← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 36

Sashe 27

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ Ai tin kafin ta ƙarasa yay wani hanzarin amsar peper da byro'n, idanunsa na zubar da wasu ruwan hawaye masu ɗaci da ƙona zuciya yayi rubuta mata sakin ya bata, tana amsa taga ɗaya tak ya mata tace se ya jere mata ukun nan cif cif..... Duk yadda yaso data taimaka ta bar shi hakan, amma haka taƙi sema bakin data sake buɗewar da niyar sake tsine masan, ya sake rubuta mata saki ukun, kana ta fice da takardar sakin a hannunta tana huci......... Kai tsaye gidansu Meenal ɗin ta wuce wacce dawowarsu kenan daga Asibitin wannan fitila'in sakin ya sake riskarsu, komai bata ji ba game da sakin domin dama tasan zamansu dole ya ƙare Ya Ahmad ɗin,duk kuwa da iriyar ƙaunar junan da suke ma juna, amma tasan mahaifiyarsa ba zata taɓa barin hakan faruwa, se da ta tayi cin mutuncin da tijararta kana ta fice ga bar musu gidan ranta fesss yau dai ALLAH ya kawo mata hanya cikin sauƙi ta raba auren Ahmed ɗin da Meenerl, duk da kasancewar gwaggo Sadiya ba uwarta bace amma seda taji babu daɗi da ababuwan da suka faru da Meenal ɗin,amma kuma ko a fuska bata nuna mata ba, amma dake jajen ciki na munafunci ne shi ta mata, har da cewa ai ƙara da ALLAH ya ɓarar da cikin suma shi ne kwanciyar hankalinsu. Baffa kuwa da Ya Sadeeq ɗin idan hankalinsu yayi dubu to a tashe yake sakamakon sakin nan na Ahmad, wanda bayan sallarn isha'a ya ƙira Baffa ya ringa kuka yana cewa ya yafe masa haka ALLAH ya gama tsara iyaka rayuwar auren da za suyi kenan dama cikin 1 year's kawai, wacce ma saura 1 months su cika shekara ɗin cif da cif, kwantar masa da hankali sosai Baffan yayi yace ba komai Ubangiji yasa hakan shi ne mafi alhairinsu gaba ɗaya, Ya Sadeeq ma sosai yaji maganar sakin har cikin zuciyarsa amma kuma se ya fawwalama ALLAH shi ma, abu kamar wasa se gashi da dare Meenal ta gaza runtsawa, magabar sakin duk bata dameta se da tazo kwanciyar. Nan idanunta suka sake ƙaiƙashewa suka soye sabo da tsabar azabar da take amsa daga gare su, Idanunta ta rumtse ko zata ji sun rage daga zogin da suke mata, amma kuma ina babu damar hakan, sema jin da tayi kamar ba zasu iya buɗe mata ba, Wayar tane ta kawo haske alamar shigowar text message kasancewar a silent take, kamar ba zata ɗauka ba amma kuma ta miƙa hannunta da kyar tana janyo wayar, tana kallar test messages ne ta sake kife wayar ba tare data duba taga ko miye ba, don kai tsaye ta san MTN ne don su ne masu mata haka. Alwala ta miƙe ta dauro ta fito ta fuskanci alƙibla, bayan ta idar da sallolin data ringa yi ta ɗauka Alqur'ani ta hau karatu har zuwa sallan asuba, bayan ta idar da sallan asuba ɗin tayi adda'o'i masu kyau da girma kana anan wurin wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, wanda baya farka ba se wajajen sha ɗaya da rabi, wanka ta fito nan tsakar gidan tayi kana gwaggo Sadiya ta miƙa mata abin kari, kanta kawai ta jijjiga don ba zata iya cin komai ba adai halin da take ciki. Wayar tane ta shiga ruri tana ɗauka taga Maman Yasmin ce makwabciyarta, jiki a matukar sanyaye ta ɗauka wayar ta amsata.... "Meenerl abinda ya faru kenan?" Ta faɗi a raunace domin sosai suke mutumci babu laifi a zaman nasu, dake duk komai da komai be fita ba se a jiyan, zancen sakin kuwa tuni uban kowa har ya sani a cikin anguwar tasu, don yau wajajen karfe goman safe Maman Ahmad ta sake komawa gidan, taje da garada ta saka suka ringa fito da kayan Meenal ɗin har ƙofar gida, inda nan fa yan anguwar suka yi dafifi wasu cike da tausayin Meenal ɗin, wasu kuwa haka kawai suna mata ala ƙara ba tare data tare musu komai ba. A lokacin da dake wannan aika aikar kuwa a lokacin Ahmad ɗin na ciki yana jinyar zuciyarsa don ko gangar jikinsa da kyar take ɗaukarsa. Yana a wannan halin ya fito don jin kwarabniyar tayi yawa, a lokacin da yake kallar Mamyn nasa tana wannan aika aikar ƙiris ne ya sa zuciyarsa bata ƙarasa ficewa a gangar jikinsa ba, da kuma ya mata magana tace kul be rufe mata baki ba yanzu taci mutumcinsa. Shi ne ya koma gefe yay ƙiran Ya Sadeeq ya faɗa masa muryansa ko fita ba yayi sosai. Dan da nan kuwa sega Ya Sadeeq ɗin har ya ƙaraso da wata motar ɗibar kaya, har kuma lokacin Mamyn nasa nan kaf komai daya danganci Meenal seda ta fito da shi, haƙuri ya ta be Ya Sadeeq ɗin yace masa babu komai haka dama rayuwa ta gada. Daga haka suka hau kashe kayan Meenal ɗin suna zubasu cikin motar da yazo da ita ta wurin da yake aiki, koda yaje shagon waje Baffansu ya buɗe musu suka jibge kayan. Aka ware mata iyaka na sawarta kawai a gefe guda da nufin nan da kamar 1 week se a bata kar abun ya mata kusa da yawa.

Bayan sun kammala wayar da Maman Yasmin ɗin har zata ajje wayar wani abu me kama da transper na kuɗi ya ɗauki hankalinta, don haka kai tsaye ta shige cikin sakon, kuɗi ne zunzurutun kudi har naira dubu ɗari biyar, me ɗauke da account na Ya Ahmad ɗin ta, jikinta na rawa ta fito daga cikin amoung balance nata messages ɗin dake ƙasar sakon kuɗin ya sake ɗaukan hankalinta don shima ɗauke yake da sunar Ya Ahmad ɗin, tana buɗe sakon bata san lokacin da kukan da tayi ta roƙon jiya su zubo mata ba se gashi kai tsaye na saƙƙo mata, kanta take dan jujjuya a cikin zuciyarta tana sake maimaita abinda sakon yake ɗauke dashi.....

_Tun daga numfashishinmu na farko bayan wanzuwarmu a doron ƙasa,sakanni suke gangarawa cikin mintoci, hakan ne yake bayuwa zuwa ga kowacce Sa'ar dake shuɗewa. Badan komai ba sai dan ta samar da ranakun da muke kidaya makwannin da suke haifar da kowanne da kowanne watan da ke yiwa rayuwarmu giɓi, kwanci tashi nake lissafin watanni da tunanin rayuwarmu, har zuwa jerantuwar da lissafin shekarun da suka shige mana a baya, Amma idan na tuna cewar ALLAH baya buƙatarr fassara, yana ganin irin girman damuwarmu,yana kuma sane da irin girman ƙaddarar dake tare damu, kuma shi ne zai shirya bamu mafita kamar yacce yace kayan cewa. Tabbas In sha ALLAHU ba zaki taɓa tozarta ba meenoh!, Kiyi hakuri na rabu dake ba wai saboda kin sanja bane, Na rabu dake ba wai saboda na gaji dake bane, Na rabu dake ba wai dan akwai wata a rai na bane, shiru na kuma a gareki ba kiyayya bace, nisanta wa ta ba rauni bane,kawai ina yaƙi da zuciyata ne, ki gafartamin canzawar dana miki Meenoh a duk tsayin watannin da suka shude mana, ki kuma yafewa Hajiyata duk irin abubuwan data ringa miki wanda samm ni a karan kaina ko hakan bana son tunawa, ki ɗauka cewar wannan ɗin Ita ce ƙaddarar mu, zanci gaba da miki adda'ar Ubangiji yaci gaba da baki kariya a koda yaushe!, Ki ringa yawan tunawa kuma da cewar. Har abada akwai waɗan da zuciyarmu ba zata taɓa dena ƙaunarsu ba, saboda girman halaccinsu garemu na gode My Ameenatou......._
Chapter 27 · 0% Book details