Sashe 81
Kanwar Maza Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adam yayi ajiyar zuciya ya ce "Bashir ne yake yi mini yawo da hankali, sonake mu haÉ—u ayi wadda za ayi, amma sai raina mini hankali yake, na ce zan bishi Abuja ya ce na jira yazo kan da kansa, kawai sai kuma ganin message É—in sa na gani, wai za shi katsina, uban me zai je yi a katsina?"
"To amma yanzu ina zaka je?".
"Zan je na yi aikina da kaina ne" ya bashi amsa yana kallon agogon hannunsa.
Jabir ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kayi aikinka ko ka ɓatawa kan ka lokaci, wata ƙila akwai dalilin da ya sanya yake yi maka yawo da hankali, ka yi haƙuri ka bi komai a hankali, ka bashi yau zuwa gobe in Allah ya kaimu mana".
Adam ya girgiza masa kai ya ce "No, ba zan iya ba" ya juya zai nufi mota. Jabir ya riƙo shi ya dube shi ya ce "Bashir amintaccen ka ne, bana tunanin zai yi wani abu da zai yi maka yawo da hankali, ko ya cutar da kai, Please ka bashi ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne" da ƙyar jabir ya lallaɓa takawa dan ba laifi Adam akwai baƙin taurin kai".
***
A hankali take motsawa, ta fara ƙoƙarin juyawa, dan gaba ɗaya a tunaninta bacci take yi, sai dai ta ji wani irin azabar raɗaɗi a ƙeyarta, zuwa kanta da wuyanta, a hankali ta tashi zaune tana waige-waige.
Jaririn yana nan in da ya faɗi, yana ta motsawa a hankali yana zura hannunsa a bakinsa, yana ta numfashi sama-sama. Rumaisa ta zuba masa ido hawaye na zuba daga idonta, haryanzu jikinsa da ƙazantar haihuwa, duk ya fita a hayyacinsa. Wani irin jiri take ji, ta kalli in da ta faɗi ta ga jini, na in da ta fasa ƙeya ta faɗi.
Ta kalli ƙugunta haryanzu tana ɗaure da ɗankwalin Anty Aisha da ta bata, ta ja jikinta zuwa kusa da jaririn, ta riƙe hannunsa tana kuka "Ka yi haƙuri yarona, na kasa baka kulawar da yakamata, kaga nima yarinya ce ban san me kake buƙata a matsayin ka na jariri na, na rasa yadda zan yi mu bar wurin nan, dan Allah kar ka mutu kamar yadda mamanka ta tafi ta barni" tayi maganar kamar tana yi da sa'anta.
A haka cike da tsananin muradin cigaba da rayuwa, ta sake ɗaukarsa ta miƙe cikin ƙarfin hali, ta cigaba da tafiya, sai dai ba ta je ko ina ba ta kasa, ta silale ta zauna a jikin wani dutse ta zubawa sarautar Allah ido.
Kamar a mafarki rumaisa ta ga wasu irin dandazon shanu sun cika wurin, ita dai ba ta san ta in da suka ɓullo ba, ta hangi mai kiwonsu, yana ta ratsawa ta cikinsu. A gefenta ta din ga ganin wata inuwa, ta ɗaga kai sai ta ga wata bafulatana, doguwa do jerin ƙorrai a kanta, ta kalli rumaisa ta ce "'yar nan dan Allah taimaka mini na sauke ƙorran nan".
Ruma ta harari matar ta kawar da kai, kamar ba ta ga a halin da take ciki ba, take cewa ta sauke mata wannan uban ƙwaryoyin, can matar ta kuma cewa "Rumaisa da ke fa nake" ruma ta kalli matar cikin mamaki za ta yi magana ta fasa, ta kwantar da yaron, ta miƙe ta kamawa matar suka sauke ƙorran.
Ta koma ta zauna ta na cigaba da kallon jaririnta, matar ta din ga auna nono, ba tare da kuma tankawa rumaisa ba, can rumaisa ta ce "Dan Allah baiwar Allah ki taimaka mini da ruwa da nono na bawa yaron nan, ni ko ba zaki bani ba, shi ki bashi dan Allah".
Matar ta yi murmushi ta ce "Ai na zata ba zaki kulani ba, na tashi na yi tafiyata".
Ta miƙawa rumaisa battar ruwa, ta karɓa ta ɗago jaririn za ta bashi, matar ta karɓe shi ta bashi ruwan, sannan ta buɗe wata ƙwarya ta tsiyayo madara fresh ba a daɗe da tasota ba, ta fara bashi, aikuwa duk da bashi da lafiya, haka ya din ga karɓa yana sha, kamar zai cinye da mazubin.
Rumaisa sai murmushi take, ganin ya samu ruwa da abun da zai ci.
Matar ta kalli ruma ta ce "Ba dan halinki ba bari na san miki ruwa ki sha, ruma manyan gari, ruma kaya da yani, gwagwarmaya na gaba ba ta zo ba kuma ba ta wuce ba".
"Wai ke a ina ki sanni?" Ruma ta tambayi matar.
Matar ta yi murmushi ta ce "Ke waye bai sanki ba, karɓi ruwan ki sha, kar kuma ki manta ki kula da amanar da aka baki, Allah ya taimake ki baki mini rashin kunya ba, Kodayake jikin ta ƙaura yayi la'asar, wallahi da a dajin nan zan barki, amma ki ka taimaka mini, sha ruwan na rage miki hanya " rumaisa ba ta gama gane me matar ke cewa ba, ta karɓi abun ruwa ta kafa kai, sai dai maƙwarwa biyu ruwan ya ƙare ba ta ƙoshi ba.
Lumshe ido rumaisa ta fara yi, tana jin yadda kanta yake ƙara nauyi, ta karɓi yaronta daga hannun matar ta rungume, sai sunkuyar da kai take, kamar ta yi shaye-shaye saboda ji take kamar zata fita daga hayyacinta.
"Ke!ke! Baiwar Allah me ki ke yi a gefen titi haka?" Rumaisa ji ta yi kamar ta farka daga bacci, ta buÉ—e idonta sosai, irin zaman da tayi ta rungume yaron a haka take, sai dai a wani wurin ta ganta daban, jeji ne wurin sai dai tana zaune a gefen titi, kwalta É—oÉ—ar.
"Me ki ke yi a nan, ina zaki je?"
Ta É—aga kai ta kalleshi amma ta ba ta kula shi ba.
"Ko dai mahaukaciya ce ne? Wannan yaron na waye, ni da na zaci tsohuwa ce ashe yarinya ce, daga ina ki ke É—an waye a hannunki?"
"ÆŠana ne" ta bashi amsa.
Mutumin ya ce "A'a ba dai É—anki ba, ina hijjabinki, ina ne gidanku?".
"Kai dan Allah ka ƙyaleni haba" tayi maganar tana neman wurin kwanciya.
"Karki kwanta da jaririn nan a wurin nan, ki gaya mini in da zaki in kai ki".
Ta kalleshi ta ce "Ka san É—orayi?".
"A'a wanne gari ne?"
"Tun da baka sani ba Shikenan, na gode sosai" gani yayi kamar maganar da rumaisa take yi, haukacewa ta yi ba a hayyacinta take ba. Wata danƙareriyar mota ce ta yi parking a wurin da mutumin yake tsaye a kan rumaisa, da tuni mutane suka fara taruwa a wurin.
"Bawan Allah lafiya, meyake faruwa ne?".
Ya kalli na cikin motar ya ce "Wallahi kaga yanzu nake dawowa, na biyo hanya ns ga wannan yarinyar da jariri, ta ma dai ƙi bari na ga yaron, amma kamar dai mahaukaciya ce".
"A'a dawanau ce ni ba mahaukaciya ba, kai haka ake tainako ƙishirwa nake ji, amma ko ruwa bai bani ba yake ce mini mahaukaciya".
Na cikin motar ya ɗauko ruwan roba, ya fito ya bawa rumaisa, ta karɓa ta taƙarƙare ta shanye shi a maƙwarwa uku tayi jifa da jarkar.
Ya kalli rumaisa a tsanake ya ce "Na ji kin ambaci dawanau, ke 'yar kano ce?"
"Eh, dawanau asibitin mahaukata ne, dan Allah idan ka san kano ka kaini, kar jaririna ya mutu, bashi da lafiya" tayi maganar cikin magiya.
Ya ce "Ok babu damuwa, amma Meyasa na ganki a haka? Ina hijjabinki kalleki futu-futu fa, ga raunuka a jikinki, kalli kanki yana zubar da jini, jikinki babu hijjabi, ƙafarki babu takalmi, dole ayi zaton ko baki da hankali".
"Kwana kusan sittin fa a dajin nan, saceni aka yi, dan Allah ka tashi ka mayar da ni gida" salallami mutanen wurin suka É—auka.
A take ya ciro id card É—in sa, ya nunawa mutanen, shi jami'in tsaro ne, dan haka ya ce zai tafi da rumaisa babban asibiti na cikin garin katsina.
Rumaisa ta ce ita fa ba ta so a kaita ko ina sai gida, ya fuskanci yarinyar kafaffiya ce, dan haka ya ƙyaleta ya ce ta taso sai ya ɗauki wakilcin mutum ɗaya su tafi, su tsaya su yi reporting wa police, su wuce da ita asibiti.
Sai dai duk yadda rumaisa ta so ta tashi ta kasa, saboda ji ta yi ƙaffuwanta kamar ba nata ba, ƙarshe sai ɗaukarta aka yi aka saka a motar suka tafi.
Sai dai fa fafur ta hana kowa jaririn nan, yana ƙanƙame a jikinta, jin abubuwan take kamar a mafarki, Allah ya kuɓutar da su, ta din ga jera hamdala ga Ubangiji.
Sai dai rumaisa na sanya ran an kama hanyar kano ne, ta gansu a asibiti, aka zo da wheel chair, aka ɗorata a kai, nurses zasu karɓi jariri ta ce ba ta san zance ba.
Emergency aka shiga da su, aka yi ta lallaɓa rumaisa ta bayar da jariri ta ƙi, ta ce idan aka matsa mata, ko da rarrafe sai ta gudu daga asibitin.
Kasancewar mutumin da ya tsinceta shi ma ba É—an gari bane ba, idanya barta babu wanda zai kula da ita, ya sanya a ka bawa rumaisa É—an taimakon gaggawa, ya É—au rumaisa tare da rakitar 'yan sanda biyu, suka taho kano.
Suna tafe a hanya rumaisa tana ta surutai, masu kama da na fita a hayyaci, ta ce wanna ta ce wancan, ita dai gata nan kamar mai barci kuma kamar zautacciya.
Ba su suka iso kano ba sai bayan tara na dare, suka biya suka kuma report ga police na kano, aka yi rubuce-rubuce, sannan suka wuce da rumaisa asibiti.
Suna zuwa aka karɓi su rumaisa, da tuni hankalinta baya jikinta, tun a hanya aka sai abin ci aka bata, amma taƙi ci, ba ta ma da nutsuwar da zata ci Abincin.
Aka zare jaririn hannunta, da a yanzu numfashi ma yake neman ya gagare shi, da yawa sai da wasu suka yi hawaye, ganin halin da jaririn ɗanyen haihuwa yake ciki, cibiyarsa ta yaƙune tayi baƙi, jikinsa duk ƙazanta, aka samo kaya aka saka masa aka wice da shi nursery domin bashi taimakon gaggawa.