← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 114

Sashe 84

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga nesa yake kallonsu, ya tattara nutsuwartsa a kan Iman, tamkar ba bugun Nigeria ba haka take.

"Ruky wannan ma 'yar gidanku ce?"

Ruƙayya ta waiwaya ta hango su Ammi, a fusace ta dube shi ta ce "To ba 'yar gidan nan ba ce, tsintota aka yi aka riƙeta a gidan nan, babu wanda ya san danginta ma, wataƙila ma ba ta da uba"
Maimakon ya fusata sai ya ce "Wow, amma dai a ƙasashen Larabawa kuka tsinto ta ko? Ko irin Afrika ta gabas ɗin nan".
"A'a africa ta sama, aka tsinto ta aikin banza " ta tashi fuu ta shiga ciki.

Tashi yayi yana kiran sunanta, amma bata ko sake waiwayo wa ba ta tafi.

"Wallahi na gaji, ni da gidan ubana saboda bala'i ban fiye zama ba, ko na kawo baƙina ba, da gayya idan bar zan yi baƙo mu zauna a harabar gidan nan, sai wannan banzar yarinyar ta fito, ita kuma ammi ta wani sako su a gaba riii kamar shanu, duk yadda na ƙallafa rai a kan gayen nan, yana ganinta ya hau wani surutu, ji nake kamar na zuba mata wuta a fuska uban kowa ya huta".

Mummy da take jin ta tayi shiru ba ta yi mata magana ba, ta ƙaraci bala'inta ta gama, amma Mummy ta fara hasala, duk yadda suka kai ga ɓata iman, ba ya wani tasiri sam. Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "daga yau idan kin yi baƙi, ku din ga shigowa falon waje, kuna zama, ku bsrni da ita, zamanta a gidan nan ya kusa expire " haka ruƙayya ta zauna tana cigaba da huci.

***
Yasir da Abdallah basu saki jikinsu ba, sai bayan ganin kyakywar tarbar da Bashir yayi musu, ya kai su wani katafaren office, har da sanyawa a kawo musu ruwa da lemo.
Abdallah ya ce "Ranka ya daÉ—e mai É—an uwana yayi ake nemansa ne? Hankalinmu ya kasa kwanciya, kar wani abu ne ya faru, mahaifiyar mu babu lafiya, ba wanda muka sanarwa ma a gida"

Bashir ya yi murmushi ya ce "ÆŠan sanda ai abokin kowa ne, ba abun tashin hankali bane, ni na so mu zo har gida amma wani aiki nake yi wa uban gidana. Shekaranjiya aiki ya kaini jihar katsina, na kwana É—aya a can, a kwana na biyu na kamo hanyar baro garin, na tsinci wata yarinya da jariri a gefen hanya, wani mutum yana tambayarta, so nayi amfani da id card É—ina, muka kaita asibiti da yaron, amma yarinyar ta kasa bamu haÉ—in kai saboda jaririn nan, so a jiyan muka taho kano, aka kwantar da ita a asibiti ita da yaron, ta ce mini dai É—anta ne, na yi reporting wa abokan aikina, shine ta bani lambar wayar Yasir ta ce mini yayanta ne, suananta Rumaisa.

Miƙewa tsaye suka yi tsaye gaba ɗayansu, suna kallon Bashir, amma suka kasa magana.
Bashir ya miƙe ya ce lafiya kuwa?"

Tuni hawaye ya wanke fuskar Yasir ya ce "Yallaɓai ina ruma take, ƙanwarmu ce aka saceta a katsina, tafi wata biyu kusan watanta uku a hannun 'yan bindiga, dan Allah tana ina"

Bashir ya dafa kafaɗar Yasir ya zaunar da shi ya ce "Calm down, tana nan ana kula da lafiyar ta, ku godewa Allah, duk da ba ta gaya mini meyafaru ba, amma dai gaskiya a galabaice take, ikon Allah ne ya fitar da ita, tana nan asibitin koyarwa na kano, zaku bamu bayanin yadda aka yi ta ɓata da komai da komai ". Daga Yasir har Abdalla aka rasa mai magana, dan Abdallah durƙusawa yayi yana kuka dan tuni suka fara fitar da rai.
Nan Bashir da abokan aikinsa, suka din ga rarrashin su, suka gaya musu iya abun da suka sani, daga tafiyar su ita da Aliyu zuwa yanzu, aka kuma duk wasu cike-cike da za ayi, aka ce zasu tafi Asibitin wurin rumaisa.

Abdallah ya gige hawaye ya ce "Yallaɓai zamu iya kiran gida mu sanar musu, mahaifiyarmu na nan ba yadda take saboda azabar tunani da damuwa"

"Eh ku kirata ku sanar musu".

Yasir ya ce "Mai sunan baba zaka gayawa, shi zai san yadda zai ya sanar mata, kar ta gigice jininta ya kuma hawa".

Haka kuwa aka yi, sai dai Umar bai ɗaga wayar ba, sai Aliyu aka samu, gaba ɗaya ya rikice da jin maganar, amma yayi iya ƙoƙarinsa ya saita kansa, mama ba ta gane ba, ya sanarwa Usman da Mai sunan baba.

Mai sunan  ya ce su yi gaba, zai taho da mama, ba tare da ya bari ta gane wani abu ba, su fara zuwa su duba idan da gaske ruman ce.

Tun da rumaisa ta ɗan farka, Yayar bashir ke fama da ita ta ci abinci, amma ta gardame ta ƙi ci, sai surutai kawai take marasa kan gado, tana kukan ita fa a kawo mata jaririnta. Sai da nurses suka ɗauko shi, an saka masa kaya, sai dai ya ɗan yi dama dama, an sanya masa robar hanci, ta nan ake ɗura masa madara.

Rumaisa ta zubawa jaririn ido a hannun Asiya, tana bashi madara ta sirinji, sai ta ga ta koma mata suffar Aisha.

"Anty Aisha, kin ga amanarki? Ashe nan suka kawo ki suka barmu a can?".

Asiya ta ce "Asiya dai, sunana kenana ba Aisha ba" sai da ta yi magana, sannan rumaisa ta ga ta koma Asiyan.

Ita kanta ruman a yanzu bata iya banbance wacece ita, da kuma rayuwar da take yi.

Ƙofar ɗakin aka buɗe, rumaisa ta ɗaga kai, bashir ne a farko da wasu 'yan sanda, Yasir ya ture su, ya rugo da gudu ya zo ya rungume rumaisa yana kuka.
Rumaisa ta kwantar da kanta sosai a jikinsa ta ce "Yasir, idan ka zo mafarkina ka daina tafiya, ka barni tsoro nake ji". Bai san me ma take faɗa ba, Abdallah ma ya garzayo ya rungumesu gaba ɗaya, sai dai ruma ba ta da ƙwarin da zata iya rungumesu ita ma. Dan ita gaba ɗaya ta riga ta yadda da cewa mafarki take yi.

Abdallah ya kalleta, 'yar da mama ke ta tattalawa tana kula da tsaftar ta da jikinta, sai gata duƙun-duƙun kamar ta warke daga ciwon hauka, koma dai wadda take cikin haukan tuburan

Su Usman ne suma suka banko É—akin, suna addu'ar Allah ya sanya rumaisan ce.
Suna ganinta suma suke kewayeta suna kuka, kallo É—aya zaka yi mata ka san ta sha azaba ta wahala.

"Dan Allah duk kar ku tafi ku barni, mu yi ta zama a cikin mafarkina" tayi maganar tana fashewa da kuka. Babu wanda ya rarrashe su, kai da ganin yadda zaratan samarin ke kuka, ka san sun shiga ɗimuwa da ɓatan 'yar tahalikar.

Mai sunan Baba da ƙyar ya lallaɓo mama a kan zai kai ta ganin likita wani asibitin daban, ta ce ba zata ba, wani abun suke ɓoye mata kawai, sai da suka kai ruwa rana sannan ta yadda.

Ko da suka isa É—akin da ruma take, kasancewar Usman ya tura masa message na sun ganta rumaisa ce, ya sanar masa É—akin da take.

Ko da mama tayi ido huɗu da rumaisa ƙamewa tayi, sai ruwan hawaye.

Ruma ta hau miƙa mata hannu tana hawayen ita ma ta ce "Mama dan Allah ki zo in taɓaki kar na tashi daga baccin na ga kin tafi" Mama ta ƙarasa ta ƙanƙame rumaisa kamar ta mayar da ita ciki.

"Dan Allah mama kar ku tafi, kullum sai kun zo a mafarki na ganku, amma sai ku tafi ku barni a wannan dajin mukaÉ—ai, dan Allah mama ki zauna da ni, Allah ya sa kar na tashi daga baccin nan, mamana tsoro nake ji kar ki bari na farka"

"Ruma nima ji nake kamar mafarkin ne, ina ta gaya musu kin dawo kina waje amma basu yadda ba, Allah Alhamdilillah" tayi maganar tana sake rungume rumaisa.

Wata nurse ta shigo da tray na magunguna ta ce "Gaskiya bayin Allah kun yi yawa a ɗakin nan ku ragu zan yi mata allurai, bacci muke son tayi ƙaaƙwalwarta ta huta" ta yi maganar tana ƙarasawa gaban gadon rumaisa.

Bashir ya ce "ki bi a hankali, watanni uku ba sa tare an saceta, ki bari ta ga ahalinta"

Nurse na ƙoƙarin ɗaga hannun ruma daga jikin mama ta yi mata allura, a zuciye rumaisa ta yi jifa da trayn "So ki ke dole na tashi daga baccin? Bana so ki ƙyaleni" ruma tayi maganar kamar mai shirin tayar da aljanu.

Sai a yanzu mai sunan baba ya ƙarasa, ya zauna a gefen gadon, ya ɗago rumaisa daga jikin mama, ya rungumeta a jikinsa, ya ɗago hannunta ya riƙe ya ce "Yi mata abun da ya kamata"

Ta yi lamo a jikinsa, sai kuma ta ce "Mai sunan baba".

Ya ce "Na'am"

"Yau a mafarkin nawa ba zaka sakani kama kunne ba? Kullum idan ka zo sai ka sakani kamun kunne, amma ko zaka sakani kamun kunnen, ka zauna a mafarkina, tsoro nake ji bana son duhun nan" tayi maganar tana shirin fara fizge-fizge amma ya danneta a jikinsa ana gama allurar ta cigaba da bacci.

Bayan baccin ya É—an É—auketa, mama ta share hawayenta ta ce "Aliyu, ku je gida ku zo da ruwan zafi, ayi mata wanka, kan mutane su ji su fara zuwa"

Bashir ya ce "No, kar a taɓata tukuna sai zuwa dare, muna jiran result ɗin likita tukuna, sai ayi mata wankan, sannan akwai jariri da na tsince su tare, ta ce mini ɗanta ne, duk da ni ban ga alamar hakan a tare da ita ba".

Mama ta ce "Jariri kuma?"

Asiya dake gefe ta miƙa musu jaririn ta ce "Gashi, bayan tafiyarka ta sanya rigima sai da aka ɗauko shi".

Mama ta karɓi jaririn tana ƙare masa kallo, Bashir ya ce "Ikon Allah, ban yi zaton yaron nan zai rayu ba, amma cikin ikon Allah kun gan shi, har da sauran ƙazantar haihuwa a jikinsa na gansu".

Usman ya ce "to a ina ta samu jariri?"

Aliyu ya ce "Oho, tubarkallah gashi ƙato mai kyau.

Ruma tana baccin nan, aka juyata ana wanke mata raunin da yake ƙeyarta, gashin kanta har da kwarkwata, ban da tarin datti da dauɗa.
Chapter 84 · 0% Book details