Sashe 91
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Baba uwani ta tashi tana murnar yadda ta sanya farantawa uwar ɗakinta ta ɓoye.
Unguwar su ruma ta É—auka cewar ta dawo, magana har islamiyyar su, gaba É—aya unguwa ta É—auka, aka din ga yi musu addu'a da tayasu murna.
Huzaifa ne yayi hankalin cewa a kira katsina a waya a sanar musu da anga rumaisa, dan gaba É—aya ma sun manta da batun su.
Sai da mai sunan Baba ya kai mama ta ga nata likitan, sannan suka tafi Asibitin da rumaisa take.
Gaba ɗaya rumaisa ta kasa daina kuka, saboda farincikin ganin 'yan uwanta gaba ɗaya a tare da ita, da ta motsa a tambayeta me take buƙata.
'yan uwa da abokan arziki kuwa da maƙwabta tuni suka fara sintiri a asibitin, domin duba ruma, kowa yazo da ɗan abun alkhairinsa da zai bawa rumaisa.
'yan uwansu na kano kuwa suma tuni suka cika asibitin, wannan su zo wannan su tafi, sai ga hauwwaliya ma sun zo da sandarta ta dogarawa, kasancewar tun karayar da ta yi kan a sace rumaisa ba ta warke ba. Suka rungume juna.
Ruma ta ce "Hauwwaliya gurguwa ki ka zama ne? Na ganki da sanduna"
Hauwwaliya ta ce "Ke ba gurguwa na zama ba, kin manta na karye ne?"
Ruma ta ce "Au haka ne fa, ban zo na ganki ba ma fa aka saceni".
"Allah sarki rumaisa, kin ga idi, zaman hannun 'yan bindiga an ce wahala ake sha fa"
Ruma ta yamutsa fuska ta ce"daina tuna mini dan Allah, wuya ko da magani babu daÉ—i"
Likita ne yayi sallama shi da nurse, mama ta yi musu sannu da zuwa, mai asibitin ne da kansa ya kalli ruma ya ce "Sai ka ce mun kwantar da shugaban ƙasa, 'yan dubiya daga wannan sai wancan, kamar ba wani mara lafiya sai ke" ruma tayi murmushi tana kallon trolleyn da suka shigo da ita, tana fatan ba za ayi mata allura ba.
Yayi murmushi ya ce "To yaya jikin naki?"
"Da sauƙi, amma haƙarƙarina fa yana mini ciwo haryanzu"
Ya ce "Mu ga wurin, ya aka yi haƙarƙarin yake yi miki ciwo?"
"Sule ne ya takani a wurin, wani jibgege, nauyin ƙafarsa kamar tsauni". Yayi murmushi yana ƙoƙarin miƙa hannunsa ya ɗaga rigarta ya duba, amma ta riƙe rigar ta tsareshi da ido.
"Dubawa zan yi na gani"
Aliyu ne ya taso, ya kama rigar tata zai É—aga "Yaya Aliyu ni kar ka buÉ—e mini jiki a ganni"
Aliyu ya ce "Ke dallacan, ina tsintoki a ka yi kanki ko É—an kwali babu, wa zaki yi wa iyayi? Ko shi wanda ya taka kin kin yi masa iyayin?"
Tana zumɓura baki ya ɗaga rigar, likitan ya danna haƙarƙarin, ta saki wani marayan kuka.
Ya ce "Is ok, zan rubuta muku hoto in sha Allah, ayi mini hoton wurin, da kuma kanki".
"Wurin mai hoto za a kai ni? Ayi mini a waya mana, bana son motsawa ko ina ns jikina ciwo yake"
Ya girgiza mata kai ya ce "X-ray nake nufi, ba hoton passion ba, sauko yau ki taka ƙafar nan na gani" ta girgiza masa kai ta ce "Tana yi mini ciwo fa"
"Sai fa kin taka yau saukko, da yayi ki ka yi gudu ki ka fito daga daji?".
Shiru ta yi sannan ta ce "Ikon Allah ne ya fito da ni" ta fara ƙoƙarin saukowa a hankali ta tsaya a kan ƙafarta. Likitan ya ce "Good, taka a hankali mu gani". Tana ƙoƙarin ɗaga ƙafar, amma ji take kamar ba a jikinta take ba, dan haka ta kasa.
Likitan ya ce "Riƙe hannuna, ki ɗaga ƙafar a hankali, bana son ganinki a kwance kullum"
Noƙe kafaɗa tayi, ita ba zata riƙe hannunsa ba.
Ya saka hannu ya riƙo na ta hannun, ya ɗan ja ta sai da ta ɗaga ƙafar sai da ta yi ƙara saboda ciwon da ƙafar take yi.
Usman ne ya taso, ya cire hannun ruma da ga na likitan ya ce "Zamu zagaya da ita in sha Allah, in dai ƙafar ce zata din ga takata" murmushi yayi ya girgiza kai, ƙiri-ƙiri ba sa iya ɓoye kishinsu a kan ƙanwarsu, zai duba mata rauni, Aliyu ya taso ya buɗe masa da kansa, yanzu kuma Usman ya zare hannun ruma daga nasa.
Ya rubuta musu duk abun da yake so a kawo masa, ya fita daga É—akin.
Hauwwaliya ta dogaro sandarta, Usman kuma yana riƙe da rumaisa suka fita zagaya asibiti.
A hankali rumaisa tana takawa, har suka je ɗakin da jaririnta ke kwance, nurses na kula da shi, sune suke yi masa komai. Ruma ta daɗe a wurinsa, sanann suka fito, a wurin komawa ɗakimta kuma ƙafa taƙi takuwa, ƙarshe sai Goyata Usman yayi ya mayar da ita ɗaki.
Ammi ba ta fito ba sai la'asar, shi ma da ta fito tea kawai ta saka a kai mata, shi kawai ta iya sha, kai da ka ganta ka san a tashin hankali take.
Wayar Adam take ta kira amma ba ta shiga.
Ta fito falo ta tambayi barorinta ko Adam ya shigo? Suka ce mata tun safe da ta raka shi ya fita, bai kuma dawowa ba.
Ammi ba ta samu wayar Adam ba sai magariba.
"Ina ka ajiye wayarka nake ta kira amma ba ta shiga?".
"Ammi na kashe wayar ne, saboda bana son a dameni da kiran waya".
"Wannan ba hujja bace, ka san dole zan neme ka ai, ya ake ciki akwai wani abu ne, ko yarinyar ta yi magana a kan Aisha?"
Kamar yana gaban Ammi, ya girgiza kai ya ce 'Ta ƙi magana, ta ce bata san komai ba".
Cikin rashin fahimta Ammi ta ce "Kamar yaya?"
"Haka dai ta ce"
Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ka zo ka sameni, asibitin zamu tafi yanzu ".
Ya sauke numfashi ya ce "To gani nan" ya ajiye wayar yana jin yadda kan sa ke sara masa, saboda damuwa da tunani.
Sai kusan ƙarfe tara na dare sannan Takawa ya zo tafiya da ammi, sai a lokacin su Iman suka samu damar ganin ammi.
Cikin damuwa Iman ta ce "Ammi ina zaki?, yau gaba É—aya bamu ganki ba"
Cikin ƙarfin hali Ammi ta ce "Ku yi haƙuri, wata unguwa zamu je, yanzun nan zamu dawo ba daɗewa zamu yi ba" daga haka ta yi gaba ta bi bayan takawa suka fice.
Iman ta ce "Yaya Nusaiba, akwai matsala fa, Ammi suna ɓoye mana wani abu ba sa son mu sani".
Nusaiba ta ce "Nima na gani, amma bari mu jira mu gani".
Ita iman abubuwan sun yi mata yawa, ga maganganun wambai, ga zancen da yake yawo a kan su da takawa, ga abun da take gudu Jabir ya furta wai yana son ta.
Kamar kurame haka su Ammi suka ƙarasa Asibitin da rumaisa take.
'Yan dubiya duk sun watse, sai Mama da Abdallah mai sunan baba suna ta shirin tafiya gida, Mama ta wanke jaririn nan tas, an haɗa madara an bashi, ya gama sha ruma tana rungume da shi, tana kallonsa tana tuna irin yadda suka sha gwagwarmaya kan su kuɓuta.
A hanyar barin asibitin, mai sunan Baba suka haÉ—u da Adam da Ammi, É—an kallon kallo suka yi da shi da takawa, amma babu wanda ya kula wani, suka wuce.
Sallamar su Ammi ce ta dawo da rumaisa daga tunanin da take yi, ta É—aga kai ta kallesu ba tare da ta amsa sallamar ba, Abdallah da mama suka amsa suna yi musu barka da zuwa.
Ruma ta ɗan ƙare musu kallo, fuskar takawa kamar ta mai amai da gudawa, duk yayi wani iri, mama ta basu wurin zama, suka gaggaisa ammi ta dubi ruma ta ce "Maman baby ba magana?"
"Ina wuni" Ammi ta ce "Lafiya lau, ya jiki ya baby kuma?"
"Lafiya lau".
Ammi ta ce "To Alhamdilillah"
Mama ta ce "Jiki da sauƙi kam, domin yau har ta tattaka, gobe in Allah ya kaimu zamu je mu kaita hoton ƙafar da kai, da kuma haƙarƙari da take kuka da shi".
Ammi ta ce "Allah sarki, karki damu, zan aiko s kaita".
Mama ta ce "A'a kar É—awainiyar ta yi yawa, zamu kaita in sha Allah"
Ammi ta ce "ÆŠawainiya ta wuce tserato wa da ta yi da wannan jaririn, ai duk abun da muka yi mata bamu faÉ—i ba".
Mama ta ce "Rumaisa kawo jaririn su ganshi mana".
"Amma mama kar ki bashi É—ana"
Mama ta ce "Shi wa?"
"Wancan mutumin" tayi maganar ba tare da ta kalli Adam ba.
Guntun tsaki mama ta yi, ta karɓi jaririn, ta miƙawa Ammi shi, Ammi ta karɓe shi tana murmushi tana ƙare wa yaron kallo, kamannin adam ne sak yaron ya kwaso.
Ta dubi ruma ta ce "To maman baby, ba a saka masa suna ba haryanzu?".
Ruma ta ce "Na saka masa suna, sunansa Mahmud!" A tare Ammi da Adam, suka É—ago suka kalli rumaisa, ita kuwa ta basar dan ba ta san me ta yi ba.
Paid book ne ₦500, via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool.
08081012243
https://chat.whatsapp.com/G9XU8tDJMjq02zlZMHurZ5*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*