ta buɗe baki da niyar masa magana ya haɗe bakin, dole ta tsaya da kyau tana bashi kulawan daya kamata, sune har wajajen karfe ɗaya da rabi basu yi bacci ba, seda suka tsaftace jikinsu kana suka kwanta tana lafe a jikinsa tana sakin ijiyan zuciya me ɗan zurfi. Daga nan wani daddaɗan bacci me cike da SO da ƘAUNAR da suke ma junansu ya kwashe su, washegari har kusan a makare suka tashi, don se a gida ya jasu sallar subhi. Daga nan basu komawa tayi ƴan gyare gyarenta ta sake gasa musu namansu na jiya suka karya dashi, sedai yau ɗin ma dai kalan jiya da doguwan riga ta bubu ta fito, se sani ƙaramin vail, har ze mata magana kawai ya kyaleta suka fita. Ajje ta yayi yau be shiga cikin asibitin ba ta wuce ita kaɗai.....

_Byu byu hayya hayya ya take ne?, fatar dai wannan É—an littafi nawa ze amsu a wurin ku, kamar yacce kuka saba amsar duka littattafaina..._

_Idan naga reactions naku akan littafin zan fara sakinsa nan bada jimawa ba IN SHA ALLAHU....._

_ALLAH yasa wannan salon labarin da muka sanja ya muku, don labari ne akan irin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin gidajen rayuwar aurenmu zahiri da kuma baɗininsu, da yacce wasu mutanen su da kansu ke siyar ƙaddararsu da kansu da kuma hannayensu...._

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.

_My NAINERH TARH, My Ƙaunar ƙaunata My aminiyar kwarai mutuniyar kirki Uwar yaro na Mubeen kuma this Book for you, gashi ya iso gareki da zafi zafinsa fa💃🤸_

Page 3&4

♡ ♡ ♡ ♡
Chapter 4 · 0% Book details