Sashe 23
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Kiyi hakuri ameenatou ki amsa wannan ƙaddarar, domin rayuwa ba zata taɓa ginamu kamar yacce muke so ba, harma abinda muke ganin yafi ƙarfinmu na iya zama abu mafi sauƙi da zarar munfi karɓi zaɓin da ALLAH ya mana, se kiga zuciyoyinmu sun sama nutsuwa ata sanadiyyar hakan... Ameenatou ina son ki saka a ranki cewar har yanzun rayuwarki na nan matuƙar kina numfashi!, duk wani zaɓi yana hannunki idan kika so ki sanja dole ne ki fuskanta matsalolinki da kanki, muddin zuciyarki naci gaba da aikinta na bugawa. Kin ga kenan har yanzun zaki iya sake *RUBUTA LABARINKI...*, Amma se kin fara fahimta da sanin cewar yin haƙuri yana kawo nutsuwa, yin godiya ga ALLAH yana ƙara ni'ima,yin adalci kuma yana samar da aminci da nutsuwar zuciya......" Se kuma ya ɗan fesar da wani huci me zafin da yaji yana nemar kuncushe ƙirjinsa. Kafin yaci gaba da fadin..... "Duk wanda yayi Adda'a sannan ya kyautatama ALLAH zato, to kuwa ya jira zuwan mafita daga gareshi zai sama ladan wannan jiran da kuma kyautata zaton da yayi, domin kyautata ma ALLAH zato da kuma tsammanin mafita daga gare shi suma ayyukan ibada ne, don haka kada jinkirin amsawa ya sanya ka sare!!!, ko kuma munana zato ga ALLAH, domin ALLAH yayi alƙawarin amsawa amma a lokacin da yace, don haka gaggawarka ba zata sanya ALLAH gaggawa ba... Ki wanke hawayenki da ruwan alwala,kiyi sallah, ki ɗaga hannayenki sama ki zayyanawa ALLAH damuwarki da buƙatarki. Idan zuciyarki tayi nauyi da damuwa ki sani Rahamar ALLAH tafi damuwarki yawa!, idan duniya ta matseki ki buɗe zuciyarki da tuba da istighfari.... Babu hanya mafi sauƙi na cire damuwa fiye da sujjuda a cikin dare, damuwa ba zata taɓa dawwamaba!, domin ALLAH yana tare da masu hakuri, ki riƙe alƙawarinsa domin shi ne da kansa yace... *INNA MA AL' USRI YUSRA* ki ɗaga hannunki ki kuma fuskanci sama ki ce.... *HASBINALLU LA'ILA HA ILLA HUWA,ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHIM AZEEM....* Zuciyarki zata huta!, za kuma ki sama nutsuwa, kwanciyar hankali kuma zata sama gurbin zama a cikin zuciyarki.... Ki sani tsoro ba zai taɓa gina mutum ba, sedai ya ruguza, domin ita kanta rayuwar ƙalubece. Amma ita nasara tana zuwar mana ne tamkar kiftawar ido,kamar yadda ajali ke zuwar mana kamar kiftawar idon shima. Anan ina son ki sani cewar damuwar da za'a barta a cikin kwakwalwa tafi kowacce kalar damuwa cutarwa, ki amayar duk abinda ke cikin zuciyarki ki kuma tsarkake ta tsarki irin na gaskiya da gaskiyar da ALLAH ke so, za kiyi albarka In sha ALLAHU....." Kuka sosai take yi wanda sautinsa ke fita da amo da kuma irin raunin dake bayyana me yin sa, Tsaye mahaifin nata ya miƙe hannuwansa a gadon bayan sa yace.
"Ameenatou a yanzun kuka ba shi ne mafita ba.... Kiyi Adda'a ki kuma yi injoining na ƙaddararki In sha ALLAHU duk bayan wani tsanani sauƙi na bayansa.... Daga haka ya fita. Bakinta yake son buɗewa tama Baffan nata magana, ta masa godiyar Adda'a da nasihohinsa gare ta amma kukan daya sarƙe maƙoshinsa na hana mata hakan, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro, ta jima tana yi kafin ta share wata irin nutsuwa da sanyin kalaman mahaifin nata gare ta na ratsa ilahirin jikinta, kukan da ya zama mafarin buɗewan yin sa kenan a cikin rayuwarta, domin kuwa daga wannan tangarɗar daya faru da ita daga nan ƙaddarar ta fara. Tin da ta shige ɗakin sallace kawai ke fito da har aka yi isha'a, tin kuma data shigo gidan gwaggo Sadiya bata ko leƙo taba, Bilkisu kuma tana maƙarfi taje wurin dangin Ummanta wani biki da suke Malam ya hanata zuwa shi ne ta tura Bilkisun. Bayan sallar isha'a ɗin Ya Sadeeq ya shigo tare da Ya Ahmad har tsakar gidan, dake gwaggo ƴar duniyace harda su ahimfiɗa tabarma, a mutumce ya gaidata sega shigowan Baffan shima, ɗakin da Meenal ɗin ke ciki duk suka shige, wanda hakan bema gwaggo Sadiyan daɗi ba, don haka ta wani ja tsuka tana furta.
"Munafincin banza..."
Bata sake sarewa da lamarin ba seda ta sake ganin Ya Sadeeq da Ya Ahmad sun sako Meenal ɗin tsaƙiyarsu, ita kuma se famar share hawaye take, domin gani take da ba sai ta koma gidan Ahmad ɗin ba, don tasan koda ace ta koma ɗin taƙi kaɗan ne ƙaddara zata raba zaman nasu. Haɓa Gwaggo Sadiyan ta riƙe a bayyane tace. "Ji wata ƙaddarar liman da sket....." Wanda ya saka Ya Ahmad waywayenta banda sauran da ko kallo bata ishesu ba su duka, har bakin motarsu suka rakata ta shige gidan baya, duk yacce Ahmad ɗin yayi data shiga gidan gaba kuwa, ita kuma ta zaɓa gidan bayan ne yadda zata fi sakewa ta kwanta sakamakon cikinta dake mata wani kalan ciwo da marar ta. Koda suka kawo gidan yaso taimaka mata amma ta dakatar dashi ta yunƙura da kanta ta nufi cikin gidan, kai tsaye ɓangarenta ta wuce ta rufe babu jimawa kuma se gashi ya biyota har nan ɗin, zama yayi daga ƙasan da itama take daf, hannunta ya kamo cikin tafin hannunsa yana ɗago fuskanta kuma da ɗayan hannun, ga mamakinta ruwan hawaye ta gani kwance sharkaf a saman fuskarsa, hannunta dake cikin nasa ya ɗan damƙe, tare da soma magana.... "Komai kikaga ya faru da bawa dama can tin daga Rabbil Izzati ne hakan, don haka nake son ki fawwalama ALLAH duka lamurran, kana roƙon da nake son na miki da kuma Alfarmar da zaki min shi ne....." Se kuma wani kukan ya sake sarƙe maƙoshinsa ya kife kansa a jikin kafaɗarta yace. "Duk yin Duniyar da za'a yi akan cikin nan karki furta komai indai kinsan ba nawa bane zaki ce, naji na kuma gani har cikin zuciya ta na wuce zan kuma karɓi wannan ƙaddarar da duka hannayena biyun nan..." Yay maganar yana ware mata tafukan hannayen nasa. Kana yaci gaba da furta. "Nie banji ma a jikina cewar cikin nan ba nawa ne Meenorh, kwanaki biyar ɗin da kika ɗora ina kallar kamar hindawar wasu kalmomi ne kikai kika aza bisa watanni huɗun, na ji na gani koda ace ba nawan bane kada abinda yasa kika shigo da maganar wannan cikin kinji *ZUCIYAR AHMAD IBRAHIM SHAREEF.....*, mu roki ALLAH gafararsa!, mu kuma rokeshi da ya yafe mana kusakuranmu na baya, ya bamu juriyar ci gaba da gudanar da rayuwarmu kamar baya koma zarta hakan..." Kuka sosai take rerewa a jikin nasa kafin cikin muryan da kuka ya gama cinyewa tace..... "Ta ya kake tunanin ni zan yarda na yaudareka, bayan na gaza kare maka kaina martaba da kuma darajata data aurenmu?, Ya Ahmad na gode da kalan haliccinka gareni kuma bazan taɓa mantawa da wannan masoyin na gaskiya da gaskiya ba, Sedai banji a jikina cewar zamanmu zeci gaba da gudana a haka ba, koda ace zai ci gaba ɗin dole se kalmar saki ta shiga tsakaninmu naje nayi istibra'i na tsarkaka kaina daga dattin zinar dake tare dani. Sena haife abinda ke cikin kina na ware shi daban, domin kuwa bazan taɓa cakuɗashi da yaran da zamu haifa masu tsarki ba I LOVE U too much love Ya Ahmad......" Daga haka ta kwace jikinta a nashi ta shige bathroom tana rufewa duk yacce yata mata magiya da roƙon ta buɗe masa amma ta ƙiya, kuma take wanda bata san ya matsaya da iyaka tsayin da yake da ba, kukane irin na kai da kai ɗin nan, kukane da iyaka me yinsa kawai ne yasan illarsa ga lafiya da gangar jikinsa!, kuka ne irin na wanda ya gama sallamawa.....
Sati guda cif suka shafe suna fuskantar azabtarwar da suka zaɓa suma junansu, taki aminta dashi, taki amsarsa a matsayin mijinta, domin tace masa ita ɗin a yanzun tamkar wata datti da zunubi ce, a kuma cikin waɗan nan satikan babu kalar barazanar da bata gani ba daga su sen Garba Aliyu na Yaya, Sedai ALLAH ya kan tseratar da ita daga jami'an ɓoyen da Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ ya zuba musu a gaba ɗaya anguwar ba tare da sanin daga ina jami'an suke ba, ita kanta ba tare da saninta ko mijin taba, don wani lokacin se ya fita zuwa wurin aikinsa kana suke affecting na shiga gidan, ganin babu nasara ne ya saka Hajiya Madinah cewa kawai a shiga kotu, don haka kwana biyu bayan haka se gashi har office an kaima Ahmad takardar fara shari'an, tun da gidan babu dama shiga, wannan abu shi ya sake tada hankalin Ahmad daya dawo gida a birkice, Me makon ace shine zai kwantar mata hankali se ya zaman ita ce ke kwantar masa hankalin, cikin ƙwarin gwuiwar jin cewa zata fuskanta duk abinda ke tunkaro ta, wannan daren da mutane suka gaza runtsa bacci, yanda Ya Sadeeq yaga Wannan tsayin dare haka shima Ya Ahmad ya gani, ita ɗin ma haka ta gani sedai ita zamu ce ta raya daren da bautama mahaliccin ta kukanta, ta yi masa kirari ta kuma roke sa akan ya kawo mata mafita ya kuma zama gatanta....