Sashe 41
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nusaiba ta zauna sosai ta É—ora da cewa "And yakamata ki daina nuna ki na jin tsoron su, musamman yaya Mahmud kamar mara tunani, abin da aka gaya masa kawai da shi yake amfani, ai gara ma yayi ya koma in da yake karatu mu huta masifaffen banza"
Iman ta toshe baki ta ce "Sai na gaya masa abin da ki ka ce, babu ruwana" tayi maganar tana dariya.
Ajiyar zuciya Nusaiba tayi tana murmushi, ganin yadda murmushi ya bayyana a kyakkyawar fuskar Iman.
***
"Ohh ni rumaisa sai girma nake, mama, ta bakin naki kwanci tashi asarar mai rai, na shiga jss2 fa"
"Aikuwa dai, kina ta girma amma babu nutsuwa ba"
"Kai mama, Allah ya nuna mini lokacin da zaki yabeni, ke kullum bana abin arziki a wurinki mamancy"
Mama ta girgiza kai ta ce "Ai ke gaba É—aya abin tsiyarki ya ninka na arzikin yawa"
"Mama"
"Ina jinki"
"To É—an kalleni mana"
Mama ba ta kalli ruma ba ta ce "Sai kuma kiyi ai"
"Dan Allah ki sai mini shayi da indomie, kin san bana son tuwon nan "
"Rumaisa ai ni ce ma Indomien, zo ki gutsiri in da ki ke so ki ci, tuwo kuma ban yi miki dole ba, ki barni da kayana"
"Allah ya jiƙan matar da ta ƙirƙiro tuwo idan musulma ce, amma ta cuceni zuciyata tafi raya mini a zamanin tsunburbura ta zo"
Ruma ta ƙaraci soki burutsunta, da gwasalewa mama tuwo, mama taƙi kulata.
Hankalin ruma ne ya tsaya a kan rediyon da mama take ji, wata mata tura wasiƙa, tana son a bata maganin da zata sha, tun da tayi yaye ƙirjinta ya zube kullum mijinta cikin yi mata gori yake.
"Kan uba, amma wallahi maza basu da kai, dan Allah meye haÉ—insa da kallonta?" Mama ta ja rediyon ta kashe.
"Mama ya zaki kashe, ki bari mu ji mana, nifa bana son harkar watsewa, wallahi ka gaya mini maganar banza sai na tafi gidanmu, wannan ai rashin tarbiyya ne, ya ya zai din ga yi mata kallon ƙurilla, kuma mama ba kin ce mini ɓoyewa ake yi ba? Ita ma har da ita"
Mama dai ta basar, tayi mata shiru, can ta kuma cewa "Hmm kin san Allah mama, nima na gani fa, 'yan ajinmu na islamiyya suka ce, wai idan mace tana tafiya ba ta saka hannu a hijjabinta, maza kallonta suke yi, haka ma idan ta juya bayanta, jiya da na je gidan Asabe ban samo gawayi ba na je titi, daga nan na tsaya sayen mai, kin san riga da skirt na saka, sai mayafin abayat, wani mutum ya tsurawa gurin zamana ido, ai ban sani ba, ina waiwayawa muka haÉ—a ido, na ce malam kalli gabanka mana, baki ganshi ba babba da shi na saka hannu na kare abina har na zo gida".
Abdallah ya ce "Sannu jikar faisal, duk 'yan matan da suke kaiwa suna komowa a wurin, ba wadda ya kalla sai ke ƙwaila, wani ɗan abu kamar falanki, saboda asara ke zai tsaya kallo"
"Wallahi ni ba ƙwaila bace ba, kuma ka je ka tambayi kowa na wurin ka ji, kallona yake yi, ni kuwa na saka hannu na rufe"
Mama ta ce "Ya isa haka, kuma saboda tsabar rashin sanin ciwon kai ki tafi har titi da ɗan ƙaramin mayafin da bai fi ayi kallabi da shi ba, duk ranar da Allah ya nuna mini, sai na zane ki. Kuma zan saka bababana ya je islamiyyar lallai a raba muku aji da wannan yaron, dan sun fi ƙarfin tunanin ki"
Da sauri ruma ta ce "Ki yiwa Allah da ma'aikinsa, kar ki aika mai sunan Baba, kin san yanzu ƙiris yake jira yayi mini aure".
"Aikuwa ina daf da gaya masan, idan har baki nutsu ba, kin daina wannan rashin kan gadon ba, gara ya aurar da ke na huta"
Ruma ta saka hannu ta kama laɓɓanta ta ce "Na daina da yardar Allah"
***
"Takawa, wai yaushe zaka je ka É—auko yarinyar nan ne?"
Ya É—an lumshe idonsa ya buÉ—e sannan ya ce "Zan É—aukota ne, gara ta É—an huta ta nutsu tukuna, visarta har yanzu da saura"
Ammi ta ce "To shikenan, yauwwa ya maganar tafiyar da na ji Jabir ya ce zaka yi? Meye gaskiyar maganar?"
"Ammi ki manta da shi kawai, É—an rainin hankali ne a wurin aiki ne za a tura mu wani bincike".
Ammi ta numfasa sannan ta ce "To, Allah ya yi jagora, amma dai duk da haka kamar yadda ya ce ka din ga kula takawa, ka san currently a ƙadamin da kake, kar ka janyo mana wata wahalar wadda muke ciki ba ta ƙare ba, dan Allah ka dinga komai a sannu, sannan ka riƙe addu'a kamar yadda nake jaddada maka"
"In sha Allah Ammi, kar ki damu ina iya ƙoƙarina wurin yin Addu'a".
"Haka ake so, Allah ya yi maka jagora"
"Amin Ammi".
Daga haka ya É—auko wayarsa yana duddubawa, yana tsaka da duba wayar, Ammi ta kuma cewa "Ko yaushe Mahmud zai koma makaranta, na ga kamar lokacin komawarsa yayi, kuma ance mini haryanzu ana ganin gilmawarsa a gidan nan"
Takawa ya sauke wayar, ya dubi Ammi ya ce "Ammi, ba babarsa tana kallo bai koma É—in ba ta zira masa ido, dan Allah ki daina damuwa da abin da ya shafe su, ki din ga É—agawa kan ki hankali".
Ammi ta girgiza kai ta ce "Da kai da su ni duk abu É—aya ne a wurina, ba zan so rayuwar wani daga cikinku ta samu tangarÉ—a ba".
"To Ammi tun da ba sa yi da ke, ai mu mun isheki rayuwa, dan Allah ki manta da su"
Ajiyar zuciya Ammi ta yi, ba ta sake cewa komai ba.
***
Yau kamar korarriya haka ruma ta shigo gida, sai cika take tana batsewa, ba ta kula kowa ba ta cire uniform ta yi wanka, ta zubo abincin ta ta fara ci.
Kamar wadda aka tsikara ta ce "Yaya Aliyu, wai ina ce makarantar 'ya'yan gwamna ne?"
Yayi murmushi ya ce "Mai yafaru?"
"A'a tambaya kawai nake yi"
"A manyan makarantu suke, wasu a turai ma"
"Suna zama a ƙasa, ajinsu babu abin zama?"
Yayi dariya ya ce "Amma kin ci kai, 'ya'yan gwamna ne zasu zauna a ƙasa? Zama a ƙasa a makaranta wannan ai sai ɗan talaka"
"To meye banbancin mu da su? Dukkanin mu ba mutane bane, kuma muma ba 'ya'ya bane?"
"Kuna da bambanci mai tazarar gaske, dukkaninku mutane ne, kuma 'ya'ya ne, amma iyayensu ke riƙe da madafun iko, abin da zaku yi ku taimaki kanku a matsayin yaran talakawa shi ne, kuyi karatu komai wahala, idan ba haka ba kuwa ku ƙare a bayinsu da 'ya'yansu"
Tamkar ruma zata fashe da kuka ta ce "To wallahi zan yi Allah ya isa, aka ce duk 'yan ƙasa ɗaya muke, bencinmu ya karye, dama wasu a ƙasa suke zama, kullum sai kayana sun yi datti, uniform ɗina duk sun fara koɗewa. Ga malaman namu ma sai a hankali, wallahi malamin English ɗin mu bai iya turanci ba kame-kame yake yi, malamin math ɗin mu kuma Arabic yayi ba uwar da muke ganewa, ga ajinmu azababben zafi window ɗaya ce, bana gane komai a makarantar kamar na daina karatun. Kuma jiya nake ji a radion mama uban kuɗin da ake saiwa wasu manyan motoci sai ka ce motar aljanna, ko meye sunansu oho na manta, to wallahi duk wanda aka raba da haƙƙina ya cinye ban yafe ba, zama a ƙasan da nake a matsayina na 'yar ƙasa"
Mama ta ce "Ruma wa ki ke yi wa Allah ya isa, ban hanaki wannan É—abi'ar ba ruma?"
"Mama ba zaki gane halin da muke ciki ba, ga rashin abin zama, ga zafi ga rashin malamai ga duka kamar an samu jakai, har noma ake sakamu fatanya a makaranta, gaba É—aya makarantar mu 'ya'yan talakawa ne, shikenan mu ba mutane bane".
Ruma kenan, gaba ɗaya tunaninta da maganganunta sun shallake shekarunta, wataƙila hakan yana da alaƙa da yawan jin radion da mama take yi, da yawan tattauna matsalolin da ƙasa ke ciki da yayyenta suke yi.
Babu wanda ya kuma tanka mata, tayi bambaminta ta gama, dan ta wani fannin tabbas Ruma tana da gaskiya, amma babu yadda za ayi a gaya mata tana da tazarar da waÉ—anda take hange take kamanta kanta da su ta gane.
Haka ta ƙare cin abincin tana mita, kuma bil haƙƙi har cikin ranta, take faɗar yadda abin yake yi mata ciwo.
Kasancewar yau Alhamis babu makarantar islamiyya, Huzaifa da Yasir duk suna gida.
Huzaifa ya nutsu yana ta kallon tiktok a wayarsa, ruma ta lallaɓa ta zira kanta tana kallo.
Huzaifa ya É—auke wayarsa ya kalli ruma ya ce "sai ka ce mayya, mara zuciya kawai"
"Eh na ji, ni kunna dai mu gani"
"Ba zan kunna ba, ke ki ke saya mini data?"
"A'a, amma É—an kunna gani kawai zan" ya haÉ—e rai ya ce "Ba zan kunna ba, bar nan wurin ko na dakeki"
Ta tashi tana zumɓura baki ta ce "Mutum dai idan tsiya tana bin sa, ko ka raɓeshi haushin ka yake ji?"
"Ni ne tsiya take bi ko? Wallahi ki ka bari na zo kanki, saina kwaÉ—a miki mari"
Cikin tsiwa da rashin kunya ta ce "To kar ka barni da rai ma mana, idan da rai nima zan yi wayar nan" Jin yadda take ɗaga murya ya san idan ya biye mata, faɗa za su yi, ran mama ya zo yana ɓaci, kawai ya shareta ya cigaba da danna wayarsa.
A hankali ta lallaɓa ta koma wurin Yasir, shi kuma Yasir Instagram yake kallo, dan haka sai ka ce dole ta ɗan maƙale tana leƙawa dan kar shi ma ya koreta.
Ya É—aga kai ya kalleta ya ce "Dawo ta nan ki kalla, madam no heart"
"Ai in dai zaka barni na kalla, to babu damuwa kafi wancan tsiyar muka rako duniya". Yasir ya yi murmushi bai ce komai ba.
Sai dai tamkar zata shige cikin wayar, ko ta ƙwace masa wayar.
Duk hoton ko videon da ta gani sai ta tsaya ta yi liking. Ƙarshe sai sakar mata wayar ya yi, ya tashi ya bata wuri.