← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 114

Sashe 68

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagaci kuwa tun da suka yi magana da dogo, a kan zai je ya bincika masa ruma, ya kira Aliyu ya sanar masa domin hankalinsu ya É—an kwanta, dan haka suka cigaba da dakon abin da dagacin zai ce masu, gashi Aliyu ya riga ya gaya musu yadda suka yi dagaci, dan haka mama kullum sai ta tambayi Aliyu, haryanzu dagaci bai yi magana ba?.

***
Kasancewa Adam ba a family house ya kwana ba, Kamar kullum bisa ga al'ada yana biyawa ya gaida Ammi, dan haka yau ma a cikin hanzari ya yake tafiya, ya ƙarasa sashinta.
A bedroom ya tarar da ita, sai dai saɓanin kodayaushe, ya tarar da fuskarta a haɗe, hakan ya tabattar masa da akwai damuwa.

Sai dai ya bari sun gama gaisawa, sannan ya ce "Allah ya baki yawan rai, lafiya na ga fuskar ki babu walwala?"

Ammi ta ce "A'a lafiya ƙalau, wambai ne ya bani saƙon cewa idan ka tashi daga aiki, yana nemanka" sak takawa yayi, ya dubi Ammi ya ce "Wani abu ne ya faru?"

"Ni ma ban sani ba, kawai dai ya ce yana nemanka?"

"Ko laifi na yi mass?" Adam ya sake tambaya.

"Ban sani ba takawa, ka je dai ka ji ko menene"

"Shikenan" ya faɗa a taƙaice, ya tashi ya ce "Na tafi".

"Allah ya tsare" Ammi ta faÉ—a ba tare da ta kalleshi ba.

Har ya kai bakin ƙofa Ammi ta ce "Adam!" Sai da tsigar jikinsa ta tashi, dan abu ne mai wahalar gaske ta kira sunansa haka kai tsaye.

Ya tsaya ya waiwayo ya kalli Ammi.

"Idan ka je wurinsa, ko me zai ce maka ban yadda ka tofa ko ka yi ƙoƙarin kare kanka ba, ka bishi da to kawai"
Ɗan shiru yayi yana nazari, akwai wata a ƙasa kenan, a zahiri kuma ya ce "To, in sha Allah".

A falo ya haÉ—u da Nusaiba, ta gaishe shi, bai iya amsawa ba sai jinjina mata kai kawai ya fice.

Yana tafe yana auna kashedin ammi da kiran da wambai yayi masa, saboda shi a yanzu tension ɗin da yake ciki ya ishe shi, ba sai an ƙara masa da wani ba.

Nusaiba ta shiga É—akin Ammi, ta tarar da ita zsune a gefen gado, ta yi shiru.

"Ammi" Nusai ta yi maganar kamar tana tsoron wani abu.

Ammi ta kalleta ta ce "Na'am ya aka yi?"

"Amma dai baki gaya wa takawa yadda kuka yi da wambai ba ko, kar ya hasala?"

Ammi ta girgiza kai ta ce "Ta yaya zan gaya masa, ni babban fatana idan ya je kiran da yake masa, Allah ya sa kar yayi masa irin cin mutuncin da yayi mini, kin san halin yayan naku da zuciyar tsiya babu lallai ya jure, dan ma na taushe shi kan ya tafi"

Jiki a sanyaye Nusaiba ta ce "Ammi ni fa gaba É—aya a maganganun da yayi, na kasa gane wane point yake son yayi magana a kai, sai kame-kame kawai yake yi yana faÉ—a na babu gaira babu dalili, ko dai Mummy ce ta je ta gaya masa wani abu?"

Ammi ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, kin san shi dai dama mutum ne mai zafi, a bar maganar kawai, 'yar auta ta ba ta tashi bane?"

"Eh bacci take yi, kin san exams suke shirin farawa".

Ammi ta jinjina kai, ta cigaba da jan carbinta.

****
Hatta masalattan unguwar su rumaisa, duk salla sai an yi addu'ar Allah ya bayyana rumaisa, saboda garkuwa da rumaisa abu ne da ya zo a bazata, kusan za a iya cewa ita ce yarinya ta farko da aka sace a unguwar, dan duk irin wannan abubuwan sai dai a ji su a nesa, amma yau gashi a cikin unguwa.

Kamar yadda dogo ya yi wa dagaci alƙawari, ya koma masa da maganar ruma.
Tun da dagaci ya ji dogo ne ya zo yake nemansa jiki na rawa ya tashi, ya fita tare da fatan Allah ya sa a dace a samu rumaisa.
Iya ma tashi tayi ta biyo bayansa, ya tsaya ya kalleta ya ce "Ke kuma ina zaki?"

Cikin rikicewa Iya ta ce "A ruÉ—e nake, ni dai mu je in ji me zai ce"

"Dan Allah ki koma, duk yadda muka yi da shi, idan na dawo zan sanar miki" da ƙyar ta yadda ta koma gida, amma ta ja ta tsaya a tsakar gida.

Cikin sauri ya fito ya iske dogo suka gaisa, cikin zaƙuwa ya ce "Ya ake ciki ka ganota?"

Dogo ya ce "Eh na ganota, tana rukunin su sha tara, sun ce ba zasu bayar da ita ba, ba sa buƙatar kuɗin fansarta, dan haka ku cigaba da addu'a, wannan yarinyar halinta zai iya sakawa su kasheta, halin na ta nema ya sanya suka ce ba zasu bayar da ita ba, dan haku ku cigaba da addu'a kawai." Daga haka dogo bai kuma ce masa komai ba ya yi tafiyarsa.

Dagaci kuwa ya tsaya ya dinga nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Jiki a sanyaye ya koma cikin gidan, iya ta tare shi tana faÉ—in "Ya ake ciki, me suka ce maka?"

Yayi shiru ya kasa magana. "Dan Allah ka yi magana mana, menene ya ake ciki ya ganota? Sun faÉ—i me za a basu?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Tana nan a raye, amma sun ce ba sa buƙatar kuɗin fansa, ita ɗin suke so, halinta ya saka suka ce ba zasu bayar da ita ba ta zama ta su"

"Wayyo Allah na shiga uku, yarinyar mutane ta salwanta a dalilinmu, na shiga uku na lalace".

"Meye haka ki ke yi kulu? Wannan ai rashin hankali ne".

"Ƙyaleni na yi rashin hankalin, har abada uwar 'yar nan ba zata mamta da ni da gwaggo ba na shiga uku, da na sani ban karɓi rumaisa ba, ban san haka zata faru ba, Allah ka shiga lamarin nan wayyo Allahna"

Haka dagaci yayi ta fama da iya tana kwarmato da ɓurari.

****
Rana ce ta take a kan su ruma, a hankali ta ja jikinta da yake mata ciwo, ta tashi zaune, jikinta babu abin da yayi saura sai tsabar ƙarfin hali da taurin kai.
Da wannan ƙaton ta fara tozali yana hararata, ita ma hararar ta watsa masa, ta mayar da idonta kan matar nan, ta fara tattaɓata. A hankali matar ta buɗe ido, ta kalli ruma, tana ganin fuskar rumaisa ta yi murmushi. Ita ma ruma murmushin ta yi mata sannan ta ce "Tashi koma waccan bishiyar, nan rana ta tarar da mu".

Cikin ƙarfin hali ta ce wa ruma "Ba su yi miki komai ba ko?"

Ruma ta jinjina mata kai, da ƙyar matar ta tashi, da rarrafe suka canza wuri zuwa wata inuwa suka zauna.

"Yunwa ki ke ji ko?" Ruma tayi maganar tana kallon matar.

Ta girgiza wa ruma kai ta ce "A'a, ke nake so ma ki samu ki ci wani abu, baki da lafiya, dan Allah ki daina rigima kar su illata ki, ba zan ji daÉ—i ba".

Ruma ta ce "Mhmm ki daina damuwa da ni, ni na saba da kasada, sonake su kasheni na huta na gaji".

"A'a bana son a kashe ki, in sha Allah zaki fita lafiya ƙalau".

"Ban ga alamar hakan ba, gara na tunzurasu su kasheni na huta, suma su huta amma wallahi in dai suka barni a raye na din ga tayar wa da uban kowa hankali kenan".

Matar ta waro ido ta ce "Ke ba kya jin tsoro ne?"

"Taɓ, ai tsoro yayi yamma na yi gabas, ni fa ƙanwar maza ce guda bakwai, ko 'yan unguwarmu sun sanni, dan ma na daina dambe da maza, yayyena sun hanani, duk wata kasada idan na ɗauko in tafi ƙarfina su suke shigar mini, ni fa har wata 'ya na taɓa karyawa. Bindigogi ne fa kawai da su, to wallahi bana tsoron bindigar su kamar yadda nake tsoron mai sunan Baba".

"Waye haka kuma?"

Ruma ta gyara zamanta ta ce "Yayana ne, sunanshi umar, hmmm ina tsoron Allah ina tsoron sa, nifa bana jin tsoron mama kamar yadda nake tsoron sa, kin san idan nayi laifi baya tashi hukuntani, sai cikin dare ina tsaka da bacci zan ji ni a sama, in zata ko raina aka zare kin san ance idan mumini ya mutu, to sama ake yi da ransa, to sai na ji an watsoni tsakar gida, sannan nake gane ai ina duniya, hukuncin ma sunan Baba ne, idan ya haÉ—e rai ya tattare girarsa sai na ji kamar in zawo a tsaye".

Duk da halin da suke ciki, bai hana matar yin murmushi ba, dan ba ƙaramin dariya ruma ta bata ba.
Ruma ma Murmushin ta yi ta ce "Mai sunan baba dodon marasa hankali in ji mama, idan ya sakani kama kunne a daren nan, to wallahi da asuba a zaune zan salla saboda azaba, mai sunan Baba ya iya punishment"

"Ni kuwa zan so na ga mai sunan Baban nan da ki ke tsoro fiye da bindiga".

"Kema idan ki ka ganshi sai ya baki tsoro, shi fa ba ya dariya, kullum fuskarsa a haÉ—e, wataran ko hararata yayi sai na kwana uku a nutse".

Dariya suka yi tare, ruma ta ce "To baki gaya mini sunanki ba, ina mijinki da 'yan gidanku?"

Matar ta yi murmushi ta ce "Suna na, sunana Aisha".

"Anty Aisha, ke a wani garin ki ke?"

"Zan gaya miki, yanzu jikina babu daÉ—i na bugu, yaron cikina sai juya wa yake".

Cikin damuwa ruma ta ce "Sannu, Allah ya sa su sake ki kan ki haihu, Allah ya sa ki amayo shi lafiya"

Cikin dariya ta ce "Me zan amayo?"

"Ɗan mana, ba ta baki ake yo aman jariri ba, haka mama ta ce mini, amma su fa akuyoyi to ta wurin kashin su suka haifo ɗa, daga yi wa mama tambaya ta ce idan na kuma wurinda akuya ta haihu sai ta zaneni" halin da Aisha ke ciki bai hanata yin dariya ba, ta riƙe cikinta, saboda dariyar ta ƙarfin hali ce.

"Ya naga kina dariya, ko ba ta nan ake haihuwar ba?"

"Ta nan ne mana, Allah ya sa na amayo shi lafiya".
Chapter 68 · 0% Book details