Sashe 108
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na ji, amma jeki yanzu, ki bari na yi tunanina" Samha ta tashi ta bar É—akin mama, tana ta nazari da zancen zuci a kan abun da maman ta gaya mata.
Nusaiba ce ke ta bawa iman labarin rumaisa, da abun da ya faru É—azu da suka zo, zasu je gidan turaki.
Iman ta ce "Allah sarki, na ji ina son ta tun ban ganta ba, ai mu duk mai son waninmu muna son shi".
Nusaiba ta ce "Ke kin ganta, wallahi yarinya ce sosai, dan ba ta kaimu ba ma ko kaÉ—an, na yi mamakin yadda ta iya tsira da sabir".
Iman ta ce "Ai babu mamaki a cikin lamarin Ubangiji, babu abun da bau iya ba".
"Gaskiya ne, amma wai ya maganar uncle J ne, kun kuma magana da shi?"
Haushi ne ya kama iman ta ce "Dan Allah ki rabu da ni da wani uncle J"
"Dole na yi miki maganarsa, ke ma kin san rasuwar nan ce ta hanashi cigaba da bibiyarki, ina son nema miki mafita ne, idan ya je ya biyo ta saman fa kamar yadda ya gaya miki?"
Iman ta É—an yi jimmm sannan ta ce "Bakomai, Allah ya fishi, mu bar maganar nan sai wani lokacin*.
Lura da yanayin yadda iman ba ta son zancen, ya sanya Nusaiba jan bakin ta ta tsuke.
Rumaisa kuwa bayan kayan takaicin da ta turawa su usman, suna tafe a mota tana yi musu waƙe-waƙe, tayi wannan waƙar ta saki ta kama wata, gashi galibin waƙoƙin na indiya take yi, sam ba ta san ma me suke faɗa ba, kawai dai tana yi ne, kuma cikin ikon Allah daga usman har takawa ba wanda ya tanka mata har suka ƙarasa gidan rumaisa.
Usman ya kalli Adam ya ce "Mun gode ƙwarai da gaske Allah ya saka da alkhairi".
Adam ya ce "Bakomai, ni ne da godiya ai".
"Hmm ai Yakamata in ƙara ma da baka haƙuri, a kan abun da rumaisa ta yi, ka yi haƙuri dan Allah" Adam yayi Murmushin gefen baki ya ce "Kar ka damu, akwai saƙonta a mota amma, bari na buɗe booth ɗin"
Ruma buÉ—e motar tayi, ta ruga da gudu cikin gida tana kwaÉ—a sallama.
Kaya ne fal a booth É—in Adam, da wanda ammi ta bawa rumaisa da wanda turaki ya bayar a bata.
Usman ya É—auka ya yi wa Adam godiya suka yi sallama ya ce a gaida mama.
Ko da ya shiga gidan, rumaisan ya tarar har ta tuɓe kayanta tayi ɗai-ɗai wai ta gaji.
"Dan ubanki ni bawanki ne? Da zaki bar ni da kwaso miki kaya dan baki da kunya?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ganin irin kallon da yake yi wa rumaisa ya sanya sanin cewa akwai abun da rumaisa ta yi.
"Usman, ya aka yi ne? Kun je É—in?"
"Eh mun je, amma ba ta sauya zani ba, ta yi iya shegen na ta da ta saba"
Mama ta kalli rumaisa ta sake kallon usman ta ce "me ta yi?"
Nan ya gaya mata iskancin da ta din ga yi, mama ta girgiza kai ta ce "Wai rumaisa me bawan Allah nan yayi miki da ki ke yi masa wannan rashin mutuncin? Duk jan kunnen da na yi miki ba ki ji ba kenan?"
"Mama na faÉ—a komai fa"
Usman ya ce "To amma meye na cewa sai mun fita, a matsayin sa na mijinta yafi kowa buƙatar sanin meyafaru da ita".
Mama ta ce "Meyasa baka kama mini ita ka zaneta ba".
Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Ai kin san wasu lokutan sa'a ce da ita, daga zuwanmu ta dinga zuba tana yi wa dattijon shishshigi tana ce masa baba, aikuwa ya dinga biye mata, saboda sakarci har da ci masa abinci a gabansa"
Huzaifa da yake banɗaki yana jin hirarsu, yana fitowa ya ce "Sai ka ce mayya daga zuwa baƙunta ki hau cin abinci"
Aikuwa ta ce "To zigazigi wutar maƙera, mai zuwa lahira da ƙoƙon dambu waya kasa da kai gwanin na iya".
"Kin rufe mini baki ko sai na taushe shegen bakin naki"
"Wallahi mama ni ban ci abinci ba, wannan abun na kayan gara mai kamar kashin nan da suga shi kawai na ci".
A fusace mama ta ce "Ni rufe mini baki, bera kawai" haka ta koma ta tura baki tare da jin haushin yadda kowa yake caccakarta.
Adam sai da ya fara biyawa yayi sallar la'asar, yana komawa mota ya tarar da missed calls É—in Bashir.
Bin kiran yayi, bayan bashir ya É—aga sun gaisa ya ce masa akwai issue, su haÉ—u a wani wurin cin abinci bayan sallar isha'i.
Adam ya amsa masa, ya yanke shawarar fara zuwa gida, kan lokacin sallar isha'i sai su haÉ—u da Bashir.
Ko da ya je gida, Ammi ta din ga tambayarsa yaya suka yi, da fari basarwa yayi, da ammi ta matsa ya gaya mata cewar rumaisa ba ta yi magana a gabansa ba sai da ya fita.
Ammi ta yi shiru ta ce "Wai ni anya Adam babu wani abu a tsakaninka sa yarinyar nan Æ´ar tsamar da ku ke ta yi yawa, ta rainaka da yawa".
Ya girgiza kai ya ce "Ni ban santa ba sai a dalilin abun nan da ya faru, dan haka ni babu komai a tsakanina da ita"
"To, amma ina kyautata zaton akwai wani abu mai muhimmanci a bakinta, tun da taƙi faɗa a gabanka".
"Haka nake tunani nima, amma zan koma wurin turaki, sai mu yi magana".
"To shikenan, Allah ya yi jagora"
Ya amsa da amin.
Kamar yadda suka shirya, suka haÉ—u da Bashir a wurin cin abinci, ya tambayi adam mai za a kawo masa ya ce ba ya jin yunwa.
Bashir ya ce "A'a ba zai yiwu ba, sai ka ci abinci ko na koma da labarin da na zo da shi".
Da ƙyar adam ya yarda a kawo masa chips, bashir ya din ga yi masa hira, tare da gaya masa ya kusa komawa abuja wurin aiki.
Adam dai bai iya tankawa ba, jira yake kawai ya ji me Bashir zai ce masa.
"Wai ni kuwa ya ake ciki da maganar binciken da ka ke yi ne, na mutanen nan mutane hukuma fa suke jira, su ji sakamakon binciken ku, gashi wa'adin da kwamitin da gwamnati ta kafa ya cika ya wuce, amma ba su ce komai ba, kaima kuma kun yi shiru.
Adam yayi ajiyar zuciya ya ce "Bashir, sawun giwa ya take na raƙumi ai, ƙasar da ba ta damu da halin da al'ummarta suke ciki ba, tayaya zan cigaba da wahalar da kaina, a hukumar tamu ma kana gani sun rabu biyu, wasu suna goyan bayanmu wasu ba sa yi, a ƙasa kuwa talakawa ne kawai suke supporting ɗinmu. Ni yanzu hankalina yafi karkata ga binciko wanda suke da hannu wurin sace matata, dan a jikina nake jin na jikina ne".
"Kenan kana nufin zaka fito ka cewa duniya sace matarka aka yi, bayan an gama jita-jitar a ƙasar waje ta zo haihuwa ta mutu?"
"Bashir dole hakan zan yi mana, ba zan bar mutuwar aisha ta tafi a banza ba, ko da haka yana nufin zubewar kimata ne a idon duniya".
Bashir ya jinjina kai, ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ya ɗan daddana sannan ya miƙawa adam.
Adam ya karɓa ya fara dubawa, shafin wata jarida mai suna ciki da gaskiya ya buɗe masa.
Yana shiga ya ci karo da hotonsa, tittle É—in labarin aka rubuta dara ta ci gida.
Shahararren jami'in tsaron nan na farin kaya, mai jagorantar wata tawaga da ta zama babbar barazana ga manya ɓarayin ƙasarmu, ko kuma dai ace, shugabannin da yake yi wa sharrin sata, wato Adam Sharif Galadima. Kwanaki kaɗan bayan kamala zaman makokin mutuwar mai ɗakinsa, An bankaɗo wani babban al'amari game da shi, in da lamarin mutuwar matarsa ya sha ban-ban da abun da aka sanar game da rasuwar ta ta, ashe ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da mai ɗakinsa, har ta haihu a hannunsu, daga ƙarshe ta rasa ranta.
A wata majiyar kuma, aka ce da sanya hannunsa a yin garkuwa da matar ta sa in da ya kasheta yayi tsafi da gangar jikinta, kwatsam wata yarinya ta zo da jariri a zuwan ɗan matarsa ne, duk dan a ɓatar da hankalin mutane, da tunaninsu daga kan zargin shi wannan zaƙaƙurin bawa da yake jin cewa ya fi kowa gaskiya da adalci, masu bibiyarmu ko menene ra'ayinku game da wannan labari?!
Hannun adam har rawa yake yi a lokacin da ya kammala karanta labarin, wani irin wahalallen gumi ya din ga tsatstsafo masa, ya aka yi maganar nan ta fita? Waye ya yi masa wannan yankan bayan?.
Jiki na rawa ya ajiye wayar, ya miƙe tsaye, jin kansa ya fara sarawa, yana neman rasa nustuwarsa, bashir ya tashi zai yi masa magana, amma tuni adam ya sulale ya bar wurin.
Kafin ya cimmasa, ya hau motarsa yayu mata key, ya fice daga restaurant É—in da gudu.
08081012143
*Paid book ne ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
Gudu yake sosai a kan titi, Bashir ya hau motarsa ya bi bayansa, amma ya kasa cimmasa.
Ko da Adam ya ƙarasa gida, wani irin horn ya din ga yi kamar tashin hankali. A gigice masu tsaron ƙofar suka buɗe masa gate ya shiga da motar, ko da ya fito ko rufeta bai yi ba ya wuce sashin Ammi.
A can cikin gidan kuwa, bayan sallar isha'i, wata hadima ta shiga ta sanar da ammi cewar mummy na son ganinta.
Mamaki ne ya cika ammi, meya kawo mummy a wannan lokacin? Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta tashi ta fita falonta, ta tarar da mummyn tare da autarta ruƙayya.
Ta kalli ammi ta yi murmushi ta ce "Barka da warhaka giwar mata".
"Barkanki dai, kuna lafiya?"
"Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?"
Ammi ta amsa da "Alhamdilillah"
"To Allah ya jiƙanta da rahama"
"Amin ya rabb"