← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 114

Sashe 89

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam bai kums cewa komai ba ya tashi ya shiga banɗaki, bai san a yaya yayi wankan ba ma, ya fito, Ammi ta saka shi a gaba, ya ɗan zuƙi shayi kaɗan ya fita. A falo ya tarar da Bashir, su Iman suna gaishe shi, amma babu wadda ya amsawa haka ma barorin da suke wurin, ya ce wa bashir tashi mu tafi.

Ammi ta bi bayansu tana yi musu magana ƙasa-ƙasa.

Nusaiba ta yi wa iman kallon meyake faruwa ne, iman ta É—an É—age kafaÉ—a alamar ita ma ba ta sani ba.

A harabar gidan suna shirin hawa mota, sai ga motar Jabir ya shigo gidan, takawa bai tsaya ba ya shiga motar bashir, saboda baya son magana da kowa a halin yanzu, kuma ya san jabir ritsa shi zai yi da tanbayoyi masu ma'ana da marasa ma'ana.

Takawa suna tafe a hanya shi da bashir, babu mai cewa komai, can bashir ya ce 'Adam ka kwantar da hankalinka, komai zai tafi dai-dai ina kyautata zaton zamu samu duk wani information da zai iya taimaka mana a kan binciken mu".

"Bashir, komai ya hargitse mini, ban san ta ina zan kuma sake fuskantar matsalolina ba, jiya kwana na yi ina tunani, yaya aka yi yarinyar nan ta kuɓuta da jariri ina Aisha take, wani irin tashin hankali da tozarci ne haka ace matarka ta haihu a hannun 'yan ta'adda?" Yayi maganar cikin tsananin damuwa da zafin rai.

Bashir ya dafa shi ya ce "Calm down, ka bi komai a hankali, komai zai dai-dai ta in sha Allah".

Baba uwani ta kasa zaune ta kas tsayez babban burinta shine ganin yadda za ta yi ta san meyake faruwa, ta samu ta kaiwa Mummy labari, domin a kan idonta Ammi da takawa suka shigo a daren jiya, haka zalika yanayin yadda ta ga fuskokinsu a wayewar garin yau ta sake tabattar da akwai wani abu da yake faruwa kuma da alama babban al'amari ne, amma babu wata hanya ko kafa aka bari balle ta ji labarin.

Bashir sai da ya tsaya a hanya ya sai carton carton na ruwa da maltina, suka ƙarasa Asibitin da rumaisa take.

Bashir ya sanya masinja ya É—auko kayan da suka zo da su, ya biyo su.

Da sallama suka shiga ɗakin da rumaisa take, ba dan ƙarancin shekarunta ba, kai ka ce mai jego ce, saboda yadda take rungume da jariri a hannunta, usman ya amsa musu sallamar ruma kuma ta ɗago ta kallesu.
Bashir ya sallami masinjan nan, sannan suka zauna, suka gaisa da usman, suka tambaye shi mas jiki ya ce da sauƙi, wanda duk bashir ne yake yi, Adam ba ya iya magana.

"Rumaisa ba magana, ina kwana ya baby?".

"Lafiya lau" ta faɗa tana satar kallon takawa da yayi zuru-zuru ta taɓe baki.

Mu ga babyn yayi maganar yana karɓar jaririn yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, kin ga babyn zai warke ya barki, gaskiya ki daina langwai" ita dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Bashir ya miƙawa adam yaron, ya kuma kallonta ya ce "To ya jikin naki?"

"Ba sauƙi" ta faɗa kai tsaye.

Usman ya ce "Ke fa daɗina da ke ƙarancin tunani, ba zaki godewa Allah ba ki ce da sauƙi, zaki ce ba sauƙi?"

Sai ta fara kuka ta ce "To ina sauƙi? Mama ta aske mini gashi, bana iya taka ƙafata ƙeyata ma ciwukan zafi suke yi mini, ga haƙarƙarina ciwo yake mini".

Bashir ya ce "Ya salam, kin gayawa likita? Ko kin faÉ—i da wurin ne?"

Ta ce "A'a wani sule ne ƙato ya dinga takani da ƙafarsa a wurin, tun daga nan yake mini ciwo"

Bashir ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam ba shi jaririn a mayar da shi nursery dan Allah, dan na ji yana atishawa ko sanyin nan yayi masa yawa".

Adam bai motsa ba, ya zubawa yaron ido yana jin wani irin tausayinsa da ƙaunsrsa na shiga ransa, ya karɓi jaririn ya bawa usman, usman ya fita mayar da shi ya rage daga takawa sai bashir da ruma a ɗakin.

Bashir ya kalli rumaisa ya ce "Rumaisa, kamar yadda dai na yi miki bayani da fari, Adam abokina ne, dukkaninmu jami'an tsaro ne na farin kaya, zai yi miki wasu tambayoyi ne dan Allah ki bamu haÉ—in kai"
Rumaisa ta kawar da kanta gefe, taƙi ko kallon in da Adam yake.

Adam ya numfasa ya ce "Ta yaya zaki tabattar mini wannan É—an na Aisha ne, ita ta haife shi"

Rumaisa jin tambayar ta yi kamar da rainin hankali a ciki "To ai ba sai ka tabattar ba, tun da dai ni na san É—anta ne, shiyasa na ce ba kaine babansa ba".

Bashir ya ce "A'a ruma yi haƙuri, kin san komai a hankali muke bi tun daga tushe, ki bamu amsa Please".

Ta É—aga filon da take kai, ta janyo É—ankwalin aisha, da yake a ninke, ta wurgawa adam cinyarsa "Ni banda wannan ban san me zance maka ba".

Ya saka hannu ya É—au É—an kwalin yana jujjuya shi, yana tuna wasu abubuwa da suka faru, tabbas É—an kwalin aisha ne.

Ya ɗaga kai ya kalli Ruma ya ce "Ina aisha take yanzu? Ya aka yi ki ka kuɓita da jaririn? Ita tana ina?"

Tayi masa banza, dan ranar ƙarshe da ya wanketa da ruwan kwata ne ya faɗo mata.

"Ruma amsa mana, ina aishan take? Kar ki damu, adam É—an sanda ne na farin kaya, ki yi masa bayanin komai"

Cikin tura baki ta ce "Saura na korayen kaya, ni ban san in da take ba"

"Kamar ya baki san in da take ba, ya ina magana kina shareni, ina Aisha take ina matata"

Ruma ta zaƙalƙale ta ce "Ka bita dajin ka ɗaukota, ka san kana sonta ka bari aka sace ta, ka ƙi zuwa ka fitar da ita, da ku ba gawara babu ba, ba da jami'an tsaro ake haɗa baki ba, haka aka ce da bakin su 'yan bindigar suka faɗa, in so kuke ku ganta sai ku tafi dajin ai, kuma wallahi idan kuma kun sani aka sace mu kuka ƙi taimaka mana a fito da mu, sai Allah ya saka mana, dukan da na sha a wurin mutanen nan ma ya isheni, ka zo zaka dameni"
Gaba É—aya ido suka zubawa rumaisa, tana kuka tana tsiwa.

Adam ya ce "Ni kike gayawa haka?"

"Tsoronka zan ji ne, wallahi bana tsoron kowa sai Allah subhanahu wata'ala, kuma wallahi tun da Allah ya sa na fito sai ka gane ba ka da wayo, sai na rama abun da kayi mini"

Kallon tuhuma Bashir ya shiga yi wa rumaisa da Adam, kenan sun san juna, akwai wani ɓoyayyen abu kenan a tsakaninsu.

Usman ne yayi sallama, ya tarar da rumaisa tana kuka, su kuma sun zuba mata ido.

Ya ce "Lafiya kuwa?"

"Ba wannan ne ya sakani a gaba yana zare mini ido ba, wai sai na gaya masa in da matarsa take, kuma ni ban san komai ba, likita ma fa ya ce kar a din ga takura mini amm yake hantarata"

Adam ya dafe goshinsa yana tunanin meya dawo da wannan jarababbyar yarinyar rayuwarsa, meyasa take liƙe da ƙaddararsa ne.
Shi kuwa bashir mamaki ne ya ishe shi, maganganun ta sun girmi shekrunta, ya kalli usman ya ce "Tambayoyi kawai muke mata, so muke mu yi ƙoƙarin ceto uwar yaron ita ma, ba wani abun aka yi mata ba".

Usman ya kalleta ya ce "Ke ki gaya musu abin da ki ka sani mana"

"Ni ban san komai ba"

"Kamar yaya, ya aka yi ki ka karɓo jariri ki ka gudo, ina babarsa take?"

"Tana can" tayi maganar tana share hawaye.

"Ke ya aka yi ki ka fito?"

Sake ɓare baki tayi tana kuka ta ce "Wallahi likita ya ce a daina takura mini, da me zan ji kai baka san wahalar da na sha ba, kun haɗu kuna hantarata"

Usman ya ce "Ke fa rumaisa makira ce wasu lokutan, uba waye ya hantarekin?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya kalli su Bashir ya ce "Tun da ba zata faɗa abubuwan da ake buƙata ba, ku ɗauke ɗanku ku tafi, kar ta sake ganinsa ma"

Ihu ta fara yi "Ni kar ku É—aukar mini É—ana".

"To ki yi musu bayanin abun da suka tambayeki*

"Ni ban san komai ba, ba 'yan sanda bane su, su je dajin mana su duba, ni nace ba abun da na sani, ni duk na manta wasu abubuwan ma".

Sarautar Allah bashir ya zubawa ido, bai taɓa zaton tana da baki haka ba, saboda yadda ya tsinto ta a galabaice.

Buɗe ƙofar ɗakin aka yi da ƙarfi, da duk sai da suka waiwaya domin ganin waye.

*₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam, jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*
Ayshercool

*KANWAR MAZA*

*20*

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
Chapter 89 · 0% Book details