Sashe 9
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yasir ya ce "Wallahi mama hakan ma ta gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ai kin yi ƙoƙari, ke Ruma wannan rigar idan ki ka sakata ai ba sai kin ɗaura zanin ba, kaɗan ya rage ta zama doguwar riga, idan kuwa zaki ɗaura zanin sai ki ɗaura shi a kam rigar, ki yi ɗaurin barmana coge wallahi kyau zaki yi"
Gaba daya ta fuskanci Yasir rashin mutunci kawai yake yi mata, kamar zata fashe haka ta tattare kayan ta kai É—aki ta zubewa Mama a kan kujera, ta barwa ranta cewa gara tayi zamanta a gida da salla, da ta saka wannan zulumbuwar rigar a matsayin kayanta na salla ta fita ayi mata dariya.
Mama ta fita yin barka a maƙwabta, hakan ya bawa Yasir damar zama ya sanya Ruma a gaba ya dinga tuntsira mata dariya, duk wanda ya shigo sai ya ɗauko masa kayan ya nuna masa, daga atamfar har ɗinkin irin na zamanin su Mama ne.
Huzaifa ya fi kowa ƙyaƙyatawa, ya ce "Lallai mama ta iya punishment, ai ni ta biyani da aka miki wannan ɗinki, kamar yadda Yasir ya faɗa, idan ki ka saka kayan nan, ki ka kafa ɗauri irin na barmana mu samo ƙorrai, da sallar nan mu baza kiɗan ƙwarya a cikin unguwa, wallahi kuɗi zamu samu, dan dama mutane duk sun watsar da al'ada".
Abdallah har da yi mata magiya a kan ta gwada kayan yanzu, ya ga yadda za su yi mata. Tayi musu banza ta koma gefe ta ci magani.
Yaya Usman ne ya zare mata ido, wai sai ta gwada kayan sun ga yadda za suyi mata, kasancewar tana shakkarsa shima, haka ta je ta saka kayan ta fito tana danne kukan da yake ƙoƙarin ƙwace mata.
Tana fitowa tsakar gidan Huazaifa ya bushe da dariya ya ce "Waya ga babba da jaka".
Abdallah ya ce "Allah ya bar mana Delun mu, wallahi dama delun aka saka miki, kin yi kyau".
Usman Ya ce "Abdallah, yi mata É—aurin barmana cogen, mu gani, zan mata video"
Duk yadda ta so haÉ—iye kukan sai ta kasa, sun kewayeta sai dariya suke kamar sun ga mahaukaciya, ga Usman yana yi mata video da wayarsa suna dariya.
Huzaifa sai kifawa yake, kamar wanda ya zare, yana cewa Usman"Ka yi mata hoton da Black and white mu ce ga kakar su Mama 1940"
Babu tsammani Umar ya shigo, ya tarar da Rumaisa a tsaye kamar an dasa ta, ga uban É—auri a ka, ta É—aura zani a kan riga, tana tsaye tana kuka su kuma sun kewayeta suna dariya.
"Meye haka?" Yayi maganar a kausashe.
Usman ya ce "kayan sallarata ne, aka kawo take ta rashin mutunci wai bata son kayan, shine nake punishing É—inta, nan gaba ta koyi godiya ga Allah a kan duk abin da ya bata, sannan ta godewa wanda ya batan".
Shi kansa Yaya Umar ji yayi kamar ya yi dariya, saboda yadda Ruman tayi a kayan, kai da gani ka san sun yi mata yawa, sai tayi kamar wadda ta kawo tallan kalwa birni.
Gimtse dariyarsa yayi ya wuce É—akinsu, suka gama yi mata rashin mutunci sannan suka sallameta.
Da ta koma ɗakin ma, sai da ta sha uban kukanta, ta cire kayan ta ajiye tana jin yadda ranta yayi mugun ɓaci a kan abinda suka yi mata.
Kasancewar yau ba tuwo mama tayi da daddare ba, ya sanya ruma zaman cin abincin dare ba tare da mita ko ƙunƙuni ba, ga kuma uwa uba a ƙule take da rashin mutuncin da su Yaya Abdallah suka yi mata. Tana ta lissafa yadda zata rama abin da suka yi matan ta huce.
Duk da yadda yau tayi shiru, babu wanda ya kula da shirun nata, dama mama na jin haushin tayi mata abu ta kushe, mama ta mayar da hankalinta kan 'yan mazanta suna ta hira.
"Mama ina da tambaya" duk suka waiwayo suka kalleta.
mama ta ce "To ina jinki, Allah ya sa na sani"
"Wallahi na san ƙarshenta banzayen tambayoyinta ne marasa kan gado, dan Allah mama kar ki saurareta" Huzaifa yayi maganar yana kallon Ruma.
Cikin tsiwa ta ce "Ban kasa da kai ba, dan haka babu ruwanka da ni".
Mama ta ce "Yi tambayarki ina jin ki"
"Yauwa, dan Allah kar na tambayeki kuma kice mini sai an kwana biyu, menene Janaba, kuma meye fyaÉ—e!!!"
Ayshercool
08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel É—ina domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
[20/06, 6:52 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
        Â
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following É—ina a arewabooks a kan account É—ina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.
P5
Sak suka yi gaba ɗayansu, lomar da Yaya umar ya haɗiya ya ji taƙi wucewa tana kai komo a wuyansa kamar zata dawo. Amma ya basar kamar bai san me suke faɗa ba.
Huzaifa kuwa tsam ya miƙe yana faɗin "Ai sai da na ce kar ki saurareta ki ka ƙi, sai ku san abin da zaku gaya mata" yana maganar ya bar tsakar gidan.
Mama ta rasa mai zata cewa Ruma da hankalinta zai É—auka, sam yarinyar bata tunani dai-dai da shekarunta.
"Wai ya na ji kin yi shiru? Me kuma nayi?" Ta yi maganar cikin taɓara.
Cikin ƙarfin hali mama ta ce "Ke a ina ki ka ji wannan kalmomin da ki ka tambayeni?"
"Mama ya kuma ki ke tambayata bayan nima tambayarki nayi"
"Ki amsa mini dan ubanki" mama tayi maganar a hasale.
Ta É—an cuna baki sannan ta ce "Ba wani ne ya gaya mini ba, kece ki ke jin radiyo ranar, na ji ana cewa ayi wankan janaba idan aka yi ko me? Oho na manta shi ne nake son na san meye janaban, kuma meye wankan. Shi kuma fayÉ—e idan aka faÉ—a a radiyo sai na ga hankalinki ya tashi kina girgiza kai kina Allah ya tsare zuriyar musulmi baki É—aya, shine nake son na san menene?"
"Tirƙashi, aiki ga mai ƙareka mama Allah ya bamu alkhairi " Yaya Aliyu ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa ɗaki.
Yaya Usman ya ce "Kuma duk abin da ake faɗa a radion babu wanda ki ka riƙe sai wannan?"
Ruma ta ce "To ai akwai wasu ma, mantawa nake yi ne sai yanzu na tuna"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Kina jina ko Ruma?"
"Eh ina jinki"
"Yauwwa, zan gaya miki zan miki bayani, amma ba yanzu ba sai an kwana biyu, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki gane ba, kuma nan gaba ko ba a gaya miki ba ma, zaki gane da kan ki".
Cike da yarinta ta ce "Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini"
"Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin ƙara girma da hankali"
Cikin mamaki Ruma ta ce "Yaushe kuma zan ƙara girman da hankali, wancan karon ma fa na taɓa tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?"
"Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi ƙarfin kanki" sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.
A hankali ta tashi ta nufi É—aki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.
Tafiya ta yi ɗaki, ta gyara shimfiɗarta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta me hakan yake nufi kenan?. Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe tana kwance tana baccinta, duk samarin gidan sun gama komai, har abin karyawa, Kasancewar Asabar ce Ruma tana ta baccin asara, ba aikin fari balle na baƙi, har ƙasan ranta tana matuƙar jin daɗin rashin zuwa makarantar allo da ba ta yi, saboda tana samun isasshen lokacin bacci.
Ji take ina ma ace bokon ma ta daina zuwa, idan tayi baccinta ta ƙoshi da yamma ta kfa suyar wainar fulawa a ƙofar gida ta tara 'yan kuɗaɗenta.
Baccin yayi mata daɗi, tayi nisa sosai a duniyar mafarkai kala-kala, ta ji kamar daga sama ana taka mata ƙafa.
Buɗe ido tayi a hankali, amma taƙi motsawa, tana son ta tabbatar da a zahiri ne ko duk cikin mafarkin ne.
Ji tayi an kuma zungurarta da ƙafa, ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Wallahi Huzaifa zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba, kar ka sake takani"
Bai ji kashedin ba, ya sake haurinta da ƙafa, "Allah ya isa wallahi, kuma ba zan tashi ba" tayi maganar tana sake dunƙulewa a wuri guda.
Ƙashin bayanta ya kuma daka da ƙafarsa, ta yinƙuro a matuƙar zafafe, da nufin ta kafa masa haƙora ko a ina ne, amma me tayi tozali da Umar a tsaye a kanta.
Jikinta ne ya hau tsuma, ta ma rasa me za ta yi, ko ta ce.
Shiru yayi yana nazartarta, daga bisani ya ce "Ki tashi ki je ki ki yi wanka ki karya ina jiranki, kuma idan ki ka ɓata mini lokaci kin san sauran"
Saroro tayi tana kallonsa, da ba ta gama fahimtar me yake nufi ba.