← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 114

Sashe 80

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye ne suka ziraro a fuskar rumaisa, wato nan ma wata tawagar ce ta daban, atishawa jaririn hannunta yayi, hakan ya janyo hankalinsu in da take.

"Kai anya ba wani naman jejin ne a wurin ba, ku duba mana".

Rumaisa kuwa tuni ta bar wurin, tana addu'a, amma yadda suka dalle wurin da fitila a ya tsorata ta, dan tuni ta saka ran an gansu, sai dai ta samu cikin ganyayyaki ta zauna tana mayar da numfashi.

"Ni yanzu ya zan yi, ya Allah ko ban kuɓuta ba ka kuɓutar mini da jairirin nan na karɓi amanar sa, Allah kar ka sa rayuwarsa ta salwanta" ta yi addu'ar a hankali.

Da ta É—an ji dama-dama sai ta tashi ta cigaba da tafiya a hankali, tana shashafawa tana duba hanya, saboda babu haske kuma tana haÉ—awa da addu'a.

Jin gajiya tayi mata yawa, ga zazzaɓi ya kamata sosai da sosai, ya sanya ta nemi wuri ta zauna, ta haƙura da cigaba da tafiyar, ta tattaɓa ƙirjin yaron zuwa hancinsa, ta ji yana numfashi, amma a galabaice, ga jikinsa zafi sosai.
A haka ta takure da shi a jikinta. Ba ta sake sanin meyafaru ba, sai farkawa ta yi ta ga rana ta ɗaga sosai a kanta, ta duba jikinta duk fatarta tayi wani irin baƙi da kore-kore, ga ƙafarta tayi tsami, saboda ciwukan da ta ji, da hanzari take sake lalube jaririn nan, amma babu abun da ya same shi, sai galabaita. Ta sake kwantar da shi a gefenta, ta lulluɓe shi, tayi taimama ta yi sallar asuba da ta tsere mata.

Har ta nemi wuri ta zauna, saboda gajiya da rashin ƙwarin jiki, amma zuciyarta ta tunatar da ita idan ta cigaba da zama, yaron nan yana iya rasa ransa, dan haka ta tashi da ƙyar, tana tattara yawun bakinta ta haɗiye, saboda azabar ƙishirwa amma bakin nata a bushe yake, ta cigaba da bin hanya tare da fatan Allah ya fitar da su.

***
Tun da garin Allah ya waye mama a rikice take, kaiwa kawai take tana komowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa abun da yake yi mata daÉ—i.

"Mama, dan Allah ki nutsu ki kwantar da hankalinki, kin san fa jininki ya hau".

Ta girgiza kai ta ce "Ƙyaleni Abdallah, zuciyata ce take ta bugawa, ko dai an kashe rumaisa, ko kuma tana cikin mawuyacin hali, na kasa samun nutsuwar zuciya".

"A'a mama, kar ki yi wannan fatan, ko sakawa kanki wannan tunanin, sharrin zuciya me kawai, amma in sha Allah tana nan a cikin ƙoshin lafiya" Huzaifa ya yi maganar cikin damuwa.

"Ba zaku gane me nake ji ba, ku ƙyaleni kawai".

Aliyu kuwa tafe yake a hanya, ya je shago ya sayo abu, sama-sama ya ji ana kiransa, sai ya ji kamar muryar rumaisa, nan da nan ya tsaya, ya waiwaya sai ya ga Habiba ce, tafe da kayan miya a hannunta, kan ta cim masa ta faɗi saboda sauri, ya ƙaraso wurinta da sauri yana "Faɗin sannu, kk bi a hankali kar ki ji ciwo" ba ta damu ba ta miƙe tsaye ta ce "Yaya Aliyu gidanku dama zan je, mafarki na yi rumaisa ta dawo, shi ne na ce Allah ya sa gaske ne, na taho in ganta".

Shiru Aliyu yayi yana kallonta, yama rasa mai ze ce mata, a ransa ya ce 'Haka mama ta yi irin wannan mafarkin, Allah ya sanya ya zama gaskiya'
A zahiri kuwa ya ce "Ki na ji na ko Habiba?"

Idonta ne ya tara hawaye ta ce "Dan Allah kar ka ce mini ba ta dawo ba".

"Ki yi haƙuri kin ji, amma rumaisa ba ta dawo ba, muna ta addu'a dai".

Kawai ta durƙusa a wurin, ta haɗa kai da gwiwa ta saka kuka.

A É—an rikice ya ce "Tashi kar mutane su ce wani abun na yi miki".

Ya riƙe hannunta ya ɗagata, sai kuka take yi.

Sai yanzu ya ƙara tabattar da soyayya da shaƙuwa da ke tsakanin rumaisa da Habiba, bayan duk saɓanin da suka din ga samu, amma taƙi nutsuwa saboda rashin rumaisa.

Ya kai mintuna ashirin yana rarrashinta, ba tare da ya ƙosa ba, saboda ƙaunar da ta nunawa rumaisa, ya sa yake jin kamar rumaisan ce take kuka.

***
Takawa kuwa ya shirya cikin wani farin yadi, yana ƙoƙarin saka hula, message ya shiga wayarsa.

*Adam ka É—an yi mini uzuri, abu ya kamani zan je katsina, sai in Allah ya kaimu gobe zan shigo kano*

Wani takaici ne ya kama takawa, a ganinsa bashir ya gama raina masa hankali, cikin hasala ya kira wayar Bashir amma ya ji ta a kashe, ko uwar me zai je yi a Katsina oho.

Wata irin ƙwafa yayi, ya kwashi mukullin motarsa da wayoyinsa ya fita, yana jin zafin abun da Bashir yayi masa.

***
Rumaisa kuwa ita kanta ta san ta galabaita, dan ta fara fidda rai da rayuwa. Tsakankanin wasu ciyayi ta kutsa, kawai ta ganta a wani fili, ta tsaya cak tana kallon wurin, idonta ya sauka a kan wani mutum a tsaye ya gama fitsari gefe ga bindigarsa.
Yana waiwayowa suka yi ido huÉ—u da rumaisa "Ke wacece, me ki ke yi a nan?" Ja da baya ta fara yi, ya É—auki bindigarsa ya nufeta. Ai ba ta san lokacin da wani kuzari ya zo mata ba, ta juya da gudu ta bar wurin, aikuwa ya bita, É—an uwansa da yake cikin ciyayi, shi ma ya fito ya rufa musu baya.

Sosai take gudu tsakanin rayuwa da mutuwa, ta yi wa jariririn nan kyakykyawan riƙo, tana jin yadda numfashinta ke barazanar rabuwa da huhunta, ƙarfinta ya fara ƙarewa, amma ɗan ragowar hope ɗin da take da shi na samun damar yin rayuwa ko jaririn nan ya rayu, ya sanya ta cigaba da bawa kanta ƙwarin gwiwa, ba ta iya gane meye a gabanta, saboda azabar wahala dishi-dishi take gani, babu zato babu tsammani ta yi karo da wani nannauyan abu, mai ƙarfin gaske, ƙatuwar bishiyar kuka ce, da rumaisa ba ta ankara da ita ba, suka yi karo, a take ta silale ƙasa ƙeyarta ta bugu, jini ya fara zuba, jaririn ya faɗi a gefe ɗaya.

Ayshercool
08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

A harabar gida takawa yana shirin fita, suka kiciɓis da Jabir, jabir ya dube shi ya ce "Ina zaka ne haka? Na ga yau Saturday babu aiki?".
Chapter 80 · 0% Book details