← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 36

Sashe 31

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

♡ ♡ ♡ ♡
ꨄ ƙarar data fasa ne ya saka Ya Sadeeq da Baffa da Bilkisu har dama gwaggo rige rigen shigowa dakin nasu. A sanƙame suka ganta jikin Shareefah ɗin gaba ɗaya jijiyar kanta sun gama fitowa sun yi ruɗu ruɗu. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Ya Sadeeq ya ambata shikenan abinda suke ta gudu ɗin ya faru, mutanen kan Meenal ɗin sun motsa, wani kalan tashi hankali muraratan kake kalla daga cikin idanun kowannensu, don kuwa jinya ce ta sau da tari ma sukan mance da cewar Meenal ɗin na ɗauke da ita, wanda suke kamar gadon mahaiyar tane tayo, idan tsanani yay tsanani suka tashi to sukan shafe tazarar kwanaki da suke ganin ace akai akai ɗin ne suke tashi, a wannan sanƙamen da take takan iya kaiwa har gobe uwar haka bata ko motsa ba, duk kuwa kalan ƙarfin adda'an da ake mata, idan suka tashi gaba ɗaya se hankalin kowa ya tashi, wannan shi ne karonta na uku kenan a tashin nasu, bata motsi bata numfashi babu alamar me rai tattare da ita. Se jijiyar babbar yatsarta kawai da take harbawa wanda shine zai baka tabbacin cewa tana da rai, a gabanta Ya Sadeeq ya zube yana amsar ta daga hannun Shareefah Baffa shima yakai tsugunne suna fara tofa mata adda'o'i masu kyau, har zuwa wani lokaci can cikin dare kana suka fita kowa ransa babu daɗi aka bar Shareefah da Bilkisu wacce da cewa yay gwaggo Sadiya ta kwana da ita tace wllh ba da ita ba, ita dai Bilkisun da taga zata iya bismilla to ga wuri na ta tsallake ta fita, su biyu kwana da ita a tsakiyar suna ci gaba da mata adda'a ɗin har bacci ya ɗauke su suma, bayan sun yi kukan sunyi har sun gode ALLAH. Ko washe gari haka yaran Malam suka ringa shigowa suna ma su Shareefah sannu dame jiki, ido duk yay jeme na alamar fita a hayyaci, Malam kuwa kusan kwana yayi zaune akan binciken ire iren matsalolin aljannu masu shige da nata, don haka da kyar ya samo wata hanya me ɗan tsauri. Da sassaucin abin ya tashi bayan Sallah a masallaci ya aiki Sadeeq Jigawa amso masa magungunan wurin hasalin tsohon malamin da ya koyar dashi. A asuba ɗin ya tafi sha biyu kuwa bata kai ba se gashi ya dawo da magungunan dana shaƙawa dana hayaƙi, wanda mafi ƙarfin cikinsu da saurin dawo da sinadaran ƙwaƙwalwa shi ne ɗan tumfafiyar da aka busar dashi a inuwa, tare da lafar ganyensa ɗaya da ɗan ɗaya se a rubuta _WALA YA HUDU HU HIFZU HUMA WA HUWAL ALIYUN ALIM, HASBINALLU LA I LA HA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHEEM AZEEM..._ SO za'a rubatasu ne a jimlamce matsayin kafa bakwai bakwai, idan ya bushe ya dake ya zama gari a shaƙama wanda yake fama da irin makamanciyar jinyar aljannu irin haka, ko me cutar farfaɗiya, to bi'izinillahi za'a sama waraka, se wasu manyan turarukan jinnul-Aashiq. Su zamfar su zauzau manyan turarukan jinnul-Aashiq ne, Shareefah fa ne ta shafe gaba ɗaya jikinta dashi wajen kala uku, kana ta kama hancinta tana cusa mata ciki, a take wata gigitacciyar hatshawa ta taho mata tana wani ƙoƙarin miƙewa a gigice, Ya Sadeeq da ya shigo yay hanzarin ɗamkar ta, wani ihun da kusan seda ya saka Baffa dake waje wurin almajirai kifawa, yayo gidan wasu maganganun da basu da kan gado ta shiga yi, tana wani jijjiga tana ƙoƙarin kwatar kanta daga mummunar riƙon da Ya Sadeeq ɗin ya mata, ahankali ahankali kuma jikinta ya shiga saki numfashinta na daidai ta koma yarab bayan a kan idonsu wani abu me kama da hayaƙi ya fita ta cikin goshinta. Wata ijiyar zuciyar data saka kowa sakin tashi shima ta saki tana laluben hannun Shareefah...

Umman Ahmad kuwa a lokacin da ta kai gidan ƙanwar mahaifiyarta Hajja ta zayyane mata komai, dake Hajja ɗin ba kanwar lasa bace itama tayi kanta tana faɗan ina ruwanta da rayuwar auren yaron nata?, wannan abu shi sake tuƙe zuciyarta har munanan kalaman Mijin nata suka shiga dawo mata daki daki........ "Bana son kicemin komai Yahanasu domin kuwa komai ɗin ya isa haka nan!, Na riga da na gaji da munanan halayenki Yahanasu, wallahi kinji na rantsema awannan karon kam babu makawa se kin tafi, tin har kika saka ɗan ki ya saki matarsa alhalin yana sonta, yanzu ki dubi halin da yaron naki yake ciki ko tausaya masa ba zakiyiba, ke kuwa wacce iriyar uwa ce data fiye son kanta da yawa uyhmmmm?, Karfa ki manta kema kina da yara matan nan har biyu, akwai Amina ga kuma Fatima kuma ke kin ma yima kanki adalci kuwa har dan ita uwar mijin Aminan tana takurata itama ki ringa tsine mata?, kin ga ashe babu daɗi ma kenan, baki isa ƙuntatama ƴar wasu kuma ke kice naki Ƴaƴan su zauna ƙalau a nasu gidajen ba, ƙarya ma kenan never wllh. Don haka kema dole kiji irin raɗaɗi da baƙin cikin dake cikin tozarcin aure........." Haka kalaman Mijin nata ya katse ta a lokacin suna yin dinner da yaranta ta hanyar faɗan haka cikin wani irin mugun ɓacin ran da bata taɓa ganinsa a ciki ba.... A lokacin jajayen idanunta ta ɗago tana kallarsa cike da wani kalan mamakinsa. Wani irin tsannin baƙin cikin ne taji ya mugun turnuƙeta, babban abun takaicin ma shima shine a gaban yaranta ya mata hakan,  ji tayi kanta na nemar zare mata don tsananin sarawan da yake mata kamar zai rabe gida biyu, a lokacin da take tunawa da maganganun nasa, tashi tayi ta bar parlourn wacce take madadin uwa a gare ta ko iya kallon gabanta batayi sabo da tsantsanr ɓacin ran dake cunkushe da ita, har tana fidda wani numfashi mai zafi.  Haka ta wuce uwar ɗakan Mamar tata tana sharce hawaye, se gashi abu kamar wasa ko Fatima Abban ya hana zuwa inda uwar take, bare me dungurin uwar du ɗin Ahmad, wasa wasa har ta cinye satin farko ta shiga na biyu, idan ta ƙira wayarsa baya taɓa amsawa, tin da ya taɓa bata amsar cewa sai idan buɗar ido kawai yay yaga Meenerl ta dawo ɗakinta, kuma har gida ya sake zuwa shida Ahmad ɗin suka sake bama Baffa hakuri yace wllh babu komai, amma zancen kome kam babu shi, haka ma sun gode ALLAH ya amfana zaman da aka yi baya, Umman bata tashi aune ba se ganin katin ɗaurin auren Abban tayi ita da wata tsohuwar aminiyarta ta ƙut da ƙut, da duk wani tafarkin rashin kirki ita ke ɗorata akai ta aure mata mijin, aikuwa tayi kukan kura irin na mahaukatan nan ta buzanta taje har gidan ƙawar nata me suna Lubna suka kwashe tsiran karen mahaukaciya da ita, ta ce ita ai bata faɗa da mahaukata jahilai sedai da masu hankali. Aure ne kuma ta kwantar da hankalinta kamar anyi an gama ne ita da masoyinta IBRAHIM SHAREEF, tace mata babu boka babu malam kamar yadda ta sani a tsarin shedules nata, amma kuma tsantsanr makirci da kisiisina za suyi aikinsu da kyau, kuma ta zuba ido tayi kallon ikon ALLAH. Anan sema ta rasa bakin magana taje gida kuma zata ma Maman nata rashin m ta dakatar da ita ta hanyar mata tass,tace ai da lokacin da take bata shawarwari akan ƙawayen banza bata ji, gani take ma lokacin da ba ita ta haife ta bane take mata hassada, har takai ta kawo seda ta ɗauke ƙafarta cakk daga gidan Maman da itace ta reneta tin daga haihuwa, wacce uwarta na haihuwar ta ta mutu, wacce kuma a lokacin uban ita yahanasun da take aure yace ba zai riƙe taba shima rashin sa'a da baƙin halin jaririyar ya shafe sa ko ya kashe saba, ita ta rene ta shayar da ita amma daga ƙarshe sakamakon data bata kenan na tsameta daga cikin rayuwarta gaba ɗaya, se da iftila'in rayuwar data gama koya mata hankali ya sameta kana ta tuna da ita, bayan auren da sati biyu sega takardar sakinta har biyu daga mijin nata ya aiko mata har gida, yace tun da ta gaza dawo da Meenal ɗin dakin nata, afujajan ta isa gidan su Meenal gaba ɗaya ta fita a hayyacinta babu alamar kowacce iriyar nutsuwa tattare da ita, haka ta din gama Baffa kuka da magiyar ya taimaka ya ceci AURENTA Meenal ta koma ɗakin ta, wanda ita kuwa zuwa lokacin ma har ta gama zubar da komai taci gaba da gudanar da rayuwar ta yacce ta zaɓa mata. Ca yay da ita Meenerl da gidan Ahmad kan babu kome amma maganar aurenta da tayi yacce wannan zai taimaka mata da ƙarfin adda'a har mijinta ya dawo gareta, yace kuma ta gane tabbas su malamai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ta inda wani malamin yana kallar ana cutata diyarsa a gidan auren ta amma ko jarkar rubutu daya ba zai taɓa bata ba da sunan mallake wani, kuma itama yace babu rubutun da zai mata amma taje za taga ikon ALLAH In sha ALLAHU....
Chapter 31 · 0% Book details