← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 114

Sashe 101

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba mai sunan baba, ya za ayi a ƙwace mini yarona, dama abun da aka shirya kenan? Mama ki saka baki" ta dubi Ammi ta ce "Dan Allah ku bani yarona, na sha wahala kan mu tsira tare, idan aka ƙwace mini shi, mutuwa zan yi, wallahi ina son sa sosai, ɗan uwanmu yaya bashir, dan Allah ka karɓo mini ɗana"
Gaba É—aya sai tausayin rumaisa ya kama su. Ammi ta ce "Kina ji ruma, ki kwantar da hankalinki, babu mai rabaki da yaronki, zamu je a kai shi cikin dangi ne, kuma in sha Allah za a din ga kawo miki shi ki ganshi".

Rumaisa ta fashe da kuka ta ce "Da na san haka ne, gara na zauna mu mutu a dajin, da da wannan mutumin ya ce in tafi ba zan tafi ba, gara a harbeni, kwanana biyu ba ma bacci ni da sabir, saboda sanyi yana kuka, kwanana uku ina bulayin hanyar da zamu dawo, kuma a ƙwace mini shi bayan mun sha da ƙyar, ba anty aisha ba sabir ɗina. Dan an ga ni yarinya ce za a ƙwace mini ɗa" Mai saunan baba ya danƙi hannunta zai yi waje da ita, tana kuka tana miƙa hannu tana "Dan Allah ku bani sabir ɗina" tun da ruma ta fara kukan nan tana zuba, ko ɗaga kai Adam bai yi ba ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Kuka sosai rumaisa take yi, tamkar an ce mata mama ta mutu, bashir ya rakosu yana ƙoƙarin rarrashinta, amma mai sunan baba ya ce ya rabu da ita, ya buɗe mota ya sakata, amma sai miƙa hannu take taka kuka.

"Ki rufewa mutane baki, idan an baki É—an ya zaki yi da shi, ke wace irin yarinya ce da ba a isa a gaya miki, ko ki rufe mini baki, ko na casaki a wurin nan" mai sunan baba yayi mata wata irin tsawa mai razanarwa.

A gigice ta ƙanƙame mama tana ƙoƙarin haɗiye kukanta, amma ta kusa ƙwarewa saboda kuka, ga hawaye ga majina har da yawu, saboda kuka.

Ammi na tsaye tana hango rumaisa yadda ake fama da ita, wani irin tausayinta ya kamata. Allah kenan ya karɓi uwar yaron, kuma ya sanya soyayyarsa mai tsanani a wata zuciyar.

A hankali ta juya ta koma É—akin da adam yake, yana rungume da jaririnsa.

Ammi ya dube shi ta ce "To me ka yanke? A ganina mu bari nan da ko kwanaki biyu ne ka gama warwarewa".

Adam ya girgiza kai ya ce "Ammi, ba zan taɓa warkewa ba, barin lamarin ina sake jinkirta loka8, abubuwa caɓewa za su cigaba da yi, daga nan gidan turaki zan wuce, zan je na sanar masa da laifina gaba ɗaya duk hukuncin da ya yanke a kaina shikenan".

Cikin damuwa Ammi ta ce "Kana ganin hakan shine mafita?".

"Ammi dole ita kaɗai ce mafita, na yi zaton aisha tana raye ne dama, shi ya sanya nake ta jinkirtawa, amma na yadda ta rasu yanzu, yanzu zan fara fuskantar mai girma turaki, daga baya kuma sai na fuskance ƙalubale na gaba".

Ammi ta ɗan yi shiru yana kallon ƙasa, daga bisani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shin, Ubangiji Allah ya yi mana jagora baki ɗaya "

Ya amsa da amin.
Bashir suka shigo tare da likita, likitan ya dubi adam da yake rungume da jariri ya ce "Allah sarki rumaisa, gaskiya ta shaƙu da yaron nan, ba ka kyauya ba da ka ƙwace mata ɗa" Adam ya sunkuyar da kai ba tare da ya iya yin magana ba.

"To Yanzu me yake damunka, zan rubuta maka teses na yi reviewing file É—in ka, na ga vitals É—in ka duk normal".

"Sallama nake so" ya faɗa a taƙaice.

"Meyasa zamu sallameka? Dole mu riƙe ka zuwa gobe in Allah ya kaimu mu ga abun da hali zai yi".

"Ba zaku hana Allah zartar da hukuncin sa ba, ku yi haƙuri tafiya zan yi " duk yadda likitan nan ya so lallaɓa adam ya ɗa zauna, amma yaƙi ammi ta ce ya basu sallama kawai, suna da issue a gida.

Haka kan likitan ya rubutawa adam sallama, da yayi tunanin ya kira jabir su tafi tare, sai ya ga babu wani amfani ma da jabir É—in zai yi masa a halin yanzu, dan haka kawai ya share suka tafi.

Suna tafe a mota, yana kalon sabir da yake ta ƙamshin turare, yana wasa da hannunsa, har da farar hoda da kwalli mama ta shafa masa, ba ayi masa aski ba, dan haka suma ta cika masa kai, ga ta a cike baƙa siɗik, har ta ƙasan hularsa ta fito, ga gashin girarsa a hankali yana tofowa.
Ƙasan zuciyar Adam yana ta fargaba da tunanin, yadda zai fuskanci turaki.

Har gidan turaki bashir ya kai su, sai dai shi ya tsaya a mota, su kuma suka shiga.

Da fari ta ƙofar turakar turaki ta harabar gidan, Adam ya shawarci Ammi su shiga, amma sai suka tarar da ita a rufe, dan haka dole suka bi ta cikin gida.

Falon ba kowa sai hadimai, suna ganin Ammi tare da Adam, cikin rawar jiki suka gaishe su, aka tafi nema musu iso wurin matar gidan.

Ba su jima a zaune ba sai ga mama ta fito cikin taƙama, ta dubi Ammi ta yi murmushi ta ce "Giwa, yau ke ce a gidan namu?"

Ammi ta ce "Ni ce, kin san ɗaurowa take a ɗaure alƙali, ya gida ya iyali?"

"Alhamdilillah, takawa magajin takawa, dan kujerar galadima ta yi maka ƙanƙanta babbar kujera muke fata" tayi maganar tana kallon jaririn hannun Adam.

Ta sake cewa "Ina ku ka samo É—a?"

Adam ya ce "Dan Allah idan babu damuwa, muna neman iso wurin mai girma turaki idan yana nan"

Ta É—an jinjina kai ta ce "Yana nan, bari ayi masa magana".

Ƙanwar Samha ce ta fito sumayya, ta gaida Ammi tare da takawa, ammi tambayeta ina samha, ta ce mata ta je abuja.

Mama ta fito ta ce "Bisimillah, ku shigo"

Ammi ta tashi, tana gaba adam na bin ta a baya, suka shiga falon turaki.

Yana zaune a falonsa, gefensa ga Alqur'ani a ajiye, da alama karatu ya idar.

Ya kallesu yayi murmushi ya ce "Maraba da manyan baƙi".

Ammi ta risuna ta ce "Barkanmu da wannan lokaci"

"Barka dai, ya iyali ya kuma rayuwa"

Ammi ta amsa da Alhamdilillah, maimakon mama ta fita ta bar É—akin, sai ta nemi wuri ta zauna.

Turaki ya kalli Adam ya ce "Takawarka lafiya, ana lafiya?"
Adam ya jinjina kai kawai, amma bai yi magana ba.

Ammi ta gyara zaman ta ta ce "Allah ya baka nasara, wata muhimmiyar magana ce ke tafe da mu, amma kan in ce komai, zan fara da neman afuwa sannan a sassauta mana hukunci"

"Babu laifi, ku muke sauraro".

Adam ya tashi a hankali, ya tafi gaban turaki ya durƙusa, ya ɗora masa Mahmud a kan cinyarsa".

Turaki ya rungumi sabir ya ce "Masha Allah, ina na samu É—a, É—an kyakykyawa Masha Allah?".

"ÆŠan wurin aisha ne" takawa ya faÉ—a jiki a sanyaye.

Turaki ya faÉ—aÉ—a fara'arsa ya ce "Ikon Allah, uwata yaushe ta haihu?, yaushe rabona da ita?"

"Allah ya baka yawan rai, haƙiƙa ni mai laifi ne, kuma a shirye nake da karɓar hukuncin da duk ka zartar a kaina. Wannan jaririn ɗan wurin aisha ne matata, kamar yadda aka kai ruwa rana da surutu a kan karatu da nace zata tafi. Duk ba wannan ba ma, maganar da nake maka, yanzu haka fulani ba ta duniya, ya rasu" Adam yayi maganar kansa a ƙasa hawaye na gangaro masa.

Ayshercool.

paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*

Haka suka cigaba da ƙulla mugunta kala-kala suna dariya.

Wunin yau Samha ba ta bi ta kan wayoyinta ba, sai yanzu ta nutsu, ta É—au wayoyinta ta kunna, ta ajiye su a kan gado, ta shiga wanka. Daga shigarta wanka zuwa fitowar ta missed calls sun fi goma sha.

Mamaki ne ya kamata, tana shirin duba missed calls ɗin, kiran Fauziyya ya shigo wayarta. Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce "Wai lafiya ake yi mini wannan kiran kamar mara gaskiya?".

Fauziyya ta ce "Ke dalla can, idan ma wani rabon ne har ya wuce ki baki É—aga waya ba, kawai kin wani kashe wayoyi".

"Ke karki É—aga mini hankali, hutu na zo yi dan me za a dameni? Ina jin ki"

Fauziyya ta ce "To, ai ni zancen ne ma ban san ta ina zan yi miki shi ba, abun farinciki zan ce miki, ko kuma tashin hankali da jimami, ko kuma abun É—aure kai?"

Samha ta É—an juya idonta ta ce "Fauzi, zan kashe wayata fa".

"Katangar da ta daÉ—e da tsaye miki, ta hanaki cikar burinki ta rushe".

"Kamar yaya kenan?".

"Ƙanwarki ce ta mutu"

Miƙewa Samha ta yi, ji ta yi kamar ba ta ji dai-dai ba, wai ƙanwarta ta mutu.

"Ƙanwata wacce? Wace ƙanwar tawa?"

"Ahh, wacece ta sha gabanki ta hana cikar burinki na auren yayanmu, aisha ɗazu aka ce wai ta rasu a wurin haihuwa, a garin da ta je karatu, amma an dawo da jaririnta, amma dai kamar akwai wani abu da ake ɓoyewa ba a son a sani".

Wata iska samha ta fesar ta ce "I hope ba ƙarya ki ke yi mini ba?".

Samha ta ce "Ana ƙarya da mutuwa ne? Ki tambayi wanda ba sa yi miki ƙarya sai ki tabattar".

"Am sorry, ba haka nake nufi ba, zan kiraki" ta kashe wayar ta cillata kan gadonta, ta hau sintiri a É—akin.

To murna za ta yi ko kuwa jimami, wata zuciyar ta ce "Ke ina ki ka gata jimami, damar da ki ka daɗe ki na jira, Allah ya kawota a sama ki tsaya wani jimami? Yanzu hanya ta miƙe miki fetal, aiki kaɗan ya rage miki".

Wayarta ta rarumo, sai dai ta rasa wa za ta kira ma, jefar da wayar ta yi, ta janyo akwatinta ta hau shirya kayanta, ko ba ta samu jirgi ba a mota zata koma gida gobe.
Chapter 101 · 0% Book details