← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 114

Sashe 49

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe ɗaya ta fi son sai ta tafkawa takawa ɓarna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.

***
Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare, ƙamshi duk ya gauraye ɗakin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.

"Mutum kwalliya sai ka ce aljana" dariya ta yi har sai da dimples É—in ta suka lotsa, ta ce "To idan ban kwalliya ba me zan yi?"

Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce "Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai" ɓata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana faɗin "My Chubby girl".

***
Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da yake garin.

Gaba É—aya Instagram sun yi banning account É—in ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram É—in sam.

Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.

Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.

Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.

A ƙofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga? Cikin dakiya ta tunkari ƙofar gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.

Gadan-gadan ta nufi shiga, wani É—an sanda yayi mata tsawa ya ce "Ke wurin wa ki ka zo?"

Ta É—an yi jimm sannan ta ce "Wurin wani"

"Waye wanin?".

"Sunanshi Adamu"

Wado ido suka yi gaba É—aya suna kallon ruma "Ke! Baki da hankali?" Saroro ta yi tana tunanin me ta yi kuma?

"Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki faÉ—i wannan sunan haka? Zaki bar wurin nan ko sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki"

"Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga"

"Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga".

"To a wurin wa zan nemi iznin?"

ÆŠaya daga cikin su ya ce "Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar 'ya da baki fil-fil kamar robot"

Ta kalleshi ta ce "Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina" tayi maganar idonta ƙyar a cikin nasa.

Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya jiƙawa yarinyar nan jikinta.

Ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana kallon hanya. Suka kunna sigari suna sha, ruma ta kallesu ta taɓe baki a hankali ta ce "An yi asara"

"Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?"

"Ni dai ba a kanku nake ba, ku ƙyaleni mana" ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu naɗi.

Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara'arsu suka fara mata magana "Baba Sabuwa, kin dawo?"

"Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?"

Suka amsa mata da Alhamdilillah.

Ruma ce ta taso da sauri tana faÉ—in "Baba" baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce "Yarinya ya aka yi?"

"Dan Allah gidan nan zaki shiga?"

Ta ce "Eh, a gidan nake aiki"

"Kin san wani Adamu a cikin gidan?" Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da fatan Allah ya sa wani bai ji ba.

"Ke 'ya ta ai ba a faÉ—ar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san shi"

Ruma ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata"

Baba uwani ta ce "To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?"

"Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi "

Baba sabuwa ta ce "to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda".

"Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku"

"Zo mu baki sigari " É—ayan ya faÉ—a cikin iya shege.

"Sai dai uwar sigari" ta faÉ—a a hankali.

Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.

Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a ɓangaren Mummy, kuma tana ɗaya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan.
Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar É—akinta takardar su fara dubawa ko kuwa? Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a É—an tofinta, ta cigaba da ayyukanta.

Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da faɗa, dan babu wanda ya san ta fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin saƙonta zai je in da take so, sai Addu'a take Allah ya sa baba Sabuwa ta bayar da saƙonta. Aliyu ya tasa ta a gaba zuwa gida, suna tafe yana ƙare mata zagi.

Wajen ƙarfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa gidan ba sai yanzu.
A gate jami'an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.

Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya ce "Kira mini Baba sabuwa" ta miƙe tana tunanin me yasa yake neman Baba sabuwa a yammacin nan?.

Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya miƙa mata hannu ya ce "Bani saƙona" babu musu ta fito da takarda ta miƙa masa. Ya juya ya fice.

Fauziyya ta ce "Sabuwa, takardar mecece?"

"Wallahi wata yarinya ce ta tsareni a ƙofa, ta ce a bashi ban san yarinyar ba ma"

"To meye a ciki?"

"Ai kin san ba iya karatu na yi ba"

"Kuma da baki iya karatun ba, mai ya hana ki kawo mini, tashi dalla usless" Sabuwa ta tashi cike da haushin tsawar da Fauziyya ta yi mata, duk da ba yau ta fara ba.

Bai tsaya duba takardar ba, ya jefata a cikin jakarsa ya tafi wurin Ammi.

Gaba daya ya manta da takarda, sai washegari da daddare yana neman wasu takardu, takardar ta faÉ—o.
Ya buɗe takardar wasu 'yan ƙananan rubutu ne, marasa kan gado a cikin takardar, bai yi zaton rubutun zai karantu ba sai da ya fara karantawa, duk an gwamutsa Capital da small latter's.

*Da farko dai zan fara da yi maka Allah ya isa, dan da alama baka da ƙanne mata shi ya sa ka yi mini abin da ka yi mini. Kamar yadda ka saka aka nemo ni, nima sai da na gano gidanku. Ka saka aka ɗauko ni, ka zageni kuma ka ci mini zarafi, to wallahi ban yafe maka ba taɓa mini nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka shaƙoni hannunka yana taɓa wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya taɓa shi ciki yake yi, to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na faɗa an saci kuɗin talakawa an je karatu ƙasar waje. Mu zuba mu gani daga maƙiyiyarka  RUMAISA MAHMUD ƘANƘARA ƊORAYI TUNGA ƘANWAR MAZA Kazo ka kasheni*

Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ƙirjinta ranar da aka kai masa ita.

Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta da ƙuruciya.

"Zan ƙure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen" ya maimaita wasiƙar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ƙular da shi irin wai ya taɓa mata nono, duk da bai riƙe cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.

Mama ta haɗawa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ƙarshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta taɓa nisa da ita na kwanaki ba, ga kuma rashin ji irin na ruman.

Uniform ɗin ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya ɗoɗar Abdallah ne ya goge mata su, sai ƙamshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye.
Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta, ƙazantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta buɗe idonta, dan ta ga wani mara mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?

A hankali ya sauke glass É—in motar, suka yi ido huÉ—u da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma kasa magana gaba É—aya.

Buɗe motar ya yi ya fito yana ƙare mata kallo.
Chapter 49 · 0% Book details