Sashe 16
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta ce "Ahh, ruma ai ba ke kaɗai ki ka san ta kan tsiya ba, na sai miki kaya ba godiya ki ka raina, na biya kuɗi ayi miki lalle ki ka ƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kina wannan shegen baccin na yi miki dungulmi da shi zaki yi sallar, tsohuwa ta faɗa kwata ba, irin wanda nake yi, kuma kitso ma gidan Hanne zan saka Huzaifa ya kai ki, tayi miki zane huɗu ba dai ba kya ji ba, ai daidai nake da ke, ina sane nake kawar miki da kai".
Ruma ta kalli yadda aka ƙunshe mata ƙafa har ƙwauri, ga hannayenta kuma ana batun ayi mata zanen Hausa guda huɗu a ka tayi salla, ta tuna uwar rigar da zata saka a matsayin kayan ssllarta, ta ɗora hannu a ka ta zunduma ihu.
DAN ALLAH MASU NEMA DAGA FARKO KU DINGA TAMBAYA A GROUP KO DUBA WATPAD KO AREWABOOKS NA GODE
AYSHERCOOL
08081012143
[03/07, 2:14 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
        Â
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following É—ina a arewabooks a kan account É—ina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode
*Ina miƙa saƙon godiya, ga waɗanda suka yi mana ta'aziyya na rashin uba da 'yar uwa Naima Suleiman (Nimcyluv) ta yi, muna fatan Ubangiji Allah ya jiƙansa da rahama.*
*TAƘABBALALLAHU MINNA WA MINKUM, INA TAYA AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA BABBAR SALLA, UBANGIJI ALLAH YA KARÆI IBADUNMU YA MAIMAITA MANA*
P8
Da rige-rige Usman da Abdallah suka shigo É—akin, suna tambayar meyafaru da ruma take wannan uban ihun.
Kallonta Usman ya yi, ya kalli mama ya ce "Mama meya sameta ne?"
Mama ta ce "Ku tambayeta mana, ba gata nan a zaune ba"
Abdallah ya ce "Ke menene?"
Nuna masa hannunta ta yi, tana sake fashewa da wani uban kukan.
"Wannan ledar ta meye haka a hannunki, kamar wata miskiniya"
Æare baki tayi, ta cigaba da kuka iya Æ™arfinta.
"Dalla ki rufewa mutane baki, kiyi mana bayanin menene?" Usman ya daka mata tsawa.
"Ba mama ce ba"
"Me maman tayi?"
"Ta yi mini lallen tsofaffi wai tsohuwa ta faÉ—a kwata ina bacci, wallahi dariya za ayi mini idan aka ganni da shi".
"Kuma saboda baki da mutunci, ki ke mana wannan uban ihun da Asubar nan, ke dai ba zaki yi hankali ba ko?"
"Wallahi mama ba ta sona, ban san meyasa ta tsaneni ba, wayyo Allah na"
Abdallah ya ce "Allah ya ƙara, a wannan shegen baccin naki, har aka yi miki lallen baki sani ba".
Mama ta ce "Ki tashi ki kwance lallen nan kiyi salla".
Ko motsi ruma ba ta yi ba balle ta tashi.
Abdallah ya ce "Wai wane irin lalle ne tsohuwa ta faÉ—a kwatar ne?"
Cikin kuka ruma ta ce "Irin fa wanda mama take yi a ƙafarta"
Dariya ce ta ƙwacewa Abdallah, ya ce "Haba mama, ya zaki yi mana haka?"
Mama ta ce "Hukunta ta nayi, duk rashin jin da take yi ba ta zaci ina da hanyar hukunta ta ba, na bada kuɗi ayi mata abin arziki na zamani, amma taƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kuma ajima da kaina zan kai ki kitso zane huɗu za ayi miki".
Sosai ruma take kuka, Usman kuwa ficewa yayi ya cigaba da sabgarsa, Abdallah ne ya kaita bakin rariya, ya tayata ya cire ta wanke, aikuwa hannunnan yayi jawur, lalle ya kwanta ɗoɗar hannunta da ƙafarta.
Da gari yayi haske kuwa, Huzaifa ya ga lallen rumaisa, ya zauna ya sakata a gaba ya dinga yi mata dariya, har da kifawa, wai hannunta kamar kuturwa.
Ko Abincin safe ruma ba ta ci ba, sai kuka da goge hawaye, wajen ƙarfe goma na safe, mama ta sakata a gaba zuwa gidan kitso.
Kamar yadda mama ta faɗa, kitson hannu biyu aka yiwa ruma, gashi ta sha azaba a wurin mai kitson, saboda da ta ƙi tsayawa, mama na dukanta, matar kuma ta matse mata kai a tsakanin cinyoyinta, ga kitson azabar zafi tamkar za a zaro ƙwaƙwalwarta saboda yadda matar ke jan gashin.
Ko da aka gama kitson, ruma ta haÉ—a gumi ga hawaye da majina saboda azabar zafi, mama ta sakata a gaba suka tafi gida.
Ruma da ta kalli hannunta ranta yake ɓaci, saboda hannun ganinsa take kamar ba nata ba.
Har ana gobe salla ruma bata farin ciki, ji take ina ma ace an fasa sallar idi wannan shekarar, saboda wannan yankan ƙauna da mama tayi mata.
Har bata son a aiketa, dan idan ta fita ta ga yara sun sha kitso da ƙunshi, sai ta yi kuka, saboda yadda ta ƙarfi ita aka mayar da ita zamanin mutanen da.
Yanzu haka tana tafe a hanya, zuwa aiken da mama tayi mata, ta gaji da tafiya ga ɓacin rai, ta samu wuri tayi zamanta a kan wata baranda, tana share hawaye.
"'Kukan me ki ke yi ne haka, ba aiken ki aka yi ba?"
Ta É—aga kai taga mai maganar, Auwal ne, na makarantar islamiyya da ta yiwa bori rannan.
Shiru tayi masa tana tura baki.
"Meyasa ki ke kuka?"
Miƙewa ta yi tsaye tana faɗin 'Babu komai"
Ya É—an girgiza kai ya ce "Ina Yasir?"
Cikin ƙunƙuni ta ce masa bata sani ba, tayi wucewarta.
Mamaki ne ya kama shi, duk in da ta ganshi ko ba zai kulata ba, sai ta yi masa magana, amma yau tayi masa wulaƙanci.
Aiken da bai fi tayi shi a mintuna ashirin ba, sai da ta shafe awa biyu da rabi, ta koma gida Aliyu sai da ya murÉ—e mata kunne, saboda yadda ta je ta daÉ—e.
Da safiyar salla kuwa, an kai ruwa rana da hajiya ruma kafin tayi wanka, dan cewa ta yi ba zata je idi ba.
Huzaifa kuwa musamman ya ƙi shiri da wuri, sai ya ga shigar da ruma zata yi yayi mata dariya.
Ta na kuka, mama ta watso mata wannan atamfa da ta zauna ta dinga kushewa.
"Mama dan girman Allah ki barni na saka tsofaffin kayana, wallahi bana son kayan nan".
"Ni ki ke gayawa ba kya son kayan nan, zaki saka ki wuce ko kuwa?"
Za ta tsaya gardama Aliyu ya yi mata tsawa, ya ce ta É—au kayan ta saka su wuce sallar idi.
Ga lalle dungulmi, ga kaya ɗinkin mutanen farko, ga kai babu kitso mai kyau, ba yari ba sarƙa koma kamar 'yar ƙauye.
Huzaifa kamar ya shiÉ—e don dariya.
"Yarinya kin yi kyau kamar bafulatanar ƙauye" Yasir ya yi maganar yana dariya.
"Babu ruwanka da ni Yasir, zan maka rashin mutunci wallahi".
"Na kuma jin bakin ki sai na ɓarara da ke, maza wuce mu tafi" Aliyu yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.
Usman ne ya miƙo mata sabon hijjabi ya ce "Gashi nan ba dan hakinki ba".
Ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai hijjabin zai taimaka mata ta rufe wannan buhun É—inkin, tun da hijjabin dogo ne.
Karɓa tayi tana yi masa godiya, ta saka suka tafi idi.
********
"Masha Allah, looking take away my beautiful angel" Ammi ta faÉ—a tana kallon Iman.
Murmushi iman tayi ta ce "Ammina, an yi salla lafiya"
"Alhamdilillah my dear, ina fatan dai an yi mini Addu'a"
Murmushi ta yi ta ce "Ba dole ba Ammina"
Wata matashiyar budurwa da ke zaune a kan kujera, ta É—ago ta ce "Wai mu Ammi baki ganmu bane?"
"Na ganku mana"
"Ai shikenan Ammi, wannan wariyar launin fata tayi yawa, mu shikenan ba za ki dinga kallanmu ba, sai wannan mai kama da bafulatanar dajin" cewar É—aya yarinyar.
Ammi ta ce "Kun dai ji kunya, da ku ke kishi da ƙanwarku"
Iman tayi musu gwalo ta ce "Iya wuya dai, nice ta gaban goshin Ammina"
'Ta mayar da ke ciki, ko a saka ki a zanin goyo a baki Nono, ƙarshen ƙauna"
Ammi ta girgiza kai ta ce"Allah ya shirye ku, Iman ki je ki shirya direba zai kai ki gidan zinariyar Galadima, ki kai musu Abincin salla".
Æata fuska Iman tayi ta ce "Ammi"
Kan ta ƙarasa maganar, Ammi ta ɗora yatsanta a kan lips ɗin ta ta ce "Shhhh, bana son musu, tana ta complain ba kya zuwa" Ɗan gyaɗa kai Iman tayi ta ce "Shikenan Ammi, bari na shirya"
*****
"Ke ba zaki ta so ki fara kai tuwon nan ba"
Ruma ta kwaɓe fuska ta ce "Dan Allah mama ki yi haƙuri, ki bawa su huzaifa su kai wallahi idan na fita dariya za ayi mini"
"Ni nake aiken ki, ki ke cewa na aiki wani ruma, ni ko ruma?"
"A'a mama ba haka bane ba, wallahi dariya yara suke yi mini" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta".
"Tashi ki wuce ki je aiken da aka yi miki" Usman ya daka mata tsawa.
Jiki na rawa ta tashi, ta É—au kwanukan da mama ta zuba tuwo, ta fara kai wa.
A hanya ta haÉ—u da wasu 'yan makarantar bokon su, cikin fara'a É—ayar ta ce "Laa ruma, ya ki ke ina kayan sallar ki?"
Ruma ta kalleta ta ce "Ji masifa, to ba ni da su, ba a É—inka mini ba"
"Daga tambaya sai masifa?"
"Eh, ina ruwanki da ina kayan salla na, tsirara ki ka ganni?" tayi maganar tana saye hannun ta a cikin hijjabi.
"Kutmelesi, ruma meye wannan a ƙafarki?" Gaba ɗaya suka kalli ƙafar ruma, da take sanye da silifas ɗan madina, ga ƙafa tayi maroon da lalle, kasancewar ruma ba iya ɗaurin zani ta yi ba, zanin ya ɗage har ƙwaurinta, kuma hijjabin bai gama rufe ƙafar ba.
"Kutmelesi, wane irin lalle aka yi miki, lallai mai lallen nan ta cuceki, kut kamar ƙafar tsohuwa"