← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 114

Sashe 57

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka kalli ruma suna son jin dalilin tsayar da su É—in.

"Mangwaro zan tsinka".

A ɗan razane Zaliha ta ce "A'a ruma, a garin nan fa bakomai ake taɓawa ba, baki ga gonaki duk an yi girbi ba, amma ba a ɗauka ba,masu garin ake jira su zo su yanke harajin da za a biya sannan a ɗebi amfanin gona, yanzu idan suka zo wucewa suka ganki, zaki saka mu a matsala.

"Suwaye masu garin?" Ta yi maganar cikin ko in kula.

Lawisa ta ce "Ke dai ki bari kawai ruma, ki bari idan muka je gida sai a saka a samo miki"

Ruma ta cire mayafinta, ta ɗorawa lawisa a kafaɗarta, ta nufi bishiyar nan, suna ƙwala mata kira, amma ba ta tsaya ba, ta kama bishiya ta haye kamar buranya, hawan katanga da bishiya ba abu ne mai wahala a wurin ruma ba.

Ta naɗe doguwar rigarta, ta tara mangwaron sannan ta saukko, su kuma suna ƙasa suna jiranta cikin tsoro suna cewa ta sauko.

Bayan ta sauko ta karɓi mayafinta ta zuba a ciki, ta saɓo abunta tayi gaba ta ƙyalesu.
Bin ruma suka yi da kallo, ta ci uwar ubansu a rashin ji, haka suka rufa mata baya suna kallonta.

Suna cikin tafiya suka ga ta saki hanya ta shiga wata gona, tarin masarar da aka jingine ta je ta fara É—auka.

"Innalillahi, dan Allah ruma kar ki janyo mana masifa, dan Allah ki fito mu tafi, duk wanda aka gani a gona bayan girbi ba a biya haraji ba kashe shi za ayi".

"Kisa kuma sai ka ce cinnaka, guda biyar kawai zan ɗauka gasawa  zan yi na ci"

Zaliha ta ce "Dan Allah ki fito kar su ganki".

"Wai suwaye ne? In sun ganni ba ruwanku ni kaÉ—ai na É—auka" ta zuba masarar a mayafinta ta fito. Kamar suna tsoron ruma suka sake rufa mata baya suna zazzare ido.

Sun yi tafiya mai nisa sun kusa gida, suka ji ana musu magana "Ke daga ina ku ke?" Gaba É—aya suka tsaya suka waiwaya, wani dogon mutum ne a tsaye, sanye da rawani hannunsa saye a cikin tsummar rigarsa, ya ma dai fi kama da mahaukaci.

Ruma ta ƙare masa kallo za ta yi gaba abinta.

"Ke ina magana zaki tafi?" Ya daka mata tsawa.

Cikin tsiwa da rainin hankali ruma ta ce "Haba babana ke fa ka ce mana, kuma na ga dai ba aikenmu ka yi..."

Da sauri zaliha ta riƙe hannun ruma ta ce wa mutumin "Dan Allah ka yi haƙuri, baƙuwa ce ne a garin".

"Baƙuwa amma mara tarbiyya ko? Ba ta san nan ina ne ba? Kuma ba ta iya ladabin yin magana da manya ba, Meye wannan ta riƙo?"

Ruma ta ja da baya ta ce "Nifa ban gane ba, me na yi maka zaka ce mini mara tarbiyya? Mangwaro ne da masara" tayi maganar tana buÉ—e masa mayafin.

"Waye ya baki izinin É—aukar masarar?"

Ruma da haushi ya fara kamata ta dake ta ce "Yi haƙuri ban san gonarka bace, idan yayana ya zo ɗaukata daga birni zai baka kuɗin masararka, ni na tafi sai kun taho" ta ɗau kayanta tayi gaba.

Su kuwa jiki na rawa suka tsaya suna sauraren mutumin.

"Lallai dagaci, wato har da kawo baƙi marasa ɗa'a ba tare da ya nemi izini ba, har su zo su karya mana doka, to zai gane kuskurensa da mu yake zancen, ku wuce ku tafi".

Da gudu suka tafi gida domin sanar da abin da yake faruwa.

Suka tarar da iya na tuhumar ruma ina ta samo wannan kayan, amma tayi shiru ta ƙi magana.
Su zaliha ne suka kwashe komai suka gaya wa iya.

"Mun shiga uku ruma, ai mu garin nan ba a mana haka, a zaune muke ƙarƙashin umarnin 'yan bindiga, suke da garin, ki daina haka ba ruwanki da kowa, duk wanda ki ka gani a garin nan girmamashi to ba ruwansu da ke, amma idan ki ka yi musu rashin kunya sai su yi miki illa".

"To ku mayar da ni gidanmu mana, ni ba wanda ya isa yayi mini wani abu, dan ni ƙanwar maza ce zane mutum yayyena za su yi. Kawai sai ya ce mini mara tarbiyya shi tarbiyyar ce ta saka yake yi wa mutane magana a haka, ni a kano kowa ya san ina girmama mutane raini ne ban so, ni na zata ma mahaukaci ne".

Iya ta kwantar da murya ta ce "To na ji, amma dai dan Allah ki kula, bari Alhaji ya shigo zai je ya basu haƙuri, 'yan bindiga ne sai su illataki, muma bin umarninsu ne ya sanya muke zaune lafiya"

Ruma ta É—an yi shiru sannan ta ce "Wai iya su waye 'yan bindigar nan?"

"'yan tayar da ƙayar baya ne, Allah ne kawai ya san meye aƙidarsu"

Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Meye ƙayar baya kuma, sai ka ce wasu kifaye?"

"Ba zaki gane ba ko na yi miki bayani, amma dai bisa umarnin su muke zaune, sai abin da suka ce muke yi"

"To suma shugabanni ne zaɓarsu ake yi, na ji kin ce ba kwa komai sai da izininsu, ko 'yan sanda ne su?"

"Babu É—aya ruma, kawai dai ku yi ta mana addu'a, muna zaune ne dan kawai mun san ko mun bar nan ba in da zamu je, bamu da wurin zuwa"

Ƙwaƙwalwa ruma ta shiga wani tunanin na daban, ba ta kuma cewa komai ba, ta shiga wata sabgar.

Tana missing É—in gida sosai, ga wayarta ta mutu ba caji tama barota cikin kaya a gidan gwaggo.

Kullum da safe cikin bata rubutu da banka mata hayaƙi ake a gidan, wai maganin tsarin jiki na baki maita da aljanu.
Ruma kuwa ta ce ita ba zata sha wani rubutu ba, warin tawadar nan amai zai sakata. A kwanaki biyu kacal ruma ta fara buwayarsu, saboda sai ƙoƙari take sai ta aikata wani abu da zata tsokano mutanen nan.

Yau da yamma kasuwar ƙauyen take ci, dan haka suka shirya su uku zasu tafi kasuwa, iya tayi ta jawa ruma kunne a kan rashin ji da kuma yi wa mutane tsiwa, sannan ta basu kuɗi suka fita suka tafi.

Kasuwar ƙauye ce dai, amma ta burge ruma sosai da sosai, ga kayan gargajiya nan kala-kala.
Sai dai abin da ya bata mamaki, yadda ta kan ga wasu mutane masu rufaffiyar fuska suna kaiwa suna komowa, hannayensu saye a cikin rigunan su.

Shagon wani mai awo suka shiga suka zauna, za su sai wake, da alama su lawisa sun san shi, sai hira suke. Suna cikin hirar wani mutum yayi sallama suka amsa masa, ya shigo ya zauna, bai ce musu komai ba, suma kuma ba wanda ya tanka masa.

Ruma ta ce "Ni fa hausar nan taku dariya take bani".

Mai awo ya ce "to  hausar mu tafi daɗi ai, na ji kamar hausar kanawa ki ke yi ko?"

"Eh mana, ni 'yar kano ce, hausarmu mai daÉ—i, garinmu ma yafi naku kyau sosai da sosai"

Mai awon ya ce "Ai mu ma dan nan ƙauye ne, amma garinmu yana da daɗi da kyau".

Ruma ta yi dariya ta ce "Ba wani nan, garin naku da baku da iko da komai, wai sai an baku umarni mutum da kayansa, kano kuwa ba haka bane, abu idan naka ne naka ne kawai. Kuma ku ba damar baƙo ya zo sai a din ga tuhuma waye wannan, kano kuwa ba a haka?. Haka wani zanƙalelen mutum kamar mahaukaci ya tsayar da mu yana tambaya wai wacece ni?"

Zaliha ta ɗan daki cinyar ruma tana ƙifta mata ido, amma ruma taƙi shiru.

"Wai me awo suwaye masu yawon nan da rufaffiyar fuska kamar munafukai" a tare suka kalli ruma, sannan suka kalli mutumin nan na zaune.

"Ya naga kuna kallona kamar an ritsa mara gaskiya? Bawan Allah ko kai ka san su?" Ta yi maganar tana kallon mutumin

Ya girgiza kai ya ce "A'a, amma ina ga ko sune masu garin da ake faÉ—a".

"Wai sune 'yan ta'addan?"

Ya rausayar da kai ya ce "Wataƙila"

Ruma ta ce "Amma kuwa ba su kyauta ba, ba su yi wa kansu adalci ba, su dinga ƙwacewa mutane kaya, nima fa da zamu zo garin nan a kan bindigogi na zo, ina 'yan ta'addan ne a mota ɗaya muka hau da su"

Ya É—an waro ido ya ce "Haba dai, baki ji tsoro ba?"

Kamar ya kunna ruma, ta gyatta zama ta ce "Ni ban ji tsoro ba, a cikinsu fa wani har kaza ya sai mini, yayi kalar masu kirki, amma ban san meyasa suke kashe mutane ba, kullum a rediyon mama sai an ce sun kashe mutane, abun tausayi, ku yi ta Addu'a kuna musu nasiha, ko zasu daina".

Mutumin yayi murmushi ya ce "To shikenan, kuma kanawa ku tayamu da Addu'a, amma na yi mamaki da ki ka ce a kan bindigogi ki ka zo, kuma ba ki ji tsoro ba"

Ruma ta yi wani irin murmushi ta ce "Baka sanni bane ba, yayyena maza bakwai" ta yi maganar tana nuna masa da yatsunta.

Sannan ta ɗora da cewa "Ni ba komai ne yake bani tsoro ba, na ce musu dan Allah su buɗe mini in gani ko da gaske suke bindiga ce, kai ka ga yawan bindigar? Allah ya kyauta kawai" ta miƙe tsaye ta ce "Bari na je na sayo gyaɗa" tayi waje.

Lawisa ta yi ƙasa da murya ta ce "Zaliha tashi mu gudu kar yarinyar nan ta ja a harbemu a tsakiyar kasuwar nan".

"Ya ya za ayi mu gudu mu barta?".

Mai awo ya ce "Ranka ya daɗe ayi mata haƙuri baƙuwace kuma yarinya ce, ayi haƙuri dan Allah" mutumin bai ce komai ba ya cigaba da danna wata waya mai madannai.

Gaban mai gyaɗa marau ruma ta duƙa, tana saya wani mutum ya wuce tare da bigeta da wani abu, kuma ko waiwayowa bai yi ba yayi gaba abunsa.

Da gudu ta tashi ta bishi "Malam ka bugeni, ba ka ji ba na ce ka bugeni fa"

Ya waiwayo yana kallon ruma.

"Ba ka ji ka buga mini wani abu a bayana, kuma ba ka bani haƙuri ba"

Ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Ni ne zan baki haƙurin?"
Chapter 57 · 0% Book details