← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 36

Sashe 20

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka baki ɗayansu suka tsinkayi muryan Meenal ɗin data fito da fuskanta duk abin hawaye ya gama bushewa, idanunta tsabar kuka kuwa sun zurma sunyi ciki. Ahmad ne yayi hanzarin shan gabanta yana me furta. "Wa ya baki umarnin ki fito?" Kai tsaye tambayar da ya fara cilla mata kenan, "Sabo da ni aka zo nema!, kuma ko da ace ban fito ɗin ba dole zasu fito dani........" Ta sake faɗi tana ƙoƙarin nufar kwalawan. Kyakkyawar Garkuwa Ahmad ɗin ya bata ta hanyar tare gabanta da yayi daga shirin miƙa kanta ga kwalawan da dake, Zuciyarsa harya fara tafasa yace "Zaki koma ne ko se na saɓa Miki?" Ya sake faɗi daidai janye san da wani police yayi daga gabanta. Ya Sadeeq ne ya iso gabansu yana sake shiga tsaƙiyar police ɗin da ita. Cikin ɗan yanayin fusata yace."Na ce muku da nine wanda zaki tafi ba ita ba amma" Ganin renin hankali da wasa da aikinsu da duka su biyun ke yi ne ya saka Wannan ƙaƙƙarfan police ɗin buga musu tsawa, yana me furta "I like that..." Daga haka yama macen dake tare dasu inkiyar ta kama Meenal ɗin, hakan kuwa akayi ta kamo hannunta tana zira mata Onka. Wani irin rinewa idanun Ahmad yayi zuciyarsa na ƙoƙarin masa bindiga. Kafin ya isa gabanta ya ce. "Abin da kike zaɓa kenan?, kariyar da muke shirin baki kika ture Meenal?, Kika zaɓa tozartamu da ƙasƙantar damu a idon duniya?...." Ya faɗi hawaye na zubo masa. Hannayenta duka biyun dake cikin onkar ta sa tana goge nata kwallar da ya ciko nata idon, kafin cikin ƙarfin gwiwwa da yaƙi ni tace. "Ko da ace ban yi hakan ba bazan taɓa tsira ba Ya Ahmad, dole gaskiya tayi halinta, dole komai ya bayyana, Me bi wannan ita ce zata iya zama magana ta ƙarshe da kai Ya Ahmad, domin kuwa na san koda na fito bayan gaskiyar komai ya gama bayyanuwa doke zaka rabu dani, domin abinda ke ɗauke a jikina da kasancewar sa ɗan duma ko an ɓoye se ya bayyana. Abinda kawai nake buƙata daga gareka shi ne Adda'a da fatan Alkhairi, tare da Adda'ar zaɓin abinda shine mafi Alkhairun mu garemu. Tabbas dukkan ayyuka suna tabbata ne da niyya,kuma Lallai ko wanne mutum yana samun sakamako ne na abinda yayi niyyar, Ubangijii ALLAH yana gani kuma shi ne wanda zai bani kariya, karka ji komai, domin nie a yanzun babu abinda nake jin ɗin kuwa... Face na bayyana gaskiyar abinda yake akwai ciki kuwa harda bayyana cikin dake jikina daya kasance na wannan dabbar ne...." Ji da ganinsa ne suka nema ɗaukewa lokaci guda, me take nufi da cikin jikinta?, tana nufin ciki ne ke ɗauke a cikin cikin nata irin na haihuwar ɗan mutum dai?, me ya sa shi da ita bata taɓa fada masa ba?, me yasa be taɓa lura da hakan ba da suna zaune gida guda har cikin yayi wannan watannin a jikinta be sani?, Haba No wonder ranar yayi ta kallarta, ramar tayi yawa, zafgewar bici ace ta iyaka damuwar da take a cikinta bace, shi kuwa me yasa be tsaya ya fuskanta matarsa ba, me yasa fushinsa gare ta har ya bari yaja lokaci haka?..... Kansa ya riƙe yana ɗan jujjuyawa yana ambatar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un a cikin kansa. Idanunsa na dishi dishin lumshewa yake ja baya yana cewa kar ta masa haka, karta yarda ta sako maganar cikin nan, nashi ne!, na shi ne!!, Ze amsa yana son ta yana son duk wani abu daya kasance tsatson tane.... Yana ji yana gani suka tafi da ita, tafiyar da ita ce farko da kuma ƙarshen rayuwa da duk wani farin cikinsa, tafiyar data tafi ta barshi na har abadan da dama ta riga ta gama ambata mishi, Kuka ya saki a wurin tamkar wani ƙaramin yaro yana buga kansa da jikin biyar settline ɗin dake tsakar compound ɗinsu, Ita kuwa zuwa lokacin idanunta sun gama ƙaiƙashewa sun bushe babu alamar hawaye, domin zun riga da sun gama zubar da iyaka ruwan da zasu gama zubar wa ɗin, sun soye kuma yanzun sun ƙaiƙashe, bata jin kuma akwai abinda ze sake sakata kuka yanzun. Da kanta tana layi tana komai ta shige cikin motar suka buga suka bar gidan da ita. Ya Sadeeq ne yayi hanzarin yin kan Ahmad ba wai dan shima tashi zuciyar na cikin sauƙi da nutsuwa ba, sedan haƙurin daya gama bata ya jure ya taya ƙanwar tashi gwagwarmaya, ya taya ta yaƙin har se inda ƙarfinsa ya kare shi ma. Ciki ya shige da Ahmad bayan ya ƙira gidansu ya sanar da iyayensa abinda ake ciki, kafin kiftar ido sega mahaifinsa a gidan, wannan ne ya saka Ya Sadeeq ɗin tafiya shima domin ya fara binciken Inane inda aka kai ƙanwar tashi. Se dai duk wata HEADQUARTERS ɗin daya sani dake cikin garin KANO ya gama zagayesu, se dai babu ita babu me ko alamarta. Sosai hakan ya tashi hankalin sa goshin zuhr ya isa gidansu, Daga yanayin yacce mahaifinsa ya ganshi a jigace ne yasan cewar ba ƙalau ba, seda ya fara shan ruwan da Baffan ya bashi ɗan huta kaɗan kana yake tambayarsa ko lafiya?... Kora masa bayanin duk yacce ake ciki yayi, se dai ya ɓoye zancen cikin da yaji ta furta kuwa, tin da bai da tabbacin hakan ne koba haka ba, ALLAH sarki take Baffa shima ya shiga wani kalan zallar tashin hankalin da ba'a sa masa rana. Kafin ka me se gashi har ya haɗa kan almajiransa ya saka su sauƙar Alqur'ani me girma, cikin gidan ya wuce yake gwaggo Sadiya ta dafa shinkafa jallop kamar kwano uku, tana gunguni tana komai ta miƙe ta ɗora don wllh ita ta tsani wannan saka aikin na Baffan, da sai kana zaune kwatsam se ɓallo maka da aiki bayan kana murna ka kammala naka, gashi babu damar musu don duk tsiyarta tana shakkarsa ai, ɗan kwalin dake ƙoƙarin zame mata ta gyara tana cewa. "Se ka bani kuɗin kayan miyar ai dubu uku..." Ganin kuma yana kallonta da kanta yasa ta tsargu don haka tace "To ai kowacce kwana kayan miyar dubu take ci, amma ba sai ka bada kuɗin mai da magi ba muna dasu...." Ta ƙare maganar da susar kan da kana kallarsa kasan bana gaskiya bane, don kar a gano ƙaryar data labta ne. Kansa kawai ya jijjiga ya fiddo ukun harda ƙarin ɗariya biyar yace ganan yacce zefi isa ma, yasa kansa ya fita. Yana fita ta ƙira Bilkisu dake daki ta bata 1500 bayan ta zare dubu biyu, tace a mata malkaɗe bashi ɗaya kulli uku na ɗari biyar biyar gida uku, iya zallar tattasai da da tarugu. Shimar nata ta koma ta ɗauko a cikin ranta tana ma Ummar nata fatan shiriya, don duk maganar da suka yi tana jin su. Fita tayi taga gidan har ga gota Baffan nata da sai da ta masa sannu ya ƙiranta, wanda se da ya saka gabanta faduwar ko tambayar ta baffan nasu zaiyi, duk da dai bawai hakan yake mata ba. Tsugunne takai tana cewa "Baffa gani!" Dubu ɗaya ya zaro daga cikin aljihunsa yace ta taho da ciyawan shayi ta ɗari biyar ta dafa mishi shayi me ɗan dama, bayan ya tambayeta ai suna da sugar tace ehhhh kana yace to ta riƙe ɗari biyar ɗin, godiya ta mishi tana miƙewa ta tafi aikar nata.

Babu jimawa ta dawo ta wuce ta bama Ummun nata markaɗen, kafin itama ta nema tukunyanta me kyau me ɗan girma ta ɗora, koda uwartata ta tambayeta me zata yi, tace Baffa ne ya sakata dafa masa shayi, yi tayi kamar tayi magana amma kuma ta fasa tana ɗaukan wata babban tukunya itama ta ɗora. Kafin kace me sega gidan ya ɗauki ƙamshin girkin gwaggo Sadiyan, ita kuwa tuni dama Bilkisu ta gama dafa shayin ta juye a wata babbar cooler. Ta nemi wankakkun ƙananun kofuna ta ɗora a kai ta ajje daga bakin ɗakin Baffan nasu ta shirya a gurguje ta wuce Islamiyya, ita kuma dama Shareefah tana school dake Monday ce tana can ba kuma zata dawowa ba se Friday, weekend kawai take zuwar musu. Bayan idar da sallar la'asar Baffa ya saka manyan almajirai fitowa da abinci da shayin da aka dafa, nan gardawan ciki suka ringa zuzzuba musu abincin da shayin, bayan sun kammala ci aka kuma taruwa aka yi adda'an ALLAH ya kawo musu komai da sauƙi...

★..
Chapter 20 · 0% Book details