Sashe 95
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nusaiba ta ɗan dafe goshi a rikice ta ce "Ammi kin hargitsani ban gane ba, ta yaya Anty Aisha da take Saudiyya za'a tsinto ɗan ta da ɗan kwalinta a Nigeria kuma a katsina, anya ba ƙarya yarinyar take yi ba, ko wani abun ake shiryawa ba"
Hawaye ya cika idon ammi, ta ɗauki wayarta, ta buɗe ta nemo hoton jaririn ta miƙa musu.
Cikin tsananin mamaki suke kallon hoton, babu in da yaron ya bar Adam saboda kamanni.
Iman ta ce "Ammi, ni fa haryanzu ban gane ba, a ssudiyyan ta haihu ko kuma yaushe ta dawo Nigeria har aka tsinci jaririnta, ita tana ina?"
Nan Ammi ta warware musu komai, kamar yadda takawa yayi mata bayani.
Nusaiba ta dafe kai ta fashe da kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ammi yanzu mai za'a cewa mai girma turaki, tayaya za'a warware wannan lamari? Anty Aisha a hannun 'yan bindiga tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani? Kuma Ammi ki ke ɓoyewa, idan zancen ya ɓullo ta wani wurin daban fa, kar ki manta ba'a san da cikin nan ba, kuma cewa aka yi zata ƙaro karatu, aka yi ta surutu a kai, tayaya za a dawo ace ba ƙaro karatu ta tafi ba, har ta je ta dawo an saceta ya haihu sai ɗa da ɗankwalinta da gwala-gwalanta, ana ma da tabbacin tana raye?"
Gaban Ammi ne ya sake faÉ—uwa, jin abubuwan da Nusaiba ta faÉ—a, take hawaye ya fara gangarowa daga cikin idon Ammi.
Iman ta ce "Anty Nusaiba, komai da muhallinsa, kan ƙalubalen ya zo, za a nema masa mafita, wannan maganganun naki zasu sake jefa ammi cikin damuwa"
Iman ta dubi Ammi a tsanake, ta fara goge mata hawayen fuskarta ta ce "Ammina, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, duk wani surutu da ƙazafi da zs ayi mana, ba zai kai wanda aka yi mana a baya ba, na san da tashin hankali, amma ammi ba zaki taɓa yanke hukuncin da zai cutar da wani ba balle mu. Ki na ji ammi ƙaddarar haihuwar yaron nan ce ya sanya anty aisha dawowa ƙasar nan, kuma suka ɓoye miki, duk da yadda suke biyayya ga umarninki, kar ki ɓata ranki ammi, kin san addu'a da ki ke yi mana ce ta zama katanga daga dukkanin sharri. In sha Allah mai girma turaki zai fuskance ki. An tambayi yarinyar ina Anty Aisha take?".
Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haryanzu fama ake ba ta yi magana ba tukuna".
"To shikenan, in sha Allah za ta yi magana, Sai a bi komai a hankali Allah ya sa tana lafiya, shi kuma jaririn Allah ya raya shi" iman ta sake É—aukar wayar Ammi, tana kallon hoton jaririn.
Nusaiba ta ce "Ba wai tayar muku da hankali zan yi ba, amma kar ku manta masarautar nan ba a iya samun bala'i ba, idan aka sako mutum a gaba da baki da surutu sai zaman garin nan ya nemi ya gagare shi".
Iman ta ce "Haka ne, amma in sha Allah babu abun da ya gagari Allah, Addu'a zamu duƙufa babu dare babu rana. Amma Ammi yaushe zamu je asibitin mu ga yaron muma?".
Ammi ta ce "Ba yanzu ba, ku É—an bani lokaci, bana son mutanen gidan nan su fuskanci wani abu tukuna"
Haka suka cigaba da tattaunawa, sai dai Nusaiba ta kasa magana domin kuwa ta riga ta gama karaya.
****
Ƙaton katafaren office ne, mai ɗauke da duk wani kayan alatu na jin daɗi da more rayuwa, Senator Usman wakili na zauna a ɗaya daga jerin kujerun office ɗin, sai kuma baƙonsa da yake zaune a kan kujerar da take fuskantar sa.
"Kana ɗaya daga cikin makusantan wancan yaron, da ya dage kai da fata sai ya ga bayana, sai dai kuma kwana biyu na ji shi shiru, duk na gama duk wani shiri da zan yi maganinsa, ko kuma akwai wani abu da yake ƙullawa da ban kai ga sani ba, kar yayi mini bazata".
"Ranka ya daɗe shi ɗain banza ja da ikon masu ƙasa? Ku ne fa ƙasar nan yadda ku ka dama haka ake sha, shi da duk masu goya masa bayan gayyar rashin sanin ciwon kai ce, dan tabbas manyan ƙasar nan akwai masu goya masa baya, wanda nake kyautata zaton 'yan adawarka ne".
Wakili yayi murmushi ya ce "Ba abokan adawata bane ba, domin abokan adawata muna aiki tare ne, mabiya kawai muke rainawa hankali".
"Haka ne Yallaɓai, amma a yanzu haka dai, bana tunanin wani shiri yake yi, dan a 'yan kwanakin nan akwai abun da ya ɗauke masa hankali, ko office bai fiye zuwa ba, ya ce bashi da lafiya, amma babu tabbas a maganar ta sa"
Wakili yayi murmushi ya ce "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shikenan ka cigaba da sanya mini ido a kan sa, da kawo mini rahoton duk abun da yake ciki, sannan zamu cigaba da shirye-shiryen tsayar da khalifa takarar gwamna, shi ma ba zamu baro ya ɓata masa suna ba".
"Amma ranka ya daÉ—e, na ji wancan satin majalisa ta naÉ—a kwamiti, domin bincikar gaskiyar abun da hukumar dss suke zarginka da shi, ya za'ayi da wannan"
Wata iri dariya wakili yayi ya ce "Duk saɓatta juyatta ne na siyasa, domin juya tunanin talaka baibai, ka san shi talakan Nigeria idan har zai ci ya ƙoshi, duk abun da zaka ɗora shi a kai zai bi a haka, babbar damuwar ɗan Nigeria ya ci ya ƙoshi ne, daga haka ba shi da wata damuwa da yadda abubuwa suke wakana, suma Dss ɗin muna nan zamu yi abun da ya dace a kan su"
Mutumin ya jinjina kai ya ce "Yanzu ranka ya daÉ—e wannan kwamitin da aka naÉ—a na binciken shi ma plan ne?"
Kamar mara imani haka wakili ya sake ƙyaƙyacewa da dariya ya ce "Ka je ka cigaba da yi mini aiki, nima zan yi amfani ƙarfin kujerata da faɗi a ji na ƙasar nan, na cika maka naka burin".
Risunawa mutumin ya yi yana jinjinawa wakili yana faÉ—in "Allah ya ida nufi, wakili na kowa"
Yayi maganar yana kamabama wakili, yayin da shi kuma yake ta ɓaɓɓaka dariya.
***
Kamar yadda Adam ya faÉ—a, da azahar bashir ya zo, zai kai rumaisa wurin X-ray, amma mai sunan baba ya ce bai yarda ba, su zasu kaita kar son banzan na su yayi yawa.
Bashir cikin mutuntawa ya ce "Haba Yallaɓai, rumaisa fa ta zama ƙanwarmu mu ma, ko ma in ce maka 'yar mu, duk abun da muka yi mata bamu faɗi ba, ka duba girman aikin alkhairin da ta yi mana, ai tafi ƙarfin abun da muke yi mata a wurin mu, dan Allah kar ka damu, wallahi ba son banza bane, idan dai har kuɗi ne, akwaisu adam ba shi da matsalar su, ku kwantar da hankalinku, dan Allah ka bari a kaita".
Mai sunan baba ya ce "Wanda ku ke yi mana, da wanda ku ka riga ku ka yi mana ma mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, amma muma a matsayin mu na ahalinta yakamata mu tagaza".
Bashir ya ɗan langaɓe kai ya ce "Zaku ja mini magana a wurin uban gidana, ga kuma uwa uba Ammi, ba za ta taɓa jin daɗi ba, sun ɗora ni a kan kula da komai, dan Allah ku yi haƙuri wallahi baku da wata damuwa a kan hakan, ɗaukar ɗawainiyarta ba yana nufin gazawarku bane ba, yana nufin nuna godiyarmu da jin daɗinmu ne a gareku, da yaba karamcinku, duk da mun san ba biyanku zamu yi ba".
Abubakar ne ya ce "Shikenan É—an uwa babu damuwa, Allah ya saka da alkhairi".
Bashir ya ce "Yauwa É—an uwa Amin, ku gama kintsawa sai a fito da ita ga mota can a waje" yana gama maganar ya fita.
Mai suanan baba ya ce "Malam wannan wane irin abu ne, shikenan sai mu zuba musu ido suna É—awainiya da mu, bana son nan gaba su yi amfani da wannan damar, su ce zasu juyamu ka san ba zai yiwu ba".
Abubakar ya ce "Haba dai, in sha Allah babu abun da zasu yi".
Sai da rumaisa ta tabattar da mama ta goya Mahmud, wanda take wa laƙabi da Sabir, ta ce saboda haƙurin yaron take kiransa da sabir, tun da suka baro daji bai fiye kuka ba, ba kamar ɗan wata malamarsu ba jarababbe mai kukan masifa.
Suka É—unguma suka tafi kai rumaisa x-ray, mama na ta fatan Ubangiji Allah ya sa lafiya babu wata matsala.
***
Adam ya idar da salla yana zaune a kan sallaya, yayi shiru ya rasa abun da yake yi masa daɗi, babu tsammani ya ji an turo ƙofar bedroom ɗin sa.
Jabir ya gani, ya shigo bakinsa É—auke da sallama.
Ya amsa masa a ciki, yau ya manta bai yi wa masu gadi warning na kar su bar kowa ya shigo ba, koma yayi musu ya san basu isa su hana Jabir shigowa wurinsa ba.
"Adam, wai ina ka shiga ne a kwanakin nan, na zo gidan nan ba adadi, bana samunka idan na je can gida ma baka nan, ina ka shiga haka?".
"Ina nan" ya faɗa a taƙaice.
"A'a, É—an tsaya meyake faruwa ne, ka wani rame, ga fuskarka duk ta kumbura har idonka, menene?"
Tashi Adam yayi ya ninke sallayar, ba tare da ya kula Jabir ba.
"Adam magana fa nake yi maka, ka wani shareni, ni ne fa nake yi maka magana, meya sameka haka?"
"Idan ka tashi tafiya, ka sanarwa masu gadi, kar wanda ya sake zuwa wurina" yayi maganar yana ƙoƙarin hawa gadonsa ya kwanta.
Ture shi jabir yayi ya tsaya a gabansa ya kalleshi ya ce "Kalleni, da Jabir kake magana, har akwai wani abu da kake ɓoye mini a rayuwa? Muna ɓoyewa juna wani abu ne?".
Adam ya dafe kansa ya zauna, yana ajiyar zuciya, ya dubi Jabir ya ce "J, gaya maka matsalata ba shi ne maganinta ba, ka yi mini addu'a kawai".
"Mu kan tattauna abubuwan da suke damunmu a tsakanin mu, ko da bamu da mafita, sai dai hakan yana ƙara mana yarda da juna da jin matsalar ɗayanmu ta dukkaninmu ne, dan haka babu buƙatar ɓoye mini komai".