← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 114

Sashe 82

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta rumaisan sai ka kai zuciyarka nesa zaka iya taɓata, saboda yanayin da take ciki na ƙazanta da dauɗa, ba yadda ba su yi ba su kwance ɗan kwalin ƙugunta, amma aka kasa, ƙarshe suka ƙyaleta suka fara kokawar ceto rayuwarta, ita kanta sai da aka saka mata oxygen, saboda sama-sama take numfashi, aka ɗebi jininta aka tafi yi mata gwaje-gwaje.

***
Kusan mintuna uku tana zaune a dining tana ta juya cokali a cikin kofin shayin, amma ta kasa ɗagawa ta sha ko da sau ɗaya, sai zancen zuci take. Jin an dafa ta ne ya sanya ta ɗago a hankali ta kalli ammi, a take ta fara ƙaƙaro murmushin da bai wuce iya leɓenta ba.
Ammi ta ja kujerar kusa da ta iman, ta zauna ta ce "Autana, ko ban tambayeki ba na san abun da ki ke ji, kuma na san ke mai juriya ce, dan haka kar ki saka maganganun da wambai yayi a ranki, ki manta da komai, ki mayar da hankali a kan karatunki, da kin kamma sakandare, zan turaki Mexico wurin laila, ki nutsu ki yi karatunki a wurinta, kuma in sha Allah zan sama miki miji na gari, mai tsoron Allah wanda zai riƙe mini ke tsakani da Allah"

Iman ta rungume Ammi ta ce "Ni dai a'a ammi, zan zauna a tare da ke, bana son mu rabu, zan cigaba jure komai in rayu a kusa da ke".

Ammi ta yi murmushi ta ce "Duk abun mutum dai dole sai aure ya rabamu, watarana sai mutum ya tafi gidan miji"

Iman ta ce "Sai mu tafi tare, duk wanda zai aureni, sai ya yi wa ammina nata É—akin".

Yana sanye da farar jallabiya, ya ɗora rigar saƙi ta sarauta, da farar hula, yana tsaye yana kallonsu, ya ɗan yi gyaran murya, hakan ya sa suka ɗago suna kallonsa.

Ammi ta ce "Ina zuwa haka?"

Ya gyara agogon hannunsa ya ce "Zan je gidan turaki ne in gaishe shi".

"Amma ina fatan ba wani abun zaka je ka gaya masa ba, ka tayar masa da hankali?"

Takawa ya girgiza kai alamar a'a, iman ta ce "Yaya a dawo lafiya".

"Allah ya sa, ki kula ki sha magungunan ki a kan lokaci".

Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah" daga haka ya fice daga falon.

"Ammina, bari na je na sha magani na É—an kwanta".

Ammi ta ce "To babu laifi, amma dan Allah kar a je a zauna ana tunani, idan na gani ba zan ji daÉ—i ba".

Iman ta yi murmushi ta ce "Ba zan yi ba in sha Allah, in dai kina nan Ammi wane tunani zan yi?" Tayi maganar tana miƙewa tsaye tana yi wa Ammi murmushi.

Ko da ta je É—akinta, ta tarar da baba uwani tana ta yi mata bincike bincike.

"Baba uwani" ta kira sunanta a razane ta waiwayo ta kalli iman ta ce "A'a uwar É—akina kin shigo?"

Iman ta ce "Eh, amma me ki ke nema ne?".

"A'a babu abun da nake nema, baki gani ba, gyara É—akin nake yi, ke da ba lafiya ba, kaye-kaye nake yi miki ai".

"Amma baba uwani na sha gaya miki, gyaran É—aki ba aikinki bane ba, ya zaki din ga wahalar da kanki da yawa haka, kiyi wancan aiki kuma ki zo ki yi wannan".

"To imanuwa idan ban yi miki ba wa zan yi wa, kuma gashi ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba, na san sai ki ce zaki yi da kanki ma".

Iman ta girgiza kai ta ce "Kar ki damu baba uwani, ki yi tafiyarki kawai, za a gyara É—akin ma ai babu datti, ina son in É—an kwanta ne".

"To Shikenan babu laifi, ki huta lafiya"

Iman ta bi bayanta da kallo, daga bisani kuma ta je ta nemi wuri ta kwanta.

***
Cikin ƙosawa take wayar, cikin yanayi mai kama da faɗa-faɗa "gaskiya Khalifa na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba, ai yakamata ace zuwa yanzu result ya fito".

"Ke duk result É—in da ki ka gani bai yi miki ba, wanne ki ke jira? Meyasa kin fiye wutar ciki ne?"

Samha ta ce "Au haka ma zaka ce, ni na kasa gane wannan yawon da hankali, ni fa na fara jin tsoro".

Dariya Khalifa ya yi ya ce "Haba jaruma, wane irin tsoro kuma? Ai mun yi kaso mafi yawa na aikin, sauran ke zaki yi wa kanki fighting, ki bi komai a hankali, idan ki ka yi gaggawa aiki zai iya kwaɓe miki, dan ni babu ruwana. Nan ba da daɗewa ba, zaki ji labari mai ɗan karen daɗi".

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya sa". Ta ajiye wayar ta yi shiru tana tunanin maganganunsa.

"Anty Samha, Anty Samha!"

Waiwayowa Samha ta yi ta kalli yarinyar a É—an hasale ta ce "Lafiya ki ke yi mini wannan kiran haka?"

"Anty Samha kin gan mu, zuwa muka yi baki yi murna ba?".

"Na ji, jeki wasanki, idan na fito ma gaisa"

Yarinyar ta ɗan ɓata fuska ta ce "Shikenan, naga uncle takawa ya zo, bari na je na gishe shi".

Da sauri Samha ta ce "Jannah, bana son shirme da gaske ki ke yi ko kuwa?".

"Wallahi da gaske, ga motarsa can da hadimansa, yana wurin Baba suna gaisawa"

"Shikenan, na ji jeki maza" janna na fita samha ta tashi ta canza kaya, ta hau feshe-feshen turare.

Takawa yana jin daÉ—in mu'amala da turaki, dattijon akwai nutsuwa da kuma dattaku, ba shi da hayaniya sam balle faÉ—a.
Sun daɗe suna hira, sai da takawa ya fara shirin tafiya sannan turaki ya ce "Amm..wato akwai maganganu da muka ji suna ta yawo a kanka, a cikin masarautar nan, sai dai bamu yanke maka hukunci ba. Maganganu ne marasa daɗi da maimaita su ma bashi da wata fa'ida, amma duk da haka zamu jadadda, a din ga kula a ƙara kiyaye martabar addini da kuma al'ada, ba zamu so zancen nan ya je kunnen mai martaba ba, mussaman yadda ake ji da kai, yake sonka, muna ta ƙoƙarin daƙile jita-jitar, mun sani shaye-shaye ba halinka bane ba, dan da kana yi, zamu gane, amma a cigaba da kiyayewa tare da riƙe addu'a".

Adam yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya ɗan risuna ya ce "Za'a kiyaye in Allah ya yarda, Allah ya ƙara maka lafiya, zamu wuce".

"To madalla, Allah ya tsare ka isar da gaisuwata ga mahaifiyarka, ka ce kwana biyu bamu ga aiken mutan daji ba ma'abota nagge" yayi maganar a nutse cikin sigar barkwanci.

Takawa ya ɗan murmusa, tare da duƙawa daga nan ya tashi ya fita.

A falo ya tarar ana ta shirya abinci, Janna ta ƙaraso gabansa ta risuna ta ce "Barka da wannan lokaci uncle".

"Barkanki dai janna, kwana biyu bana ganinki, ya makaranta?"

"Lafiya ƙalau"

Ya ce "Masha Allah". Yana ɗaga kai ya yi tozali da matar da ya tsana a duniya, mahaifiyar su Jamil, wato mama, bai san ya aka yi suka san ya zo ba, dan ta ƙofar baya ya shiga sashen turaki, ya nemi ayi masa iso.

Ta washe baki ta ce "Takawarka lafiya toron giwa, gaba salamun baya salamun, galadima magajin galadima, da haka za a wuce ban san an zo ba? Ai yakamata mu gaisa ko".

"Ai ban zaci idonki biyu ba, barka da wannan lokaci" yayi maganar yana ɗan risunar da kansa ƙasa.

Kan ta amsa samha ta fito tana murmushi "Takawa, yau kai ne a gidan namu? Zaka tafi babu ko sallama da mun yi faÉ—a da kai kuwa" wasu irin matsatsun kaya ne a jikinta riga da skirt, ilahirin surar jikinta ko ina a matse.

"Ku yi mini afuwa, dama ina da niyyar shigowa".

Mama ta ce 'Amma na ga kamar kana shirin tafiya, da ka yi É—an waken zagayen, ga abinci nan na saka a kawo maka ai".

"Ayi mini afuwa sauri nake ne, ana jirana, zan sake yin zuwa na musamman na barku lafiya" bai ma tsaya ba balle ya ji mai za su sake cewa ba ya fice.

***
Ɗan ƙura mata ido yayi, bacci take kamar babu rai a jikinta, yanzu babban fatansa ya san daga in da take a nemo 'yan uwanta, su zo su san abun yi a wanke mata wannan dattin na jikinta, ko ita ma ta samu ta ji daɗin jikin nata.

A hankali ta buÉ—e idonta, ta É—an motsa jikinta da yake ta yi mata azabar ciwo.

Ya ce "Alhamdilillah, kin farka?"

Ta yi masa ƙuri da ido tana kallonsa.

Ya durƙusa a gaban gadon ya ce "Ki bani lambar wayar wani a gidanku, a sanar musu kin dawo".

A hankali ta buÉ—e baki ta ce "Haka muka yi da kai?"

Ya ce "Me fa?".

"Ina É—ana?" Ta tambaye shi.

"Yana sashin jarirai ana kulawa da shi, kin san ya galabaita".

Rumaisa ta ce "Lallai baka sanni ba, ni fa a kan yaron nan, sai na tayarwa da kowa hankali, a bani É—ana"
Zai yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ciro wayar daga aljihunsa, ya kalli screen É—in wayar ya ce "Jarababbe, na san na shiga uku da masifarka yau".

Ya É—aga wayar ya saka a kunnensa ya ce "Ya?".

"Abun da ya kamata ka ce mini kenan?".

Bashir ya ƙara nutsuwa ya ce "Sorry man, na san na yi maka laifi, am sorry for that, wani emmrgency case ne ya faru, na bayar da taimakon da zan iya, yanzu haka ina Asibiti wata yarinya na tsinto a katsina ta kuɓuta daga hannun 'yan bindiga".

"Ina ruwana, ta ina hakan ya shafe ni? Ni abun da ka yi mini ka kyauta kenan? Na rantse da Allah muka haÉ—u sai ka gane baka da wayo".

Ruma ta yi ƙuri da ido tana sauraren muryar da ko daga maye ta farfaɗo, ba ta manta mai ita ba.

Ayshercool
08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
Chapter 82 · 0% Book details