← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 36

Sashe 7

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Meenerl kuwa yau se aikinta yafi na jiya yawa don har sun sau mata ragamar fara aikinta gadan gadan, harma sun gama tsara mata time table na lokutan aikin nata, a sati tana aikin tin daga safe har zuwa yamma sau uku, daga yamma zuwa safe sau biyu. Koda ta koma gida take bashi labarin be ce mata komai ba, har ya fara gudanar da aikin nata, a memakon shigar da take ya sanja sema sake ɓauɗewa da take, amma se ya tattarata duk gefe guda yaga iyaka nata gudun ruwan, itama kuma bata damu ba haka har suka cinye tsawon wata guda kenan a hakan, idan tayi bacci yakan ɗauka wayanta time to time bawai don yana zargin tana sedan kawai tsaro da kariya, baya shiga duk abinda ya danganta family issue nata, be kuma taɓa kamata da aikata ba daidai ba, sedai yakan tsinci video's nata tsilli tsilli duk ranar da take da kwanan asibiti tana yar rawa abinta, wanda take yi a tiktok seta yi sev nashi akan wayan,seta goge daga tiktok ɗin da dama a private account nata yake. Amma na yau ɗin se yafi na koda yaushe daga masa hankali don kuwa daga ita se wata sky ɗin rigan baccinta iyaka gwiwwa kanta babu kitso a tubke ƙasar ƙeyarta, ga hannun bra nata nan ɗaya ya fito koda saninta kodai akasin hakan, se ya shigawa WhatsaAp nata ze tura a wayanshi amma se wani abu ya ɗauki hankalin sa a cikin wayar nashi, wato kamar sabbin status da sunan _BESTIEN BESTY_ ke ɗauke dashi, don haka kai tsaye ya shiga status ɗin ya kalla, video'n daya gama kalla yanzun ne tayi status dashi, duk da kasancewar ta saka hoton love ta kare jikinta amma kuma ai be dace ba, inta kare ƙasan saman kuma fa?, nan ya shiga na biyun yaga ol de same da wancan ɗin, shi wannan da tana yi har kamar wulgawar wani namiji ya gani da kayan likitoci sanye a cikinsa. Guda uku ne don haka na ƙarshen tana tafiyane tanayi tana sanye da kayan ta na aiki ta a video ɗin, view na mutanen da suka kalla ya duba, yaga sama da mutum goma sha biyar har sun kalla, cikin kuwa harda classmate nata, fitowa daga wurin status ɗin yayi yana duba na farko farkon da suka fara mata message, nan ya kalla na Yayanta Sadeeq da shi kai tsaye cewa yayi Lallai lallai maza maza ta sauƙe status ɗin, bata bashi amsa ba duk da ganan taga message nashin, daga nan yaga group
na school mate nasu saƙonni nata shigowa, don haka se hankalin sa yafi karkata wurin kawai ya shiga, shi dai wannan video ɗin da tayi status dashi ne wata daga cikin freind nata da suka kalla ta tura musu, a ƙasan video ɗin ta rubuta. _Gafa mutuniyar an fara ɗaukan haske...._ Mutum na farko kuma daya fara magana akan video ɗin na miji ne, me suna Hasheem Al'asan, shi ne yace. _Ohhh ALLAH Yarinyar nan wai dama zata waye haka?, kodan No wonder daga yanayin tsiwa da rashin kunyar tama, idan kuma aka haɗe da kalan mijin data samu lallai dole ne ta numfasa itama...._ Se na biyu shima dai namijin ne inda shi kuma yace. _Wooo Malam yarinya ta gama timbatsa ba, ta zama wata se kace renon madara da A/C....._ se ta ukun kuma macece ita kuma tace. _Shegiya nera wato dai shi kuɗi da jin daɗi babu abinda baya saka mutum aikatawa ci gaba dayi da kyau hakan ma India'n girl...._ namiji ne ya sake tag na hoton yace. _Je kaya alaji, gaskiya sa hijjab ma duniya, da yarinya kullum a cikin manyan kanya,amma da dukkan alamu mijin nan nata na shagwaɓata da yawa..._ _Yo ba dole ya shagwaɓata ba ya sama wanga ganima haka, dole ai yayi ta bata tana kwashewa ita kuma...._ Wani kalan rumtse idonsa yayi ganin duk cikin maganganun babu na kirki, babu kuma wanda aka samu ya ce tayi ba daidai ba, se dai masu yabon tama. Dubawa yayi yaga itama group admin ce a group ɗin, don haka kai tsaye ya goge video ɗin, tare da exit kanta daga cikin group ɗin gaba ɗaya, yana fitowa ga mamakinsa duk da kasancewar lokacin wajen karfe ɗayan dare ne se yaga wani guy har ya biyota private yace. _Haba India'n girl ya zaki mana haka uyhmmmm?, bafa mu riga munyi saving video ɗin nan a wayoyinmu ba kika goge?, kana kinyi left daga cikin group ɗin, halan Mijin kine yasa ki fita ko???, Hhhhhhh yayimin dai-dai ta wani fannin kuma be kyauta min tin da duk mun sakan kance bamu yi sev na video ɗin cikin wayoyin muba, ita kuma waccen Yar Is ɗin data ɗora na mata magana naga bata online, dama ita kowa yasan kasa ce uwar yan bacci, amma zuwa safe na mata magana ta turomin, in kuma zaki bani zan yi farin ciki da hakan, daga Jinior Ahlam kd_ take wani mummunar ɓacin rai ya sake kume zuciyarsa, kai tsaye ya rubuta masa.

_Come to your senses and calm down, otherwise I may mislead you or end your life in prison, be careful..._

Daga haka yayi block nashi yabi yarinyar data É—ora video É—in, yace mata.

_ The biggest mistake you will ever make is to forward this video to someone else, because I will look at every possible connection between the two of you and I will have you arrested, an arrest like forever, so be careful, From Meenal's husband Shehu Usman_
Chapter 7 · 0% Book details