← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 114

Sashe 19

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ya cika babar su Habiba, ta riƙe haɓa ta ce "Habiba, wato cigaba da shiga sabgar yarinyar nan ki ka yi ko?"

Habiba ta girgiza kai ta ce "Wallahi Ummanmu ba kulata nake yi ba, na daÉ—e ma bamu haÉ—u ba".

Ruma ta miƙowa Habiba leda ta ce "Kawo miki na yi, ki zo ki karɓa ki gani"
Babu musu ta ƙarasa ta karɓi ledar, taga ɗinkakkiyar atamfa ga abin hannu da ribbon, sai kuma ƙullin nama.

Habiba ta ce "Ruma wannan na waye?"

"Naki ne, in gaya miki, kayan salla na  kala goma sha biyu da hijjabai, har da abin hannu da sarƙa, shine na ce bari na kawo miki ɗaya, ki saka mu je yawon salla".

Babar su Habiba ta ce "Ba ta so ba zata karɓa ba, bana son shishshigi, ba ta kayanta ce muku aka yi tana buƙata? Ita ma tana da kayan salla"

Idon Habiba ya cika da hawaye ta ce "Wallahi Umma bani da kayan salla, ina son kayan dan Allah ki bar ni na saka".

Ruma ta ce "Dan Allah Umma ki bari ta saka, mun shirya ai mun dai na faÉ—a, dan Allah ki bari ta saka"

Umma ta kalli yadda Habiba ta rungume kaya tana kuka, wai tana so, haka ta ƙyaleta. Habiba ta shiga ɗaki ta saka kayan, aikuwa tamkar dan ita aka ɗinka su suka yi mata kyau.
Sani ya din ga ce wa habiba mara zuciya.

Abin ka da ƙuruciya, tuni habiba ta shirya a cikin kayan, duk da babar Habiba na jin haushin ruma, hakan bai hanata rawar jiki wurin raba naman kazar da ruma ta kawo ba, fan kuwa an daɗe ba a haɗu ba.
Daga haka suka fita nasu yawo.

Tamkar awakai haka suka dinga yawo, kusfa kusfa gidajen ƙawayensu, wasu a haɗu a rabu da su ƙalau, wasu kuma a ƙare da faɗa. Ruma ba ta tashi tuna kashedin mama ba, sai bayan azahar tana ta gararanbarta a gari.

A suwkane ta nufo gida, tana ta tunanin yadda za ta kare kanta a wurin mama, dan ta san zuwa yanzu ana can ana nemanta kamar kuÉ—in guziri.

Yaya Usman ta hango a tsaye a jikin wata mota, ya sha kwalliya, shi da abokansa, da alama fita za su yi.
Da gudu ta ƙarasa in da yake tsaye ta ce "Yaya ussy, me ka ke yi a nan?"

"Ban sani ba, wuce ki tafi gida, ki kai aiken da aka yi miki" abin da ya faÉ—a ne ya sanya ta fuskanci kamar mama ba ta neme ta ba, dan haka ta ce "Dan Allah ina zaka?".

"Zamu É—an fita chilling ne"

"Meye chilling kuma?"

Ya haÉ—e rai ya ce "Cewa na yi fa ki tafi gida ko?"

"Dan Allah ka yi haƙuri, zan bika dan Allah"

"Ke wai ni sa'an wasanki ne? Ba zaki wuce ki tafi gida ba?"

Ta sake marairaice wa ta ce "Dan Allah Yaya"

Riƙe rigarsa tayi tana kallonsa kamar za ta yi kuka. Tunawa ya yi da haushin ƙin tafiya da ita zai iya sanyawa ta tona masa asiri.

Yayi ƙasa da murya ya ce "To ki je ki tambayo mama, idan ta yarda sai mu tafi"

"Wallahi na san idan na tafi, tafiya zaka yi"

"Shegiya sai ka ce mayya, idan na tafi da ke a ina zan saka ki motar ba space" yayi maganar a ƙule.

"Sai na zauna a cinyarka" duk yadda ya so ya yakice ruma, taƙi ta nace, gashi ya san zai sha kunya, idan har ruma ta tona masa asirin yana waya da budurwa, dan ya san sai dai ya kasheta bayan ta faɗa zare idonsa ba zai hanata faɗar abin da ta yi niyya ba.

Haka ya sakata a motar, dama ta abokinsu ce, ita kaÉ—ai a cikin maza, sai zaginta yake, amma ko a jikinta, ya sakata a gefensa.

Abokansa sai dariya suke masa, suna "Ka ga Ƙanwar maza, suke mulkin amma dole a biki ko ba a so" ba wanda ta kula a cikinsu suka tafi.

Wurin shaƙatawa suka je, duk abin da suka ci sai da suka sayawa ruma ita ma ta ci, da ta ji ta ƙoshi ta kalli Usman ta ce "Yaya ussy, a samo leda a ɗaure mini sauran na tafi da shi gida"

"Saboda kowa ma bashi da hankali kamar ke? Wallahi baki isa ba" ba dan ya ji daÉ—in fitar ba, ya azalzali abokansa suka koma gida, saboda yadda ruman ke ta zubar masa da mutunci a idon abokansa.

Ko da suka je gida, mama a kiÉ—ime take, tun sha biyu ake nemanta ba a ganta ba.

Bin su da kallo mama ta yi, ta dubi Usman ta ce "A ina ka ganota?"

"Nima a hanya na ganta bayan la'asar, zamu fita da abokaina, ta nace sai ta bini, na kira Aliyu a waya na gaya masa muka tafi da ita".

"Ku ka je ina?"

"Wurin wani cin abinci ne, ni da su Isma'il ne"

"Kuma ita kaÉ—ai a cikin maza Usman, ka san tun yaushe yarinyar nan ba ta gidan nan, ka ga tashin hankalin da na shiga kuwa? Wallahi yau sai kin ci ubanki"
Abdallah ya ce "Wallahi mama ko ba ki daketa ba, sai na zaneta yau, ki yi mata bugun shekararriyar dawa, yarinyar nan ta ci a bata gado a Asibitin mahaukata".
Mama a tsananin fusace ta janyo ruma, ta din ga turjewa tana ihu, mama ta zaro bulugari ta dinga bugunta da shi tana kurma ihu tana neman taimako.

Mama ba ta saba tarbiyya da duka ba, amma idan ta kai bango jikin mutum yana gaya masa, sai da Usman ya ƙwaci ruma da ƙyar a hannun mama.

Tun daga ranar, mama ta ce ba zata bata sauran kayan sallar baz gashi an aiko mata da kayan salla daga can garin su, ga dangin mahaifin su ma, sun É—inko mata kaya, sun aiko mata da su, duk mama ta ce ba zata sake sakawa ba ta gama kwalliyar salla.
Washegari ta na ji ta na gani mama ta shirya, ta tafi cikin gari, ta bar ruma a gida.

Gidan duk ya yi mata babu daÉ—i, sai faÉ—ace-faÉ—ace take da su Yasir.
Suka gama suka fice suka bar ta a gidan. Ta ji babu daÉ—i rashin tafiya da ita da mama ba ta yi ba, gaji da zama ta tashi tana neman abun yi.
Ɗakin 'yan mazan ta shiga, ta fara gyara musu ta ci karo da shaddar yaya Umar ya saƙaleta.
Wani tunani ta yi, ta kwaso shaddar ta fito da ita tsakar gida. Ta zuba ruwa a bokiti ta tuttula omo ta zunduma shaddar nan a ciki, ta koma ta cigaba aikin gyaran É—akin.
A ƙalla shaddar nan ta kai awa biyu a ruwa, ruma ta fito ta jagwalgwala ta shanya. Ai kuwa shaddar nan gaba ɗaya ta daina wannan shining ɗin da take yi saboda azabar omo.

Aka jima, ya haÉ—a wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.

Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta duƙufa tana guga.
Ya tsaya yana ƙoƙarin gane me take gogewa.

"Wai meye wannan ki ke gogewa haka?"

Ta ɗago ta kalleshi ta ce "Kayan yaya Umar ne, na ga ya saƙale su a ɗaki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa".

Abdallah ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?"

"To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?"

"Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?" Ai suna cikin maganar ruma ta ƙone gaban rigar.

Dafe kai ta yi ta ce "Innalillahi, na shiga uku, Abdallah ya zan yi na ƙona masa shadda?"

Abdallah ya ce "Maganinki shegen karambani, kya san mai zaki gaya masa"

Hannu ruma ta É—ora a ka ta dinga kuka, dan ta san yau kashinta ya bushe, sai yadda Allah ya yi da ita.

Haka mama ta dawo ta tarar da ita, tana ta uban kuka, Abdallah ya gaya mata abin da ta aikata.

Cikin kuka ruma ta ce "Dan Allah mama ki bashi haƙuri, yau na san na mutu wallahi, dan Allah mama kar ki bari ya dakeni ko ya saka ni punishing".

"Ba ruwana, ai nima ba jin maganata ki ke yi ba".

Abu kamar wasa, har bayan la'asar ruma ba ta ci ko Abincin rana ba, sai kuka take yi.

Huzaifa ya ce "Ni ne mutum na farko da zai sanar da mai sunan Baba wannan taɓargaza da ki ka aikata masa"

Duk da mama a ƙule take da ita a kan laifin da ta yi mata jiya, amma hakan bai hanata saka ruma ta ci abinci ba, amma ruma taƙi ci sai aikin kuka. Ita kanta mama na tausayawa ruma hukuncin da zata fuskanta a wurin Umar idan ya dawo ya tarar da ɓarna da ta aikata masa, sai dai ita ta janyo kanta, rashin jin ta ya yi yawa.

Mai sunan Baba bai dawo ba sai bayan sallar magariba, tun da ya shigo ta sake takurewa tana uban kuka.
Ya dube ta, cikin kakkausar muryarsa ya ce "Kukan me ki ke yi?"

Huzaifa ya gyara zama, ya wassafa masa ɓarnar da ta aikata.
Duk da babu isasshen haske a tsakar gidan, ta tsorata da kallon da ya yi mata.

"Dan Allah yaya ka yi haƙuri, ba a son raina na aikata hakan ba, wallahi kawai niyyata na baka mamaki, na wanke maka na goge maka ban san haka abin zai zama ba"

Kalmar ta bashi mamaki sai da ta saka Aliyu dariya, ya ce "Lallai kin bashi mamaki kam"

Yadda ta firgice ne, ya sanya Yasir ya ce "Dan Allah yaya ka yi haƙuri, kuskure ne, tun da tsautsayin nan ya faru ba ta ci Abinci ba"

"Zaka É—au hukuncin da zan yi mata kenan?" Yayi maganar ba tare da ya kalli Yasir ba.

Yasir ya ce "Eh ni ka hukunta ni a madadinta, a tsorace take"

A É—an tsawace ya ce "Tashi ki É—auko mini kayan na gani"

Sumi-sumi ta tashi ta je ta ɗauko kayan, ta miƙa masa.
Ya karɓa ya duba, gaba ɗaya kayan sun tashi daga aiki, jikinta sai rawa yake yi.

"Tun da ki ke na taɓa saka ki wanki?" Ta girgiza kai.
Chapter 19 · 0% Book details