← Book details Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 114

Sashe 83

Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

Bashir ya san iya tijara zai sha ta a wurin takawa, dan haka ya shiryawa karɓar da duk wani hukunci da zai yi masa, ya kwantar da murya ya ce "Tuba nake, ka bari zan zo in sameka, na gaya maka ina Asibiti ne".

"Kar ka sake ka zo in da nake, idan ka zo haÉ—uwarmu ba zata yi maka daÉ—i ba"

'shi wannan kowa ma yi wa masifa yake yi?' ta tambayi kanta, can kuma ta ce 'Ƙila ma ba gaske bane mafarkin da na saba nake yi'.

Maganar Bashir ce ta dawo da ita hayyacinta "Haryanzu ba ki gaya mini ko sunanki ba, mun kawo ki unconscious, ki gaya mini sunanki, ki bani lambar wayar wani a gidanku, na kirasu ga abinci nan na kawo miki, yan sanda suna jirana na je na kai report".

"Ina jaririna?" Shine abun da ya fito daga bakin rumaisa.

"Na gaya miki yana nursery, an saka mishi oxygen ana ƙoƙarin ceto ransa".

"Idan wani abu ya same shi ba zan yafe maka ba, kuma wallahi sai na saka yayyena maza sun zane ka" ta yi maganar tana hawaye.

Bashir ya sake nutsuwa, yayi murmushi ya ce "ba zata kai mu ga haka ba,  babu abun da zai same shi sai abun da Allah ya ƙaddara masa, trust me, yanzu bani lambar wayar".

Ta É—an rausayar da kai ta ce "Allah ya sa ba mafarki nake yi ba, ni na manta lambar kowa, bari na baka ta Yasir, yayana ne ta sa na tuna.

Ya ce "Ok, gaya mini" yayi maganar yana riƙe wayarsa.

Ta gaya masa lambar cif, yayi saving ya ce "Tashi ki ci abinci, yayata zata zo ta zauna da ke, kan 'yan gidanku su zo".

Ta girgiza masa kai ta ce "Ni ba zan ci komai ba, sai na ga mama".

Bashir ya ce "No, ba za ayi haka ba, ki daure ko kaÉ—an ne"

"Ni dai ka tashi ka kirawo mini ita kan na farka daga baccin da nake yi" tayi maganar tana kuka har da sheshsheƙa.

Ya ce "To shikenan, bari na je, yayar tawa zata zo, sunanta Asiya, za ta zauna da ke"

Ba ta ce masa komai ba ta cigaba da share hawayenta.

Mintuna talatin da fitarsa, sai ga yayarsa Asiya ta iso, ta tarar da rumaisa tana barcci, dan haka ta nemi wuri ta zauna tana jin tausayin yarinyar, mussaman yanayin da ta ganta a ciki.

***
Kasancewar yasir ya iya gyaran kayan Electronics sosai, ya sanya ya buÉ—e É—an case da yake gyare-gyaren sa, ko yanzu da yake ta aiki yana yi ne ba dan yana jin daÉ—in aikin ba, sai don rage kewa da kuma damuwa.

Wayarsa ce ta fara vibrating, yana ji yayi banza sia da ta kusa katsewa, sannan ya É—aga ya yi sallama.

"Wa'alaikum salam warahmatullah, ina magana da Yasir ne?"

Yasir ya ce "Eh ni ne".

"Yauwwa, sunana Bashir kibiya, ni jami'in tsaro ne dan Allah idan ba zaka damu ba, ina son haÉ—uwa da kai a babbar headquarter 'yan sanda ta bampai"

Waro ido Yasir yayi ya ce "Yallaɓai me na yi? Wallahi ni ban yi wani laifi ba"

"Na sani malam Yasir, ni yakamata na zo da kaina ma, amma wani abu ne ya riƙeni ka zo da gaggawa ka sameni"

Jiki a sanyaye Yasir ya kashe wayar,ya kwashe kayansa, yana tunanin wa zai jewa da wannan maganar, babu yadda za ayi a gayyaci mutum bamfai ace lafiya lau.
Ya tsaya a ƙofar gida ya kasa shiga gida, sai rarraba ido yake yi.

Abdallah ne ya fito daga cikin gidan, Yasir ya ce "Alhamdilillah, zo ka ji wani abu".

Abdallah ya ce "Ya aka yi?"

Kamar Yasir zai fashe da kuka ya ce "Wani ne ya kirani, wai na je bamfai yana jirana kuma ni wallahi tsoro nake ji"

Abdallah ya ƙare masa kallo sannan ya ce "Kai, ka gaya mini idan wani abun ka aikata, Kodayake da ruma tana nan sai in ce ko ita ake nema, amma kuma ks tabattar ba 'yan iskan gari bane ba, ko a cikin abokanka wani ke son raina maka hankali ba?"
Yasir ya ce "Bana tunanin hakan, mutumin muryarsa ba ta yi kama da haka ba".

Abdallah ya ce "Bani lambar" Yasir ya bashi lambar ya saka a wayarss ya kira, yana kira Bashir ya É—aga, suka gaisa Bashir ya ce "Bawan Allah, yayan yasir ne ni, ina son jin dalilin da ya sanya ake nemansa a bamfai?"

Bashir ya ce "Eh, abu ne mai muhimmanci, da laifi yayi gida zamu zo mu kama shi ai, ku hanzarta dan Allah"

Abdallah ya ce "To shikenan babu damuwa ".

Ya katse wayar ya kalli Yasir ya ce "Zancenka gaskiya ne, ka san wani abu? Kar mu gaya kowa, zo mu je mu ji koma menene, sa ji daga baya" Abdallah ya ƙwararawa Yasir gwiwa, suka kama hanya suka tafi.

***
Ammi ta fito babban falo, ta dubi É—aya daga cikin barorinta ta ce "Maza je ki korawo mini iman" ta amsa mata cikin girmamawa, ta tafi.

Bai fi mintuna bakwai ba, sai ga Iman "Ammi gani, Allah ya sa ba laifi na yi ba?".

"Ai laifin ki ka yi, na gaji da zaman ɗakin nan da ki ke yi, jikinki ai da sauƙi yanzu, ki shirya zamu je gidan Jamil, an ce matarsa tayi ɓari" ɗan ɓata fuska iman tayi kamar zata yi kuka.

"Menene ko ba zaki ba?" Ammi tayi maganar tana tsare iman da ido.

"A'a zan je, bana son na je na tarar da Anty samha ne" tayi maganar kamar ta rushe da ihu.

Ammi ta kalleta a tsanake ta ce "Meye tsakaninki da Samhan da ba kya son haÉ—uwa da ita?" Sai kuma ta sha jinin jikinta jin abun da ammin ta ce.

"Bakomai Ammi, bana son fita ne"

"Aikuwa sai kin fita, maza muje in shiryaki, kar ma ki ɓata mini lokaci" Nusaiba kuwa sai dariya take yi, ganin ammi ta saka iman a gaba wai ita zata shiryata. Hakan kuwa aka yi, Ammi na tsaye iman ta shirya cikin baƙar abaya, da ta karɓi kyakywar farar fatarta, sai ɗaukar ido take yi, ta ɗora mayafin a kan ta, sai dai kwantaccen gashinta sai da ya bayyana.
Tare suka fito da Ammi, tana janyo hannunta, ita kuma kamar ta fashe da kuka, sai tura baki take yi. Haka suka jera da Nusaiba da iman da ammi.
Nusaiba ta ce "Allah ammi kin shagwaɓa yarinyar nan da yawa, ji wata taɓara da take yi".

Ammi ta ce "Bar ni da ita, sai na zaneta tukuna" haka suka fito harabar gidan a tare.
Chapter 83 · 0% Book details