← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 36

Sashe 18

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Gefen kunnensa É—aya ya É—an kama yana me sake cewa. "Ohh to ni kuma É—an Ummiensa mi ye nayi kuma?".

"Ka dawo ka sake tafiya ko kallarka ban yi ba!..." "Ohhh SO sorry na dena cutie " daga nan ya kama hannunta suna hayewa sama. Se da aka ƙira sallan isha'a suka fito tare da ya wuce masjid tare da Daddynsa. Koda ya dawo dinner ma sama sama yayi ya haye sama bayan ya musu sallama, yana isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom, wanka yayi tare da ɗauro alwala kana yafito, dogon wando na bacci ya sanya babu da vest, kwanciya yayi akan makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa yana faɗawa wata duniya ta daban. Bacci barawo gaza ɗaukan sa yayi se daf da asba, amma hakan be sa ya makara sallar ba, yana dawowa ya sake komawa bacci me nauyin da be sama ma daren jiya na sake ɗaukarsa.
10:30am.
Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa masu ɗauke da zara zaran gashi asamansu, kai tsaye ganinsa na sauƙa akan agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin, cike da nutsuwar daya samu ya zuro ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, bathroom ya shiga babu jimawa ya fito da alaman wanka ya yo. Tsab ya gama shirya kansa cikin wani lallausan yadi, ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi da kama jiki, combat shoe ya sanya aƙafarsa haɗe da ɗaura agogon Apple a hanunsa na dama, sosai yayi kyau bana wasa ba, ahankali ya isa gaban mirror yana ɗora kyawawan idanunsa ya kalli kansa acikin madubin. shi kansa yasan cewar shi cikakken kyakkyawan Namiji ne mai aji da kuma ɗaukar hankali. Haka ya tsaya sosai gaban madubin yana kallar kansa, Kafin ahankali ya sauƙe idanunsa ƙasa yana nufar wayarsa me ƙirar Galaxy S50 ya jefa cikin aljihun kayan dake jikinsa, yana sa kai ya fice daga cikin ɗakin.....

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.

Page 11&12

♡ ♡ ♡ ♡

ꨄ A ƙasa ya tarar da Ummiensa da ƙanwarsa Ikleemerh, dama AYLA wacce ke lafe jikin Ummiensa. Idanunsa ya lumshe da sake buɗe su akan Ayla ɗin dake jingine da jikin Ummien tana mata rigima, domin bata jin daɗi lumonia ɗin tane ke nemar tashi. Sakamakon hunturun da aka tashi dashi, gashi jiya da dare ba tare da sanin Ummien ba taje ta sheƙama jikinta ruwan sanyi, Shi yasa yau bata wani tashi da kuzarinta da ƙarsashin taba kamar kullum, Shi ne ma yasa ko school bata je ba duk da kasancewar Monday ce yau ɗin. Suna haɗa ido yaji wani irin raunin da ganinta ya sake haifar masa na ƙoƙarin taso mar, Ayla kuwa da ganin Papa ɗin nata ne ya sanya ta a farin ciki ne ta taso da gudu zuwa wurin sa, hannayen sa kawai ya buɗe mata domin ya san mine take shirin yi, tsamm ya rungume Babyn nasa zuciyarsa na masa wani mahaukacin bugu, Jin yadda jikin yarinyar ya saki, ga wani ɗan banzan sanyin da gaba ɗaya jikinta ya ɗauka. "Paapa" haka ta ƙirayi sunan shi cikin maraitacciyar murya.wanda hakan ya sanya Majeed ɗago haɓarta ya zuba idanunsa cikin muryan shirin yin kuka tace. "Paapa na dena wasar ruwan, kuma ma I hate him!, tin da yake sani jinya." Yanda tai maganar a hankali cikin rauni ne yasa kaɗan ya rage zuciyarsa bata fito waje ba, amma ya daure cike da son nuna jarumta yana ƙara ƙanƙameta sosai a cikin jikin sa. Kafin ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya, yana jin gaba ɗaya komai na nemar cinkushe masa. dole ne yana buƙatar ƙara ƙadaice kansa, domin gudun kada iyayen sa su fahimci rauni da kuma halin da yake ciki, zare ta yayi daga jikinsa samm baka isa kai tsaye ka fahimci halin da yake a ciki ba, amma a baɗini da zaka ga irin tarin raunikan dake chunkushe a cikin zuciyarsa, da kuwa tabbas saika tausaya masa.
Chapter 18 · 0% Book details