← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 114

Sashe 54

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Aliyu ya ce "Magana ake miki, ihun me ki ke yi wa mutane?"
Ta É—an É—ago ta kalleshi, idanunta sun yi ja saboda gajiyar tafiya ga bacci da bai isheta ba ga kuma razana da ta yi.

"Mafarki na yi na tsorata"

"Kuma shine ba zaki yi addu'a ba,waye ma ya ce ki kwanta ki yi bacci da la'asar É—in nan?"

Gwaggo ta ce "Daina yi mata faɗa, wannan ba laifin kowa bane laifin babarku ne, bana tunanin ta na nemawa yarinyar nan maganin tsari, wataƙila aljanu ne ko kuma mayu suka tsorata ta, bana raba ɗaya biyu suke bibiyarta"

Ruma ta waro ido ta ce "Mayu kuma, ni fa wani mutum nake gani, ki daina tsorata ni"

"Ahaf sai kuma ki yi, ko dai maye ne, ko kuma aljani shi ya sa ki ke ganinsa, kurwarki ya ke son lashews" shiru ruma ta yi tana tunani a kan mafarkin da ta yi.

"Aikuwa sai dai ya ci kansa, ba dai ni ba"

"Tashi kiyi sallar magariba, a samo mini gaushi, na turara miki tsakin kuka da tazargade haɗi da turaren mayu, koma menene zai barki, ai kaf zuriyarmu kurwarmu tafi ƙarfin maye, aljan kuwa sai dai yayi ya barmu"

Aliyu ya girgiza kai mutanen karkara sun yarda da camfi, kuma ba ka isa ka sauya musu ra'ayinsu ba.

Takawa kuwa a hankali ya gama watstsakewa a kan gadon ba tare da ya motsa ba, a hankali ya furta "Wai me na yi miki ne haka ki ka sakani a gaba, wace irin jaraba ce wannan duk in da na motsa yarinya ɗaya nake gani, wannan idan har ba aljana ba wataƙila tana da wani mugun nufi a kaina, Allah ya shiga tsakanina da ke".

Rurin da wayarsa ke yi ne, ya sanya ya miƙa hannu a hankali ya janyo wayarsa ya duba, magariba ta riga ta yi, ya tarar da missed call rututu, wanda na Ammi duk ya fi yawa sai na Jabir.

Ammi ya fara kira, bugu É—aya ta É—aga cikin damuwa ta ce "Ina ka shiga ka ajiye wayarka nake ta nemanka ba ka É—agawa?"

Ya É—an gyara muryarsa ya ce "Ammi na ajiye duka wayoyin ne na fita, shi ya sa".

"Amma bai kamata ka ajiye wayoyi ka fita ba, ka saka hankalina ya É—aga sosai, amma ya na ji muryarka a haka, ba ka da lafiya ne?"

Yayi Murmushin ƙarfin hali ya ce "Haba Ammi, lafiyata ƙalau mura ce ta kamani, da na motsa sai ki ce bani da lafiya?"

"To ai dole sai ina yi ina bin diddigi, tun da ba cikakkiyar lafiya gareka ba, Ubangiji Allah ya tsare"

"Amin Ammi, na gode" ya katse wayarz ya tashi a hankali, ya ji jikin da sauƙi yanzu ba kamar ɗazu ba, ya lallaɓa ya shiga banɗaki yayi alwala, ya dawo ya yi salla.

***
Har zuwa dare, ruma ta ƙi sakin jikinta, kamar ba ita ce mai shegen surutun nan ba ta bi ta takure a wuri ɗaya kamar mara kuzari, gaba ɗaya ji take jikinta babu ƙwari. Yaya Aliyu ne suke ta hira da Gwaggo, da wasu daga cikin samarin gidan da suka shigo, duk yadda suka so su yi wa ruma wasa ta kulasu taƙi, ta koma gefe ta takure ta sha kunu.
Cikin damuwa Gwaggo ta ce "Rumaisatuna, wai menene gaba ɗaya kin ƙi sakin jikinki sai ka ce wata baƙuwa, me yake faruwa ne?"

Sheshsheƙa ruma ta fara sheshsheƙar kuka.

Gaba É—aya hankalinsu ya dawo kanta.

"Menene, me ki ke so?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Aliyu ya ce "Ba magana ake miki ba?"

"Gida" ta faÉ—a tana rushewa da kuka.

"To dan ubanki nan a titi kike ba a gida ba?" Aliyu yayi Maganar a hasale dan daga tahowarsu zuwa yanzu, ruma ta kai shi bango.

"Ni mama nake son gani, ka kira mini ita a waya". Gwaggo ta ce "To shikenan, yi shiru a kira miki ita. Ka ga illolin rashin zumunci ko? Yanzu da ana zuwa da ita, yaushe zata yi kuka dan tana cikinmu, ai duk abu ɗaya ne, amma kalli yanzu kallon baƙi take yi mana, yi maza ka kira mata ita ko ta daina kukan".

Takaici ya rufe Aliyu, kamar ya tashi ya naÉ—awa ruma duka, sai iskanci take kamar wadda aka kawo yaye, ya kira mama a wayarsa, ya jefawa ruma jikinta.

Mama na É—aga wayar ruma ta saka kuka, cikin kiÉ—ima mama ta ce "Lafiya kuwa ruma, menene?"

"Mama gida, ni ba zan iya bacci ba"

Mama ta ce "Haba ruma, ai sai ki É—aga mini hankali, ba kun sauka lafiya ba ko wani abun aka yi miki?"

"Ba ayi mini komai ba, ni kawai gida a kusa da ke zan kwana, kuma ina son in ga su Yasir da Abdallah da yaya usy".

"Ke dai ki na da shirme, to da aure aka yi miki fa, dangin mahaifinku ne fa nan ma gida ne ruma, duk abin da ki ke so za su yi miki, dan Allah ki daina É—aga musu hankali"

"To ni gaskiya ki ce a dawo da ni gida gobe, ni so nake na ganki dan Allah".

Mama ta ce "Ke ki mayar da hankalin ki, bana son sakarci fa, meye haka ne ruma, kawai daga zuwa baƙunta ki tayar musu da hankali, ko sai na haɗaki da babana?"

Da sauri ruma ta ce "A'a".

"To ki nutsu ki daina yi musu kuka"

Ruma tana share hawaye, wasu na gangarowa ta ce "To, na daina".

"Yauwwa, sannan ki yi fitsari kan ki kwanta, kar ki yi musu fitsarin kwance kin san dai kashedin da na yi miki ko?"

"Eh"

"To ki nutsu, sai da safe ki gaida gwaggon"

Usman ya karɓi wayar a hannun mama ya ce "Ke ruma, maman nono za ta baki da zaki din ga kuka ke mama, to idan ma shayar da ke take yau an yayeki"

Cikin shagwaɓa ta ce "Yaya ussy".

Ya amsa da"Na'am ƙanwar maza".

"Yaya usy ina son in ganka".

"To idan kin gannin lada za a baki? Zan gayawa Ali, idan kin samu miji a nan mun bar musu ke, su aurar da ke".

Aliyu ya fizge wayarsa ya ce "Ba katin banza ne da ni ba, kar Allah ya sa ki daina kukan, dama akwai karnuka da suke yawo a garin da daddare, idan baki nutsu ba, a ƙofar gida zaki kwana".

Gwaggo ce kawai ta din ga rarrashin ruma, ta gyara mata kan gadonta na ƙarfe ta kwanta.
Tsananin gajiyar mota, da baƙunta ya sanya bacci kwashe ruma.

Ɓangaren mama ma, hakan take, kewar ruma take sosai, tun yamma su Huzaifa suka fuskanci hakan suke tsokanar mama suna mata dariya, wai yau an ɗauke mama 'yar gudaliyar ifrituwarta, duk ta damu.

Mama ta din ga basarwa, irin ko a jikinta ɗin nan, amma tun da ta ji kukan ruma hankalinta ya ƙara tashi, cikin dare kuwa kasa bacci tayi, sai kallon wurin shimfiɗar ruma take yi. Sai yanzu take jin ina ma ba ta bayar da ruma an tafi da ita ba, dan gaba ɗaya hankalinta ya ƙi kwanciya.

***
Samha ce zaune a wani katafaren office, tare da Khalifa wakili, sai juyi yake a kan kujera yana kallonta yana mata murmushi, ita kuwa ta yi tsuru-tsuru kamar ɓera ya kwan a gadon kyanwa.

"Ki kwantar da hankalinki mana, babu wani abun damuwa a ciki fa"

"Khalifa, dan Allah kamar yadda muka yi yarjejeniya, tare da yin alƙawari a fari, dan Allah kar ka cutar da Adam, ni yanzu haka ma fa a tsorace nake"

Yayi wata makirar dariya ya ce "Lallai kin damu da shi da yawa, kar ki ji komai fa, kin fara naki ɓangaren, saura ɗaya ɓangaren suma za su yi nasu role ɗin "

"Amma haryanzu ba ka gaya mini su waye ɗaya ɓangaren ba, kuma aikin me zasu yi ba su, bayan da fari ce mini kai deal ɗin ni da kaine kawai".

"Saken da ki ka yi na rashin ba da amsa da wuri ya sanya third party joining deal É—in, kuma na ga za su taimaka sosai, shi ya sa na haÉ—aku ku duka a tafiyar, amma ki kwantar da hankalinki ba wata matsala"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, ni zan wuce sai ka ji ni".

Ya ce "To a sauka lafiya, zamu yi magana" bayan fitar Samha Khalifa yayi wata uwar dariya ya ce "Yaro man kaza, zaki gane baki da wayo"

Ɓangaren samha ma bayan fitarta jinjina kai ta yi ta ce "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, da na yi achieving abin da nake so, zan nuna maka wacece mace, zaka gane ba ka da wayo, kuma zan gano wanda ka sako a cikin sabgar nan bayan ni, zan baka mamaki".

****
Ko da garin Allah ya waye ma, aka yi alwala aka yi salla, ruma ta gaida wanda ta ga zata iya gaisarwa, ta koma ta yi shiru abun ta.

Lawisa ta dubi ruma ta ce "Sannu, kina buƙatar wani abun ne?"

Ruma a ranta ta ce "Wannan yarinyar kin isheni wlh" a zahiri kuwa ruma ta shareta, dan ita ji take kamar a kan wuta take, ba ta son zaman gidan nan.

Aka yi abin karin kumallo, kunun tsamiya da wainar gero, ga kunun na daka ne, sai ƙamshi yake, sai dai tun da Aliyu ya ga an kawo kunu, kuma kunun babu suga yake kallon ruma ya ga, wani action za ta yi, za ta sha ne ta yi kara ko halin za ta nuna.

Ta kalli kofin kunun, ta kalli Aliyu, amma ya kawar da kansa, ya na shan nasa.

Lawalli da yake yayan lawisa ya ce "Rumaisa ki sha kunun mana"

"Bana shan kunu" ta faÉ—a a raunace.

Ya ce "Au mutan birni ba cimarku ba ce ba, Gwaggo dafa mata shayi, bari na sayo madara a shago, a sayo miki burodi"
Dariya ruma ta yi ta ce "Meye kuma burodi, buredi ake cewa ai" karo na farko da tun da ta zo ta yi dariya, gaba É—aya hausar ta su wani iri take jin ta.

Shima ya yi dariyar ya ce "To shikenan buredi bakanuwa".

Ta ce "Banda buredi, shayin kawai zan ci wainar geron"
Chapter 54 · 0% Book details