← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 114

Sashe 96

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam ya kama hannun Jabir, suka zauna a tare, ya kalli Jabir ya ce "Haƙiƙa ka tuna mini abun da na kusa mantawa, tabbas damuwar ɗayanmu, ta dukkaninmu ce, duk da ina ta ɓoye abun, ban bari kowa ya sani ba, amma a kowane lokaci na san dole komai zai fito, amma a yanzu ku ɗaga mini ƙafa please ".

Jabir ya jinjina kai ya ce "Shikenan" ya fice ya bar Adam, da ganin s yadda ya fita Adam ya san bai ji daÉ—in abun da yayi masa ba, sai dai shima dole ce babu yadda ya iya.

Sai daf da magariba sannan Bashir suka dawo da rumaisa daga wurin X-ray, yanzu tana iya taka ƙafafuwan ta sannu a hankali.

Sai bayan sallar magariba, sannan Bashir ya yi musu sallama, mama ta yi ta masa godiya da sanya albarka.

Daga nan asibitin bai wuce ko ina ba, sai gidan Adam, ya tarar da shi ya dawo daga masallaci sannan, lokacin an yi sallar isha'i.
Bayan sun gaisa Bashi ya ce "Yauwwa, mun je an yi mata hoton, likita zai ganta gobe in Allah ya kaimu, sannan ya duba idan da yiwuwar a sallameta"

Adam ya É—ago ya kalleshi ya ce "Babu in da za a sallameta sai ta faÉ—i in da matata take, ko na sanya a tsareta"

Bashir ya girgiza kai ya ce "No, Adams, a hankali zamu bi ta, duk da muna cigaba da ɓata lokaci, kuma can katsinan ma, babu wani cikakken bayani, dan haka na yanke shawarar zamu je da police, kai tun da ban san meye a tsakaninku ba, kamar wasu maƙiyan juna kai da ita, za mu je da masu uniform, wataƙila su ta yi musu bayani, yadda ake ciki sai mu san abun yi".

"Zuwa yaushe kenan?"

'Zan yi magana da Hassan, sai muje ko zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe ne".

"Wannan shi ne chance na ƙarshe, idan har ba ta yi magana ba, zan saka ta yi ta ƙarfin tsiya!".

Ayshercool.

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*

*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar special kuma, suna iya zuwa arewabooks su yi searching.*

Bashir ya ce "A'a, ba sai an kai ga amfani da ƙarfin tsiya ba, zata yi magana a hankali, ƙuriciya ke damunta, amma duk da haka kamar akwai wata 'yar tsama tsakaninka da ita, yanayin abubuwan da take yi maka, kamar da gayyya take yi maka".

Adam ya É—an yi guntun tsaki ya ce "Manta da ita kawai, sai gobe in Allah ya kaimu, X-ray É—in na ta babu wata matsala?"

Bashir ya ce "Ai na gaya maka sai gobe in Allah ya kaimu likitan zai duba".

"Allah ya kaimu"

Bashir ya amsa da "Amin".

**
Nusaiba tun da ta ji abun da yake faruwa, ta rasa nutsuwarta, ko abincin kirki ba ta iya ci. Yanzu haka tana tsaka da tunanin da ta saba ta ji Iman ta dafata "Anty Nusaiba" Nusaiba ta É—an zabura sannan ta sauke numfashi ba tare da ta ce komai ba.

"Anty Nusaiba tunanin me ki ke yi haka ne?"

"Bari kawai Iman, tun da Ammi ta gaya mana zancen nan, na kasa nutsuwa ina tausaya mana idan zancen nan ya fita, kin san yadda aka samu a gaba da ma a masarautar nan, ƙiris ake jira wani abu ya faru, to ga wannan babbar magana gaba ɗaya na kasa nutsuwa, idan har ba Anty Aisha aka gano ba, wallahi muna cikin tashin hankali".

"Haka ne, amma babu abun da ya gagari addu'a anty nusaiba, kuma babu ta yadda muka isa mu kaucewa ƙaddara, in sha Allah babu abun da zai faru".

"Iman, na san kina dakewa ne kina ƙoƙarin kwantar mini da hankali, amma kar ki manta abun da aka gaya wa mutane a kan barinta ƙasar nan, kin san yadda aka sako yaya Adam a gaba, yanzu idan maganar nan ta fasu, babu irin sharrin da ba za ayi masa ba ba shi ba har Ammi da mu baki ɗaya. Shiyasa ni tun farko ban so hukuncin da ammi ta yanke ba, tun da komai muƙaddari ne" ta ƙarasa maganar tana kuka.

Iman ta rungumeta ita ma tana zubar da hawaye ta ce "Na sani Anty Nusaiba, amma Ammi uwa ce, duk abun da zata yi, tana yi ne dan bamu kariya da wanzuwar farincikinmu, kuma in sha Allah ƙoƙarin ta ba zai tafi a banza ba, komai zai zo ƙarshe da yardar Allah, ki daina damuwa, komai zsi zo da sauƙi, ai babu abun da ya gagari Allah" suka cigaba da kuka iman na rarrashin Nusaiba.

Baba uwani ce ta shigo tana sallama, tare da zuro kai. Da sauri suka gyara iman ta amsa mata.

Ta dubi iman ta ce "Uwar É—akina lafiya kuwa?".

Iman ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Lafiya lau baba uwani, akwai wani abu ne?"

"Ni fa na kasa gane muku gaba ɗaya, giwa ta daina walwala, mai gida ma haka, kuma gashi na tarar kuna kuka, dan Allah me kuke ɓoyewa ne meyake faruwa haka? Gaba daya gidan babu daɗi, babu wata walwala saboda yanayin nan da ku ke ciki" Ta yi maganar tana neman fashewa da kuka.

Nusaiba ta ce "Baba Uwani babu wani abu kar ki damu".

Cikin damuwa iman ta ce 'Dan Allah kar ki yi kuka baba uwani, komai zai daidaita ba wani abun bane ba, Ammi jikinta ne ya ɗan tashi shiyasa bata walwala, kuma kin san walwalarta ce ta mu, kar ki yi kuka Please" baba Uwani ta matse ƙwalla ta ce "To shikenan, Allah ya bata lafiya, ya sanya komai lafiya, ya jishe mu alkhairi" tana gama maganar ta juya ta fice.

Iman ta ce "Allah sarki baba uwani, tana sonmu da yawa, bana son in ga masu shiga damuwar nan suna ƙara yawa, Allah ya bamu mafita, ina shirin gaya miki wani abu, wannan maganar ta kunno kai".

Nusaiba ta dubeta ta ce "Wane abun?"

"Ki bari wannan matter ta yi settling, zan gaya miki".

"No, kin san ba zan jure ba, ba zan iya jira ba, ki gaya mini yanzu kawai".

Iman ta ja numfashi ta ce "Kin san me uncle J ya ce mini?"

Nusaiba ta girgiza kai ta ce "Sai kin faÉ—a".

"Wai so na yake yi, kuma ko ban amince ba zai bi ta in da ya san za a bashi ni"

Nusaiba ta yi murmushi ta ce "Ni na san a rina ai, take-takensa duk ya gama nunawa, amma ke mai ya sa na ga kamar ba kya son shi ne? Mai uncle J É—in ya yi?"

Iman ta É—an murza zoben hannunta ta yi shiru.

"Do you still loves him?" Nusaiba ta yi maganar tana kallon fuskar Iman.

Iman ta É—an waro ido ta ce "Who?".

"Your recent ex, É—an......"

"Shhhhh" iman ta katseta.

"Kar mu kai ga nan Please, mu bar maganar ma kawai"

Baba uwani kuwa da ke laɓe a ƙofar ɗakin, jin sun sauya hira ya sanya ta tafi tana tsaki "Aikin banza jarababbu, sun ƙi yin maganar gaba ɗaya, zancen da suka yi kuma, idan na kai mata ba so take yi ba, aikin kawai".

***
Adam yana kwance ya ƙura wa roofing ido, sai ya tuna Jabir, abun da yayi masa ɗazu ya tuna, sai ya ji bai kyauta ba, jabir a komai yana tsaye a kan lamuransa, bai kamata ya yi masa haka ba, kuma jabir mutum ne mai kaifin tunani da hangen nesa, sanin ko ya so ko bai so ba zancen zai fit6, ya yanke shawarar ya yi wa jabir zancen, mussaman da suna tare Ruma ta yi masa abun da ta yi masa da farko, tare da saka ran Jabir zai iya samo masa mafita.
Da sauri ya tashi ya fita, ya É—au mota ya tafi gidan Galadima mai ci.

Sai dai tun a hanya yake kiran wayar Jabir ya ƙi ɗagawa, ya je gida ya tarar Jabir baya nan, sarai ya san in da zai same shi, dan haka bai tsaya ko ina ba sai can.

Ko da Jabir ya ga Adam, ƙoƙarin share Adam ɗin ya yi amma ya kasa.

"Wurinka na zo" Adam yayi maganar yana duban idon Jabir.

"Ina jin ka" jabir yayi maganar yana basarwa.

Adam ya sanya hannu ya É—ago Jabir da kwalar rigarsa, ya ja shi suka fita waje.

"Wai meye haka ka ke yi?".

Adam ya tsuke fuska ya ce "Yaya na zo wurinka in ce wurinka na zo, ka shareni ba ka fini mulki da jin kai ba, na san ka sani".

Jabir ya kalli Adam ya ce "Har ka manta few hours ago abun da ka yi mini?".

"Forget about it, just feel like to share it you"

"Ka riƙe sirrinka, tun da bai kamata na sani ba".

Adam ya dafa kafaÉ—ar Jabir ya ce "Kar ka yi mini yawa mana, yakamata ka saurareni".

"Ina jin ka"

Adam ya É—an yi shiru, sannan ya gaya wa Jabir abun da yake faruwa.
Sak jabir yayi, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, wani irin gumi ya shiga tsatsfo masa ya ce "Takawa, wannan fa ba ƙaramar magana ba ce, case ne mai girman gaske, ni gaba ɗaya sarƙaƙiyar nan ta yi yawa, na kasa ganewa gaba ɗaya, an ce Aisha zata tafi ƙaro karatu, kuma tana Saudiyya rainon ciki, ta dawo ba wanda ya sani an yi garkuwa da ita, ta haihu jariri ya kuɓuta ita ba a san in da take ba, wannan zancen kamar film ko almara ni ban gane ba".

Cikin matsananciyar damuwa Adam ya ce "Bar shi a baka gane É—in ba, ka san wacece ta zo da yaron?"

Jabir ya girgiza kai, Adam ya ce "Wannan yarinyar da ta zageni a social media, da na yi niyyar hukuntawa ka hanani".

Jabir ya waro ido kamar su faÉ—o ya ce "Again? Ita a ina ta samu jaririn naka?"
Chapter 96 · 0% Book details