← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 114

Sashe 114

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Ka biya ka fara ajiyeta a gida, ka sanar musu halin da ake ciki, don a saka ido sosai a kan ta ta daina missing makaranta, kuma kar ta sake yin wannan doguwar tafiya haka a ƙafa ita kaɗai"

Ya jinjinawa ammi kai.

Rumaisa ta fito, idanun nan sun yi ja ta ce "Ammi zan tafi".

"Maman Sabir har kin gama, bari ya mayar da ke gida" rumaisa ta kalli Adam sannan ta kalli ammi za ta yi magana, ammi ta girgiza mata kai ta ce "Ba'a jayayya da umarnin giwar galadima" Ammi ta yi mata maganar cikin gargaÉ—i, haka ya tilastawa rumaisa yin shiru.

Adam ya miƙe yayi gaba, rumaisa ta durƙusa ta sumbaci goshin sabir, sannan ta bi bayan Adam.

Kamar yadda ransa yake a haÉ—e, haka ita ma ta tsuke ta ta fuskar, babu alamar wasa da yarinta.

"Laa ka ga, bawan Allah" Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa, da gudu ya ga ta nufi jikin bishiyar dabinon da ke tsakiyar harabar gidan. Mahmud ne a tsaye yake waya, amma ya katse wayar ya zubawa rumaisa ido yana jiran ta ƙaraso.

Ta ƙarasa tana ɗan haki ta yi murmushi ta ce "Ashe ba kai ne shi ba?"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

Rumaisa ta nuna masa in da Adam yake.

"Na zata shine da na ganka ɗazu, idona ya rufe sosai da ɓacin rai, ga gajiya kuma kuna kama sosai da sosai, dan Allah ka yafe mini na yi maka rashin kunya a gaban mutane"

Yayi murmushi ya ce "Kin ga jaririn naki?"

"Na ganshi, Allah ya saka maka da alkhairi da ban ganshi ba yau, da ina ga mutuwa zan yi. Ɗa na ne fa anty aisha ta bar mini shi, amma ya ƙwace shi kuma wai ya hana ni shigowa gidan nan"

"Wace aishar?"

"Kai baka san ta ba? Kai ba É—an nan gidan bane?".

"Eh ɗan nan gidan ne, amma bana ƙasar jiya da daddare na dawo".

"Au ho, to in gaya maka sace ni aka yi a katsina, sai aka sato anty aisha matarsa, ta haihu ta rasu ta bar mini jaririn na kuɓuto da ƙyar, bayan na yi kwanaki ina wahala, amma ya ƙwace ɗan kuma wai idan na zo kar a sake barina na shigo, dan Allah wannan ba mugunta ba ce ba?"

Mahmud ya yi murmushi ya ce "Bai kyauta miki ba gaskiya"

"To kai baka taɓa zuwa sashin ammi ka ga jaririn ba, au ashe fa ka ce jiya ka dawo, ba ka ga ɗan nawa ba, mai kyau tubarkallah, ai na san ammi zata nuna maka shi ma, tunda a gidan nan ka ke"

"Eh a gidan nan nake, amma ni ba a sashinsu nake ba, ni É—an Mummy ne".

"Wacece kuma hakan?" Ta tambayeshi tana É—an gyatsine fuska.

"Babata ce, ko baki san mata biyu ne a gidan nan ba? Anyway na ga kamar jiranki yake yi, ki je kar ya zo nan wurin ya karairayaki, shi yafi masa komai sauƙi"

Cikin fitsara rumaisa ta ce "Wallahi wuce nan, na gode sosai ba zan taɓa manta taimakon da ka yi mini ba yau, kuma ka na da kirki fiye da wancan mutumin, dan Allah ka je ka ga ɗana a wurin ammi, sunanshi Mahmud ana ce masa sabir" tana maganar ta yi gaba tana murmushi.

Turus Mahmud yayi ya bi rumaisa da kallo, Adam ya sanyawa É—an sa sunan Mahmud? Ya tambayi kansa, dan abun da mamaki.

Wurin motar adam ta nufa, da tuni ya kunnata, ya fito ya saka ana karkaɗewa motar ƙura.

Ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Bawanki ne ni da zaki shanya ni ki tafi yawon surut?".

Ta kalleshi ta ce "Ba yawon surutu na tafi ba, godiya na je yi masa na bashi haƙuri. Ya nuna mini karamci saboda ni ɗan adam ce bai koreni ba ɗazu da na rasa nutsuwa ta ina kuka ba, ya taimaka mini na samu abun da nake so". Ta yi maganar irin ko maganar ta yi masa daɗi ko kar ta yi masa bai shafeta ba.

"Tun daga lokacin da ki ka sake shigowa rayuwata, ki ke ta wasu irin halayya da son nuna lallai akwai wani abu a tsakanina da ke, ina ɗaga miki ƙafa albarkacin yaron nan da kuma ƙuruciyarki, idan ki ka cigaba da wannan abubuwan ki ka shiga trap ɗi na zaki sha wahala na gaya miki, and as from today kar ki sake zuwar mana gida, abun da ki ka yi Allah ya baki lada, bana buƙatar sake ganinki a cikin gidan nan da sunan kin zo ganin yaron nan, idan kuma ki ka cigaba da zuwa zan nesanta shi da ke, nisantawa mai tazarar gaske da ba zaki iya cimm masa ba, dan haka idan ma wani abun ne a ranki ya sanya ki ke bibiyarsa, ki saka abun da na gaya miki a ranki. Idan har zaki cigaba da bibiyar yaron nan, za'a iya amfani da ke a cutar da shi, dan haka bana buƙatar sake ganinki a kusa da shi" yayi maganar cikin kashedi.

Cak ta tsaya ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta yi, sai wasu irin hawaye da suke zubowa daga idonta.

Ayshercool
Chapter 114 · 0% Book details