← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 180

Sashe 83

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ni taran da aka ci Alhaji ne ma yafi
ona min rai wallahi, ga mari ga tsinka jaka, ki sake kiran wayarsa kiji ko zai shiga" Meemah tace "Baza fa a samesa a waya ba Momy, mu da ganin Abdallah sai ya cika burin dake ransa kema ai kin san halinsa, gwara ma ki saka ma ranki salama mu bi sa da addu'a kawai" Momy ta kalleta tace "Wato kin san inda yake kenan?" Meemah tace "Ke dai kawai ki bi sa da addu'a Allah ya basa nasaran abinda ya saka a gaba Momy, amma shegiyar yarinyar nan ai kamar ta shigo gidan nan ne babu me hana hakan, don baza mu yi biyu babu ba" Momy ta tabe baki tace "Har ga Allah ni so nayi kawai ya hakura da er matsiyatan nan Meemah, kada tsautsayi ma yasa a hada iri da ita mu shiga uku, hada iri da talaka ai ci baya ne Meemah, don ni har cikin raina naki jinin talaka wallahi balle in hada zuri'a da su" Meemah tace "To ai dama bama fatan a hada iri da ita Momy, personally bazan ma bar hakan ya faru ba trust me, kawai ta shigo gidan ta gane Allah daya ne, ke kuma ki fara masa fafutukar wani auren da wuri wuri" Momy dai tayi shiru, can ta tabe baki tace "Allah ya sa ya saurareni to" Meemah tace "Haba dai zai saurareki, da kaina zan masa magana, a samar masa yarinya dai dai class dinsa" Momy tace "To ai shikenan, yanxu tracing din matsiyaciyar yarinyar ya sa a masa kenan?" Meemah tace "Ko ma dai menene mu dai mu zuba ido mu bi sa da addu'a kawai Momy" Mikewa Momy tayi tace "Bari in je in lallaba babanku, na dade ban ga ransa ya baci irin haka ba, haba ai abun da bacin rai, wai ace talaka yayi nasara akan ka a kotu bayan kai ne me gaskiya ai abun da ciwo" Daga haka ta wuce sama, Meemah ta dau wayarta tayi dailing number da take samun Abdul da shi ta tashi ta shiga dakin dake parlon.

Da asuba ko sallah ba ayi Malam Ali ya fito da er jakar da yake tafiya da shi bayan ya mulke jikinsa da basilin saboda sanyin da ake, bin dakunan matan nasa yayi duk ya kwankwasa masu kofa, Mama Zubaida da Mama Shatu suka fito suna kallonsa da mamaki suka ce "Lafiya Malam?" Mama Zubaida tace "Ko tafiya kauyen ne ya taso?" Shi dai bai tanka su ba ya dinga goge takalminsa da yayi
ura, Umma ce karshen fitowa ita ma ta tsaya tana kallonsa ta kasa cewa komai don tasan manufarsa, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda hankalinta ya tashi, Nenne ce ta shigo gidan yafe da zaninta tana ganin Malam Ali tace "Yauwa ko sallah kar ka jira kayi idan kaje tashar kayi a can Ali, ga er soyayyiyar nama da gurasa na kullo maka ka ci a hanya" Mama Shatu tace "Tafiya zai yi ne Nenne?" Nenne tace "Babu ruwan ku, ku dai ku yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya" Malam Ali ya amshi kullin nama da gurasan da Nenne ke mika masa, yana kallon matan nasa yace "Toh sai Allah yayi min dawowa" Mama Shatu tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya tsare Malam" Mama Zubaida ma tace "Allah ya tsare duk da muna da hakkin ka sanar mana inda zaka je da asuban fari Malam" Nenne tace "Bazai sanar ba Zubaida, uban me sanin inda za shi zai kara maki?" Mama Zubaida ta juya ta koma daki, Mama Shatu ma ta tabe baki ta koma dakinta, Nenne ta kalli Umma tace "Wato ke ce isasshiyar da bazata yi masa Allah ya kiyaye ba ko Zahra'u" Shi dai Malam Ali tuni har ya fice daga gidan, Nenne na nuna Umma tace "Mugun abun ku zai kare maku da ke da er ki wallahi, babu wanda ya isa ya salwantar min da
a na lokacinsa bai yi ba" Daga haka ta bi bayan Malam Ali da sauri zata rakasa bakin titi ya samu adaidaita sahun da zai kai sa tasha.

That same day bayan an idar da sallahn asuba Jay ya shigo parlorn Mai martaba da sleepy face ta dalilin kiran da yayi masa, ganin irin zaman da Abba yayi kamar yana fadarsa ya gane serious issue Abban zai yi discussing da su kenan, ya kalli Ajay dake parlon zaune shi ma alamar kiran sa Abban yayi, Aunty ma na zaune parlon, Jay ya sauke kansa ya karasa kusa da Ajay ya zauna kasan lallausan carpet din parlon, dabi'ar Abba ne sai ya iya minti biyar zuwa goma kamar me nazari kafin ya fara magana in ya tara ku, Jay ya sunkuyar da kansa ya lumshe ido, Ajay ya
an kallesa sanin sai ya iya bacci a haka, ai ko yaga baccin yake, Ajay ya
an tunkudesa da elbow dinsa, Jay ya bude ido da sauri yana gyara zama, shi dai Abba kallonsu kawai yake, At last Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa yace "First of....
Chapter 83 · 0% Book details