← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 114

Sashe 53

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wane irin fitsarin jini kuma? A garin yaya?" Mama ta yi maganar a tsorace.

Usman ya É—an yi gyaran murya ya ce "Wato ainihin, muna tunanin, wato ko.. abin nan na mata da suke duk wata, wato haila shi ta fara" waro ido waje mama ta yi ta ce "Ban gane ba"

Mai sunan Baba ne ya karɓa yayi wa mama cikakken bayanin abin da yake faruwa.

Mama ta yi salati tare da tafa hannu ta ce "Ruma haila, iko sai Allah girma ya riga hankali zuwa, a yanayin jikinta ban taɓa kawo zuwan wannan abun yanzun ba, ikon Allah"

"Mama wai menene ya sameni?"

"Girma ki ka yi" mama ta bata amsa.

Mama ta sake kallon igiya da kayanta a kan igiya, ta jinjina kai ta ce "Lallai ƙanwar maza, yanzu har ɗan kamfan ma ku kuka wanke mata? Iko sai Allah to Allah ya shiga lamarin, amma akwai badaƙala".

"Mama wai mutuwa zan yi?"

"Ba mutuwa zaki yi ba, abin da yake hana 'yan makarantar ku salla shi ne ya zo kanki". A gaban su Yasir mama ta zauna tana yi mata bayanin komai, sai a yanzu ta gane wasu daga cikin karatun da aka yi musu a Islamiyya in da suka dosa.

Gaba ɗaya jikin ruma yayi sanyi, babu babban abin da ya tsorata ruma, sai cewa da mama ta yi ita ma yanzu za a din ga rubuta mata zunubi idan ta yi saɓo.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku, dan Allah kar a rubuta mini zunubi".

Aliyu da ta kwanta a kan cinyarsa ya ce "Wallahi sai an rubuta miki, gara tun wuri ki nutsu ki shiga hankalinki"

"Astagfirullah, dan Allah mama kar a rubuta mini zunubi, ba na jin magana, dan Allah mama kar a din ga rubuta mini zunubi bana son na mutu yanzu. Wayyo Allahna"

Mama ta ce "Iko sai Allah, na ga yadda za ayi wannan lamari da wannan yarinyar mara kan gado".

Har zuwa washegari aka samu zazzaɓi ya sauka, amma jikinta babu ƙwari, mama da kanta ta kaita banɗaki za ta yi mata wanka, sai dai pad ɗin jikinta ba ta ɓaci ba, mama tana yi mata wanka ruma tana ɓoye ƙirjinta.
Mama kawai ta yi dariya ta cigaba da silleta.

Da ta fito da ita kuwa, tuni sun haÉ—a mata tea, Yasir ya É—auko mata kayan sawa, har da pad É—in da zata saka.

Mama kawai girgiza kai ta yi, gaba ɗaya sun wani nutsu sun damu, duk saboda ƙanwarsu.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni ba zan saka wannan abar ba, damuna take yi?"

Mama ta ce "A haka zaki zauna?"

Ruma ta É—aga kai alamar eh.

"Aikuwa kya ɓata jikinki, a haka jininki ya ƙare, ni babu ruwana" mama kan ta mazewa take yi, amma lamarin ya zo mata a bazata, ba ta taɓa kawo wannan abu nan kusa a kan ruma ba.

Da ƙyar ruma ta yadda ta saka pad ɗin nan, duk nasihar da mama tayi mata, tare da bayani, lokacin salla na yi ta ɗau buta ta ce ita alwala za ta yi.

"Wai ke wace irin yarinya ce ne haka? Ba na yi miki bayanin babu salla, babu azumi, ga duk wadda take haila ba".

"To ni mama da wanne zan ji, kin ce mini za a din ga rubuta mini zunubi,. Yanzu kuma kin ce ba zan salla ba, in shiga wuta kenan?"

"Wai ke Meyasa duk bayanin da za ayi miki, ba zaki tsaya ki fuskanta ba sai dai ki yi ta wauta, Allah ne ya É—auke miki, sai kin yi tsarki zaki yi salla" Aliyu yayi Maganar a fusace dan ya fara gajiya da halin ruman, ana mata bayani tana bauÉ—ewa.

Tun ranar da ya ɗan zubo ɗin nan, bai sake zubowa ba, ruma ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, ga pad ta isheta gaba ɗaya abin duniya ya isheta.

Tun daga kwana É—ayan nan ya É—auke, mama da kanta ta kaita banÉ—aki ta koya mata yadda ake wanka, babu babban abin da yake cigaba da É—agawa ruma hankali, cewa da mama ta yi, ita ma za a fara rubuta mata zunubi.
Ta tattara laifin kacokan ta ɗora shi a kan takawa, wanda a dalilinsa duk haka ta sameta, dan daga watsa mata taɓo ya sa ta fara rashin lafiya, wannan abun ya zo mata.

Mama ta ce a bar tafiyar su katsina, sai bayan ruma ta gama warwarewa zuwa wani satin.

***
Takawa kuwa har zuwa yanzu, bai daina jin muryar ruma ta na zuwar masa ba, abin har mamaki yake bashi. Wasu lokutan a zahiri yake jin muryar tana yi masa gizo, gashi tun daga ranar yau kwanaki huÉ—u kenan, bai sake arba da wani abu da ya shafe ta ba.
Haryanzu zuciyarsa ta kasa nutsuwa da cewar ruma mutum ce, duk da sidi ya tabbatar masa da binciken da ya yi a kan ta da makarantar da take zuwa, wanda makarantar yayi niyyar zuwa, amma suka haÉ—u a hanya.
Tunawar da ya yi cewa yana da tafiya Abuja jibi zai je wata ganawa ta musamman da wasu lawyoyi, tuna hakan ya sanya shi dawowa nutuswarsa, ya bar tunanin ruma ya tashi ya fice.

Gidansu ya tafi, ya je ya samu Ammi dan sanar mata da batun tafiyar sa. Cikin damuwa Ammi ta ce "Ina fatan ba a kan mutanen ne zaka yi tafiyar ba, ka je ka cigaba da bin diddiginsu su illataka ba?"

Takawa ya ce "A'a Ammi, tattaunawa ce da wasu lauyoyi, kwanaki uku kawai zan yi na dawo"

"To Allah ya kaimu, ka kula sosai takawa, ka riƙe azkar sannan ka sanya Allah a ranka, kar saboda kana da matsala da wani ka sako shi a gaba da niyyar fansa, ka saka Allah a cikin lamuranka"

"In sha Allah ammi"

"Allah Ubangiji ya tsare, zaka ci Abincin dare a nan ne, ko kuma gida zaka tafi?"

"Ina da ayyuka a gida Ammi, ku ci abincinku kawai".

"To Shikenan, Allah ya tsare"

Ya amsa da Amin, ya tashi ya fita.

Yana daf da kaiwa in da motarsa take, motar Mummy ta yi parking. Ta buɗe ƙofar motar ta fito ta nufi Adam tana wani irin murmushi.

"Manya gatan wasa, a gidan ka wuni ashe, kwana biyu ba ka shigowa mu gaisa"

"Na yi busy ne" ya bata amsa a taƙaice.

"Ashe Abuja za ka tafi, to Allah ya tsare"

ÆŠan turus ya yi yana tunani, ya aka yi ta sani? Amma kasancewar ba ya son yin doguwar magana, mussaman da ita, ya sanya bai tsaya bin diddiginta ba, ya buÉ—e motarsa ya shiga.

***
Sarai ruma ta warke, mama ta sake haɗa mata kayanta, sai dai dare ya raba, ruma ta na cikin net ɗin ta tana ta bacci, mama kuma ta zubawa jakar da ta haɗawa ruma kayanta, haka nan ta ji ba ta son tafiyar da ruma za ta yi, kuma ba ta ji za ta iya hana tafiyar ba, ba ta taɓa rabuwa da ruma na lokaci mai tsawo ba sai wannan karon, gaba ɗaya jikin mama a sanyaye yake, ba ta da wani kuzari, zuciyarta na raya mata ko ta hana tafiyar da ruma, amma daga ƙasan zuciyarta ba ta ji ta yarda da wannan shawarar ba.

Tun asuba ruma ta fesa wanka, sai murna take ba ta taɓa tafiya mai nisa da wayonta ba, mussaman barin Kano, mama dai jiki a sanyaye take taya ruma shiryawa, tana yi tana mata nasiha, a kan ta nutsu har su je su dawo, ban da gantali da neman magana.

Ƙarfe goma na safe, suka kammala shiryawa, Aliyu ya ɗau jakar kayan, suka tafi, ruma sai ɗagawa mama hannu take tana murmushi, yayin da mama ko murmushin ta kasa, ruma ta ɗauko wayarta ta wurin Yasir, ta saka a jakarta.
Gaba ɗaya su kansu sauran yayyen na ta, jikinsu a sanyaye yake, kamar su ce a fasa tafiyar da ita, daga ƙarshe da ta gallabe su, suka ce Allah ya raka taki gona.

Ɓangaren takawa ma, yau ta kasance ranar da zai tafi Abuja, ya biya gida ya yi wa Ammi sallama, sannan ya ɗauki mai kaishi airport, ya dawo da motar. Sai dai tun a daren jiya yake jin ba ya son tafiyar, duk da ba yau ya fara tafiye-tafiye ba, amma yana jin sa wani iri, kamar akwai wani abu mai muhimmanci da zai yi nesa da shi, yana tsaye yana gyara agogon hannunsa, Ammi sai kallonsa take yi.

Ya kalleta ya ce "Ammi, ya dai na ga kina ta kallona?"

"Haka kawai bana son ka tafi ne, ji na yi kamar na ce ka fasa".

Murmushi ya yi ya ce "Ammi kenan, sai ka ce zan bar gari, saudiyya fa sai da ns kwana ashirin da takwas, kwanaki uku fa zan yi kacal na dawo, ki yi mini addu'a, idan su Nusaiba sun dawo daga makaranta, ace musu na tafi"
Ammi ta jinjina kai ta ce "Allah ya tsare" ya É—au jakarsa ya fice.

Huzaifa da Yasir, sai da suka raka su Aliyu tasha, suka hau mota, Ruma sai É—aga musu hannu take, ta na yi musu gwalo, wai ba za a tafi da su ba.

Tun da suka baro tashar suka nufo gida, jikin Yasir yake a sanyaye, Huzaifa na ta magana, amma ya kasa amsa masa.

"Wai lafiya na ji ka yi shiru?"

"Huzaifa, ji na yi ban yarda da motar nan da su ruma suka hau ba"

Ya kalli Yasir cikin mamaki ya ce "Saboda me?"

"Mutanen da suke cikin motar ne ba su yi mini ba sam, ni duk wani iri nake ji a jikina!!!

Ayshercool
08081012143

*Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haÉ—a mini document É—in littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haÉ—a mini document É—in littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Chapter 53 · 0% Book details