← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 114

Sashe 66

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wambai ransa ya ɓaci ya ce "Shi takawan da kansa yake wannan rashin albarkar? Aikuwa albasa ba ta yi halin ruwa ba, haka ya canza hali? Har galadima mai ci yana batun zai yi murabus, mun fara tattaunawa a kan akwai yiwuwar a dawo muku da sarautarku, tun da ya kawo ƙarfi, kuma shi galadima babu lafiya, ina daf da kai maganar ga mai martaba, to a haka za a bashi mulkin yana wannan rashin ɗa'ar?"

Gaban Mummy ne ya faÉ—i, jin batun wambai na cewa za a dawo da sarauta gidansu a bawa Adam.

"Allah ya baka yawan rai, ni ba ziga ba, kuma ba wai ina kushewa bane ba, amma takawa ai ba zai iya jagoranci ba, ya fiye zafin zuciya da saurin fushi, abu kaɗan idan su Fauziyya suka yi masa ba ka ga cin mutunci ba, kuma kar ka manta bashi da cikakkiyar lafiya, larurar nan da yayi tun yana yaro haryanzu fa tana tashi, ai gara a bawa mahamud duk da shi ma da sauran ƙuruciya a kansa, ko a barwa Jabir kawai"

Cikin mamaki wambai ya ce "Kina nufin haryanzu takawa bai warke ba, amma ta ja bakinta tayi shiru balle a cigaba da nema masa magani? Meke damun Binta ne?"

"To ban sani ba idan ka shiga lamarin ko a samu mafita, amma takawa bai dace da sarautar nan ba ba zai iya ba, gara Mahmud amma Mahmud haryanzu hankalinsa da saura, ai gara a bawa Jabir, idan yayi murabus shine yakamata ya gaje shi"

Wambai ya ce "Wannan ba huruminki bane ba, sai abin da muka yanke, tashi kije zamu san abun yi".

Mummy ta duƙa ta ce "Allah ya baka yawan rai, a huta lafiya" ta tashi ta bar gidan.

***

Mai sunan Baba ne yayi rigingine yana kallon saman roofing, zuciyarsa sai bugawa take yi, yana ji a ransa da ya san direction ɗin da zai nufa ya tarar da in da aka kai ruma da sai yaje ko da zai mutu a can, babban fatansa kar a lalata rayuwar ruma, gashi tun yana buga waya ya ji ya ake ciki, har ya haƙura, dan babu wani labari mai daɗi an doshi sati na biyu.
A hankali ya tashi ya buɗe ƙofar ɗakin su ya fito tsakar gida, ya ga ƙwan ɗakin mama a kunne.
A hankali ya ƙarasa ya tsaya ta window ɗakinta ya leƙa, mama na zaune ta ɗaga hannayenta sama sai zubar da hawaye take yi.

Har ya shiga ɗakin ba ta sani ba, ga furar da ya kawo mata da magariba ko taɓawa ba ta yi ba.

Motsin da ta ji ne ya sanya tayi saurin goge hawayen ta ce "Babana ba ka yi bacci ba?" Ya zauna a gabanta ya ɗan kalleta ya ce "Ba ki sha furar ba, ki yi haƙuri ki daina zama da yunwa" ba ta iya ce masa komai ba sai kallonsa da take yi.
"In É—auko miki kofi ki sha?" Yayi maganar a hankali.

Hawaye ne ya cika idonta, ya miƙa hannu ya ɗau kofin da ya kawo mata tun a lokacin, ya tsiyaya mata ya ce "Ki sha ko kaɗan ne"

"Ba zan iya ba, na san ruma ba ta sha kamar wannan ba, kar su lalata mini 'ya babana na fara karaya" tayi maganar tana rushewa da kuka.

Kamar zai yi kukan shima, ya dake duk da yadda zuciyarsa take masa zafi.

Ya kai hannu yana goge mata hawayen ya ce "Duk abin da ya sameta dama Allah ya rubuta mata faruwar hakan, amma addu'armu tana tare da ita a duk in da take, damuwar ki kawai ta isa ta ƙara mana zullumi, ki kwanta ki huta ki cigaba da yi mata addu'ar.

Haka ya lallaɓa mama ta kwanta, ba dan yana saka ran zata yi barci ba, sai dan fatan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta su samu salama.

Ya tashi cikin sanyin jiki, ya tafi ɗakinsu, sai dai yana zuwa ya tarar da Huzaifa da Yasir sun haɗa kai da gwiwa suna ta uban kuka, Abubakar yana rarrashinsu, Abdallah ma ya haɗe kai da gwiwa usman kuwa ya zuba tagumi yana bin su da kallo, hannunsa riƙe da Alqur'ani, Aliyu ne kawai a kwance shima kuma ba bacci yake ba.

A hankali mai sunan Baba ya ja da baya, ya koma tsakar gida ya zauna, yama rasa ina zai saka kansa, shima da hali kukan zai yi, ya riga ya gama karaya.

Wayewar garin Allah, jikin ruma ya ƙara tsanani, sai rawar jiki take tana kwarara wani irin koren amai, ga kukan ciwon ciki da take yi duk ta fita hayyacinta.

Babu wanda ya damu da halin da take ciki, sai wannan matar, da a yanzu ba ta kanta take ba ta ruma take, saboda tausayin da take bata, sai sannu take yi mata, tun tana iya amsawa, har ta daina .

Cikin damuwa matar ta ce "Dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kai yarinyar nan asibiti, kar ta mutu a haka, wallahi tana jin jiki sosai".

"Idan ta mutu meye naki? Ki ji da kanki mana uwar shishshigi" wani daga cikinsu ya bata amsa.

Cikin damuwa ta ce "Amma yarinya ce, dan Allah ku taimaka ko magani ku sai mata kar ta galabaita" banza suka yi mata suka cigaba da shaye-shayen su.

Kamar zata yi kuka, sai sannu take yi wa ruma tana dafa goshinta.

Ruma kuwa sai jujjuya kai take tana kiran sunan mama, duk ta fita kamar ta shekara tana ciwo.

Ko da rana ta É—an É—aga idon matar nan yayi ja, jikinta sai rawa yake saboda yunwa da take ji, ga É—an cikinta sai motsi yake, ga mura da ta addaba mata, amma tafi tausayin halin da rumaisa take.

Mijin iya ne wato dagaci a tsaye a tare da wannan dogon mutumin da su ruma suka taɓa haɗuwa da shi.

"Dan Allah dogo ku taimaka dan zatin Allah ku sako yarinyar nan, ko ku faÉ—i abin da za a baku, ba 'yar garin nan bace ba, a mayar da ita hannun ahalinta wallahi marainiya ce".

Dogo ya ce "Ni ba 'yan ƙungiyar mu ne suka kawo farmaki ba, kuma dama yarinyar na ga kanta yana rawa, tun da aka kai wannan lokacin ba su ce muku komai ba, wataƙila sun kasheta".

Cikin kiɗima dattijon ya girgiza kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah tun da baka tabattar ba ka duba mini, waɗanda suka sako suka dawo gida,  sun ce mana tana can a raye, dan girman Allah ka duba mini ka sanya baki a lamarin nan dan Allah"

"Ni ne zan saka bakin? Su sha tara ne fa suka yi aikin, ban maka wannan alƙawarin ba, zan dai je na duba maka ko tana nan"

Dagaci ya ce "To shikenan, hakan ma na gode sosai"

***

Mummy na barin gidan wambai ta tafi gidan aminiyarta Hajiya Lubabatu, domin fesa mata labarin da ta guntso a gidan wambai.
Sam labarin bai yi wa Hajiya Lubabatu daÉ—i ba.

Cikin hasala take cewa "Yanzu saboda tsabar wulaƙanci ace har yana shirin yin murabus amma ni ban sani ba".

"To da baki sani ba ni ba gashi na gaya miki ba, kuma shi yana can Germany ke kina nan ta ina zaki sani?"

"Amma shima wannan wamban ƙasurgumin munafuki ne"

Waro ido mummy tayi ta ce "Rufa mana asiri kar wani ya ji mana, ke ai ba a wannan yakamata ki mayar da hankali ba, wai yana tunanin idan yayi murabus Adam za'a dawo wa da sarauta, sai dai na gyara miki hanya, dan na kunno mus wuta daga shi har uwarsa, dan sai da na tabattar da na fusata shi sosai a kansu. Yanzu dai ki nemi Jabir ku tattauna a kai, ku yi duk iya ƙoƙari kar a rabaku da sarautar nan, Jabir ya gaji ubansa".

Hajiya Lubabatu ta ce "Ai faɗa ma ɓata baki ne, ai dan ubansa dole ya zo ya san abin yi, ya tare a gindin Adam sai ka ce ubansa".

"To wallahi ku san abun yi"

"Kar ki damu zaki ji ni" daga haka suka cigaba da hirarrakin su.

****
Kamar a bayi haka aka fara rabawa su ruma abinci, gurasa É—aya da ruwa É—aya, haka ake basu kullum, sai ranar da Allah ya kawo wannan mutumin, ya kan kawo mata abinci.
Wannan matar kuwa ko magana ta kasa saboda a wahale take, ji take kamar yunwa za ta kasheta.
Ko da aka bata gurasar nan ba ta tsaya komai ba, ta yi loma uku da ita, saboda azabar yunwar da take ji.

Ruma ta miƙa mata tata ta ce "Gashi ki ƙara da tawa ni na ƙoshi".

Matar ta girgiza kai ta ce "A'a, ke ce baki da lafiya, ki daure ki ci, sai ki ji ƙwarin jikinki" ruma ta girgiza mata kai alamar a'a.

Matar ta saka gefen zaninta, ta sharewa ruma gumin da ta fara yi, saboda zazzaɓin jikinta ya sauka.

Mutumin da ya tinkaro su, ruma ta tsaya ta zubawa ido, sarai ta gane shi, mutumin da ya tare su yana tambayar wacece ita?
Kenan duk rabin mutanen garin abu É—aya suke yi kenan, satar mutane? Ta tanbayi kanta.

Suka gaisa da 'yan bindigar da suke wurin, ya yi musu magana da yaren da ruma ba ta iya ji.

Suka amsa masa, sannan ya shiga duba mutanen wurin, can ya nuno ruma, ya ce "Waccan ce".

Ƙaton da ya taɓa dukan ruma da bakin bindiga ya tashi ya je ya danƙo ruma, kamar an yi cinikin kaza za a sayar haka ya fizgota, cikin dakiya ta fizge hannunta tana haki.

"Bata da lafiya ka yi mata a hankali" cewar matar da haryanzu ruma ba ta san sunanta ba.

"Ke idan baki kiyayeni ba, da shiga abin da ba a saka ki ba, wannan cikin naki ba zai hana na keta miki haddi ba a gaban jama'a ba, ki shiga hankalinki" daga haka ya mayar da idonsa kan ruma ya ce "Wannan ka ce ko?"

Dogo ya ce "Eh ita, ya ce ku taimaka ku faÉ—i abin da za'a bayar ku bayar da ita"
Chapter 66 · 0% Book details