← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 36

Sashe 32

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk se jikinta yayi sanyi ta ringa rokar tafiyar Meenal ɗin tace babu komai ita dama bata taɓa riƙe taba, don kowa yayi na fari kai nasa. Cikin kwanaki uku kuwa Malam ɗin ya ƙira Alhaji Ibrahim Shareef ɗin har ƙofar gidansa ya masa nasiha,yace kuma ya sani auren Meenal dama ALLAH yayi bame tsayi bane, kawai dai ita ta zama sila ne, wanda dama komai da yake faruwa a cikin duniyar yana da sila ko sanadi, yace indai don akan auren Meenal ɗin ne ba niyar juyama matarsa baya yayi ba to yayi hakuri ya maida ta,nan jikin Abban Ahmad ɗin yayi sanyi ya sake godema Baffan ya nufi gidansu Maman kai tsaye, anan gaban Maman ya sake ƙare mata tanadi ya kuma warware mata duk maganganun da uban wacce tafi tsana ɗin fiye da komai ya sanya shi amincewa ya dawo da ita ɗakinta, kuka ta dinga yi tana cewa sharrin zuciyane dana shaidan amma In sha ALLAHU bata sakewa ta tuba,tuba kuma na har gaban abada wllh. ALLAH sarki akace uwa uwace duk kuma inda ɗan uwa yake daɗi ne, haka kafin ta koma Maman ta sake bata wasu sirrika irin nasu na tsofin da da su suke kame zuciyar mazajensu, ta kuma sake mata faɗa da nasiha sosai kana ta koma gidanta. Sannu a hankali ta ringa sace zuciyar mijin nata duk da dama can ita ɗin ce a ciki, sedai rashin kirkin ta yasa ta fita a kan nasa, Gyaran kwanakin da kawai tasha a wurin Maman nata da adda'a 'oin data ɗorata akai suka fara tasiri, tuni ta sake janyo zuciyar mijinta gare ta, adda'o'i kala kala Maman ta bata, har da wani sirri data bata ganin yadda Ibrahim ɗin ya ɗan wazana Yar nata, tace ta nemi tsamiya cikin tafin hannunta biyu, wacce ba'a bare ɗin nan ba se da kanta ita ta ɓareta ta jika a cikin ɗan kofi haka, daga safe zuwa dare zata barta ta jika, idan dare yayi se ta ɗauko kofin data jiƙa tsamaiyar nan nata se ta karanta YA WADUDU, ƙafa bakwai, kowacce ƙafa ɗaya ta tofa a cikin ruwan, bayan ta kammala seta shanye ruwan ta ce da yadda ta bare wannan tsamiyar ta shanye ruwan ta haka ta ɓare zuciyar mijinta ta shanye, ta ce ta bata wannan sirrin ne kuma ba dan ta yi cuta ko tun kaho ba, ta bata ne kawai don ta kwato ƴan cinta daga wurin mijin nata da ƙawa ta mata kwace.... Kwarai ta bata sirrika da yawa masu kyau irin na gargajiya....

★..

Ahankali jirgin ɗaya taso daga ƙasar Istanbul ya fara landing a babban filin jirgin Aminu Kano, ahankali fasinja suka fara fitowa zuwa lokacin daya sanyi kansa shima a natse cikin layin passingee's ɗin dake fitowa a natse. Wata iska ya shaƙa ta ƙasarsa da kusan 3 months kenan da baya cikinta, sakamakon damuwar data kusa haifar masa da ciwon zuciya ya saka Daddy'n tattarasa ya komar wurin Yayansa ABDOUL-MAJEED, da dama sunansa ne Majeed ɗin yaci, Kansa a ƙasa ya fara tafiya yanajin kamar wacce aka yi safarar zuciyarsa daga wata ƙasa zuwa ƙasar ne, Taku yake yi cikin natsuwa wanda kallo ɗaya zaka masa kasan cewar ehhhh lallai MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ba ƙaramin jarumin namiji bane, yanda yaje kan matakin girmansa daya ɗara samartajarsa, se dai kyaun jikinsa ke ɓoye hasalin shekarunsa. duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai sedai yanayin murjewan fata dana jiki kawai wanda hasalin Luxury da Luxury suka gama ratsawa, se dai Yanayinsa kaɗai zaka kalla ka tabbatar da cewan lallai ba lafiyansa lau yaje ba .Amma darajar addininsa hadi karamci da kuma tsananin kwarjinin sa suka shanye yanayin san na kowanne irin halin da yake a ciki, Toyota Camry TRD ɗin da tazo ɗaukarsa ya nufa, sedai ga mamakinsa Bilal ne tare da Ikleemerh dama Ayla. Rumgume Ayla a jikinsa yayi yana sakin wata wahaltacciyar ijiyar zuciyar kewarta da kawai yayi. Hannu Bilal ɗin ya basa suka gaisa, Ikleemerh ma ta gaidasa ya amsa cikin kulawa kai tsaye suka lula zuwa gida...

Meenerl....

Alhamdulillah abubuwa sunci gaba da gudana cikin rayuwarta, inda dama bata da wata idda akan ta sakamakon barin cikin da tayi, sosai Baffa da yan uwanta sune ƙoƙari akanta,kafin kace me har masoya sun yi ca a kanta ciki kuwa harda samari don sunce ai sauta ga wawa ce, tin da ko shakera ba tayi da auren ba kuma ta fito, gashi ko haihuwa ba tayi na, sedai bata taɓa kula kowa har se da Baffanta ya mata magana, yace ta ɗauki dangana kuma ai dole zata yi auren ba wai ta ƙare shi bane da wannan ƙananun shekarun nata, kuka ta saka masa a lokacin tace ita Allah tsoron mazanma take, tsoron tayi zaɓen tumun dare take yi, nan su Yaya Sadeeq suka yi ta bata baki, ga nan ma wani nan cikin anguwarsu daya nuna yana son nata amma taƙi, don matarsa bata da mutumci suna na gaba gaba wajen aibantata a lokacin da wannan ƙaddarar ta sameta, don haka tace bata son shi, ita ta ma rasa ta yadda aka yi mutane suka san da maganar sakin nata, ita da tin da abun ya faru zata iya irga fitanta dududu be fi uku zuwa huɗu ba ƙarewa maza suka mata Caaaa aka. Se dai ana tsaka da wannan danbarwa se ga bayyanuwar Alƙalin daya mata Shari'a, wato ALƘALI YAHAYA SHEHU ƊAN BATTA shima ya faso cikin maneman nata, wanda tsananin tausayinta a karon farko ne ya addabi rayuwarsa, bayan ya bibiya lamarinta har ya gano mijinta ya rabu da ita, sedai beyi gaggawa don se wajen wata na biyar kana ya bayyana, wanda kai tsaye kuma ta hannun Baffa ya biyo ganin shi ba yaro bane, kawai ra'ayinta za'a tambaya masa ita in tana yin sa shikenan, wannan karamci da Baffan ya masa ne yasa har yake jin har abada ba zai taɓa mantawa da shi ba,a lokacin da Baffanta yake tinkararta da maganar se taji ta ɗan fi samun nutsuwa akan sauran mane man nata, don haka Baffan ya bashi umarnin fitowa yace ba da gaggawa haka ba, don yana son su fahimci juna kafin komai, don shi rayuwar soyayya yake son suyi bata alfarma ko ta girmama juna ba, don yana son soyayya sosai gaskiya, ɗan dudu du ba zai wuce 40 year's ba. Kuma jikinsa a gine yake daidai misali don haka ya fara zuwa zance, Maganar aikinta da ada har zata koma ta koma baya, ɗaukarta yake yana kaita wuraren shaƙatawa yadda zata sake sakewa dashi, ta kuma manta da giɓin dake cikin rayuwarta cikin sauƙi. ALHAMDULILLAH kuma sun fara fahimtar juna har tana jin sa cikin zuciyarta, Dake anan cikin Kanon yake anguwar SHARAƊA PHASE 0, kuma matansa biyu ata uku zata je, sedai ba gida ɗaya zasu zauna ba amma Baffanta yace inda hali ya haɗesu a gida ɗayan, sama yana da wadataccen gidan kawai dai dan kar ya zama kamar ya tauyi haƙkin tane ya saka shi ware mata gidan, amma se da ya sake tambayarta tace ba komai ALLAH ya basu zaman lafiya. 3 months ya saka bikin domin akwai buƙatan yayi wasu ƴan gyare gayre, ana saura 2 weeks bikin aka kawo lefen da ya bama koma mamaki don kowa be sha har wani laife ze mata ba, amma ga mamakin kowa se ga akwatu har guda biyar da kaya na kece raini a ciki, dede da wayar hannunta ya jima da sake mata ya sai iphone 13 pro max. Kuma gata hannunta Pop 9 Tecno, se ta barma Shareefah Pop ɗin nata ita kuma ta bama Bilkisu nata da itama babbace babu laifi, gwaggo Sadiya dai kada ran kada han haka take tsakanin nasu. Se ta ga dama take shiga lamarinsu in bata so bata shiga, amma su basa taɓa renata, ko kayan lefen ma a dakin gwaggo Sadiyan yake.... Kuma sunci gaba da mutumcinsu da Dr pooja har takan zo mata ma.

A lokacin da ya dawo Risach nata ya fara yi amma yaga bata dawo wurin aikin ta ba, don haka se ya cire duk wani abu daya danganceta yaci gaba da rayuwarsa kamar baya, Sedai yafi bama aikin company'nsa ƙarfi fiye da hospital ɗin, gashi ma shirye shiryen bikin Ikleemerh suke suma nan da 3 weeks.......

Kwanci tashi aka ce asarar me rai se gashi har ranar tazo, sosai Meenerl ta sake yin kyau na musamman wanda farin cikin wannan aure babu ya Shareefah don tana kallar kamar wahalar yayar nata ne ya yanke yazo ƙarshe se dai aka ce kashh?..... Cikin nutsuwa da aminci aka gabatar da komai cikin kwanciyar hankali,sedan tin da ake abun babu mahaifiyar Alƙali ko kaɗan. Ranar da aka ɗaura mata Aure da Alƙalin ranar saura ƙiris Ahmad yabar duniya, amma kuma yana nan yana Adda'ar ALLAH ya fito da ita in yaso komar da ita, tin da dama haramta auren ai yayi, kuma zuwa yanzun Ummansa ta sake musulunta dan har wurin bikin ma tazo, tana sake kuka tana cewa ALLAH yasa Meenerl ɗin rabon ɗan tace, su a nufin su kamar tayi Auren kisan wuta kenan ta fito se ya sake aurenta, a ranta take jin batayi wannan auren don ta fito ba, kuma ko babu komai hankalinta ya sake kwanciya da Alƙali Yahaya Shehu ɗin tin da ya ɗan manyanta yasan darajar sosai, ita kuma dama can ba son ƴan bama bakwai ɗin nan tayi ba, sedai idan ta tuna cewar cikin mata uku zata shiga gabanta kan faduwa time to time, amma data gayama Yaya Sadeeq shi kuma ya faɗa ma Baffa se ya saka wani ɗalibi mata rubutu na tsawon sati guda, kuma Alhamdulillah ta rage jin hakan, har sauƙa Baffa ya mata tun da yaga wani shirun baya isar wa, kuɗinta da Ahmad ya turo mata lokacin daya mata sakin nan dubu ɗari biyar ta bama Baffa ya sake mata kaya masu kyau, duk da be so amsa ba amma haka ta matsa masa.
Chapter 32 · 0% Book details