Sashe 24
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar mama za ta yi kuka ta ce "Ba wnai fitinar maraya, dama can haka ake fama da ita, a ina ta samu keken da ta hau ni da na aiketa wuri daban, kullum sai ruma ta sakani asarar kuɗi da yawon ban haƙuri, nan gaba idan ba ayi wasa ba, sai wasu sun kai ƙararmu ga hukuma"
"A'uzubil'ahi kina uwa ba zaki faɗi alkhairi a kan yarinyar ki ba, ƙuruciya ce, kowa da irin ta sa" mama ba ta kuma cewa komai ba, idan ta biyewa zuciya, za ta iya musayar yawu da Gwaggo, wanda ba za ta so hakan ba.
Huzaifa ya shigo a kumbure yana bala'i "Mama! Ina ruma take wallahi yau sai na tattakata, sai na ci mutuncinta"
Mama da take a ƙule ta kalle shi ta ce "A ina ka ganta?"
"Mama shagon aski fa ta bini, na koreta shi ne ta É—auke keke na ta gudu, ni sa'an wasanta ne ita duk wani halin zubar da mutunci ta iya"
Mama ta safe kai ta ce "A ina da ta samu keken kenan? Za ta gane ba ta da wayo da Baba zan haÉ—ata bari ta dawo"
"A'a ke wace irin uwa ce, wannan mugun É—an na ki, haka kawai ya kassarata a'a ban lamunta ba "
Huzaifa ya harari Gwaggo ya ce "Wallahi ko ba a gaya masa ba, da hannun nawa zan ci ubanta, sai na girgiza ƙashin haƙarƙarinta "
Har gefin magariba babu ruma babu alamarta, tun mama tana jurewa, har ta saka aje a nemo mata ruma.
Aliyu Allah ya bawa sa'a, ya ganota a wata tawagar 'yan d.j, ana biki an kunna d.j, ta shige tsakiyar manyan mata, ana rawar sabada, ta gantsare sai rawa take, tana wani juye-juye sai ka ce an saka mata batir, ga ta a shafe ba gaba ba baya ama sai karkaÉ—a jiki take.
Cikin 'ya'yan Mama, Aliyu Ustaz ne, ba shi da ra'ayin wannan abubuwan, amma yau a saboda ruma, sai gashi a tsakiyar mata, ya samu bayan ruma da take ta juyi, ya tsula mata tsumagiya.
A zafafe ta ƙandare ta juyo, a zaton ta yaron mai D.J ne ya daketa, dan dama yana ta korar yara daga cikin filin rawar taƙi tafiya. Ba kuma rawar kawai take yi ba, har da satar kuɗin liƙi tana sakawa a cikin hijjabinta, sai ta gantsare tana rawa idan aka liƙo sai ta wayance ta ɗauke kuɗin.
Cak ta tsaya tana kallon Aliyu, ta É—aga kai ta kalli yadda gari ya yi duhu.
"Sannu 'yar makaÉ—a, aike da aka yi miki kenan ko? Fita ki wuce mu tafi"
Kasa magana tayi, a take tayi saranda, da jin za ta iya É—aukar kowane hukunci, saboda ita kanta ta san ta tafka ta'asa.
Ta janyo keken Huzaifa, da Allah ya sa ba a sace ba, ta hau turawa, Aliyu ya haske keken, tayoyi duk sun sace, dan É—ayar ma fashewa ta yi, ga kaca ta zube keken duk wani gurin ya lotse, adon fitulun da ya yiwa keken kuwa, suma wasu duk sun fashe.
Yana tafe yana kallon ruma, yana tunanin anya ruma mutum ce, fitinarta ko su da suna kamarta ba su yi haka ba, su dai akwai dambe kamar zakaru, kamar su cinye juna, amma rashin ji a gida, rashin ji a unguwa rashin ji a makaranta wannan sai Ruma ƘANWAR MAZA.
A ƙofar gida suka tarar da Uamar, yana tsaye yana waya, tana ganinsa ta fara kuka, tana cewa "Kashina ya bushe"
Aliyu ya ingiza ƙeyarta zuwa cikin gidan, da sauri Huzaifa ya taso, dan ta kekenaa yake yi, sai dai yana kallon keken ya san ko a wurin 'yan gwan-gwan wannan keke ba zai daraja ba, kamar yayi shekara da shekaru.
A ka rasa wanda zai ce mata komai, duk suka zubo mata ido.
Mama ta ce "A ina ka ganota?"
"Ga ta nan ku tambayeta"
Cikin muryarsa mai razanata musamman idan ba ta da gaskiya ya ce "Daga ina ki ke?"
Jikinta ya hau rawa ta ce "Dan Allah mai sunan Baba......
"Daga ina ki ke fa kawai na ce?"
Gwaggo ta ce"Ya zaka razanata da wannan muryar ta ka, ka tambaye ta cikin nutsuwa mana"
Huzaifa ya daÉ—e bai ji abin da yake shirin sanya shi kuka ba irin yau, ya kasa ko tari tun bayan tozali da kekensa.
Rarraba ido kawai take tana kokowa da numfashi, ganin yadda kowa ita yake kallo yana jiran amsarta.
Wata irin gigitacciyar danƙa Uamar ya yiwa kunnenta, ta kurma ihu, ya janyota har tsakiyar tsakar gidan, ya dungurar da ita, ya naɗe hannun rigarsa cikin tsawa ya ce"Ina ki ka je da aka aike ki?"
Cikin kiɗima da razani, ruma ta wassafa komai, ba ta ɓoye ba ciki har da zuwa wurin aski da yadda ta ɗau keke tana tafe tana faɗuwa, duk ta gurje gwiwa, da yadda bayan ta dawo daga aike ta tsaya wurin 'yan bikin da ba ta san suwaye ba ma, tana rawa tana satar kuɗin liƙi.
Sai a lokacin ta faɗi har faɗa suka yi da yaron dj yana ce mata shegiya ɓarauniya.
"Yanzu ina kuɗin da ki ka ɗebo ɗin?" Yayi maganar yana miƙa mata hannu.
Aikuwa ta zura hannu a rigarta, sai ga kuɗi, a ƙalla idan aka ƙirga sun kai dubu uku da ɗoriya.
(SORRY FOR THE LATE UPDATE, AYYUKA SUN YI YAWA NE, INA GODIYA DA TARIN ADDUOI DA ƘAUNAR DA KU KE WA BOOK ƊIN ƘANWAR MAZA)
Ayshercool
08081012143
[13/07, 9:01 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
        Â
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
12
Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce "Sata ki ka koma yi kenan ko?"
Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.
"Ba zaki buÉ—e baki ki yi mini magana ba?"
"A'a Yaya wallahi ba sata nake yi ba"
"To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?" Ta girgiza masa kai.
Ya ce "Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki"
Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce "Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo"
Gwaggo ta ce "Ku dai din ga haƙuri yarinya ce, ƙuruciya ce kawai take damunta"
Huzaifa ya yi ƙwafa ya ce "Ba ƙuriciya da yarinta ba, Allah ya sa ɗanyar ƙwaƙwalwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali"
Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguÉ—awa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.
Daga shiga banɗaki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta ɓata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta ɗau hijjabi ta tayar da salla.
Ita kanta ba ta san adadin raka'ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ƙarshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu ɗaya nazari kawai take.
Haka ta idar ta saka addu'a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faÉ—a sannan take zaman yin addu'a.
Ganin taƙi sallame addu'a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu'a ta tashi.
Ya ce "Oya, kamun kunne"
Cikin marairaicewa ta ce "Dan girman Allah Yaya.....
"Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?"
Jiki a sanyaye, ta durƙusa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.
Gwaggo ta ce "Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?"
Ruma ta ce "A'a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi haƙuri"
Mai sunan Baba yayi shiru, ya ƙi kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce "Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?"
Mama ta ce "Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam" ƙarshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba ɗaya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi haƙuri ya ce in tashi"
"Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waÉ—anda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana"
"Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur'ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan"
Yasir ya ce "Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun"
Gwaggo ta ce"Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin ƙi, ni babu abin da ya ƙular da ni, irin wannan goho da ya saki kina 'ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin ƙi".
Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.
Cike da ƙuluwa Yaya Aliyu ya ce"Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba" haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka ƙasa-ƙasa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.