← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 180

Sashe 138

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki san hanyar gidan ba, ko ni na kawo ki?" Ta daga kai ta kallesa ta ma rasa abinda zata ce, ya wani murtuke fuska yace "Ni ba Jay bane da kike ma iskanci iri iri kina controlling din sa" Juyawa tayi a hankali ta bar bakin kofar yayi banging kofarsa ya kulle, ya koma ya dau wayarsa har yayi dialing number Jay sai kuma ya katse kiran ya ja tsaki, Khaleesat na komawa dakin da take ta dau handbag dinta da wayarta sannan ta fita daga dakin, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs ta nufi kofar fita daga babban parlon sai taga kofar a kulle, duk kokarin da tayi na ganin ta bude kofar ta kasa budewa gashi bata ga makulli a jiki ba, ta fi minti biyu tsaye bakin kofar tana jin tana flow a hankali, ta juya ta kalli hanyar sama, komawa tayi tana tafiya kamar bata so ta nufi bangarensa, jingina tayi da bango kamar bazata kwankwasa kofar ba sai kuma dai tayi knocking din kamar tana tausayin kofar, Ajay da har ya kashe wutan dakinsa ya kalli kofar babu ko kiftawa, sai kuma ya gyara kwanciyarsa bai motsa daga inda yake kwance ba, Khaleesat ta fi minti biyar bakin kofar bata kuma fasa knocking din da take ba, cire Duvet din jikinsa yayi ya jefar gefe sannan ya sauka daga kan gadon fuska daure ya nufi kofar ya bude yana kallonta at the same time cutting her a serious warning yace "Ki ka sake knocking din min kofa zan maki walakanci wallahi, why are you such a nuisance?

Pls get out before i loose my temper" Khaleesat dake kallonsa ta wani hade rai tace "To ta window kake son in fita daga gidan bayan kofar parlon a kulle yake??" Yace "Ki bi ta roof ma ba window ba" Yana fadin haka zai kulle kofarsa tayi saurin shiga cikin dakin kamar zata fashe da kuka ta nufi tsakar dakin ta tsaya tace "Kasan dalilina na cewa zan tafi gida ne?

Kawai kayi ta ma mutum masifa baza ka tsaya kayi considering dinsa ba ka basa listening ears, kawai haka nan zan taso cikin daren nan in ce zan tafi gida?

Ni ban ce sai kai ka kaini ba ka zo kawai ka bude min kofa inyi tafiyata...." Magana take amma gaba daya hankalin Ajay na kan dakinsa da ta shiga kai tsaye, he look shock irin he didn't see that coming, he ignored her ailment that he understood immediately, ya
an yi calming din kansa yana kallonta yace "Saboda kin ga ranan ya shigo dake nayi persuading kaina ban yi reacting ba sai kika yi zaton public room ne wannan?

An gaya maki ko shi Jay din yana shigar min daki anyhow?

Baki da hankali ne or are you out of ur mind?

Come and get out before u push me to the wall, kuma kar ki kuskura ki taka min carpet dina da wannan kafafuwan naki, wannan filthy dakin da kika shiga kika kwanta duk
ura da datti common sense dinki bai gaya maki ki share dakin ki goge ba sannan kiyi changing bedsheet, sannan zaki shigo min da
i ki kakkabe min du
kuran da kika kwasa a jikinki ki cuceni, plss come and get out before i loose my temper...." A fusace ya kare maganar yana kara bude mata kofa da kyau ta yanda zata zo ta fita, Khaleesat ta wani ta
e baki tace "To ai sai kaje ka bude min kofar parlor" Tsawa yayi mata yace "Baza ki fice min daga daki ba?" Ta fashe da kuka ta nufi kofar tace "To kasan me yasa zan je gida ne, ko ba saboda urgent issue bane" Yace "Ke kika san urgent issue din, get out of my room" Ganin he is damn serious don gaba daya mood dinsa ya canza tun da ta shiga dakin yasa ta fita daga dakin tana kallonsa tace "Don Allah ka bude min kofar parlon before it's too late" Banging kofar dakinsa yayi ya kulle, Khaleesat ta dinga kallon kofar, after a minute sai gashi ya fito, ya saka takalmin da yake yawo da shi a gidan, ta bi sa da kallo sai kuma ta bi bayansa tana hararansa, downstairs ya sauka ya tafi ya bude mata kofar parlon, tana tafiya a hankali ta karasa bakin kofar sannan ta fita tana kallonsa, kulle kofar parlon yayi, Khaleesat taji wani sanyi don iya Hijab ne jikinta babu rigar sanyi, walking slowly ta fita daga compound din gidan gaba daya wani mugun sanyi ke shigarta, sai yanxu ta kara tabbatar da Ajay mugu ne kuma ba shi da conscience, ta ciro wayarta taga ko zata iya order din ride, tana ta tsaye a Neighborhood din bayan ta duba ride din, after almost 5 minutes taga hasken fitilar mota daga compound din gidan, dauke kai tayi har ya fito da motar, taga yayi parking inda take tsaye, ta wani kallesa, fuska daure yace "Do not waste my time Malama" Ta wani tura baki ta bude front seat, sai dai kuma tsoro take kar ta zauna ta
ata masa motar ta shiga uku, haka dai ta shiga sai bata sake jikinta gaba daya a zaune ba, tana shiga ya ja motarsa, har suka isa apartment dinta bai ce mata komai ba, bayan yayi parking murya can ciki tace "Nagode" Daga haka ta sauka daga motar ba tare da ta kallesa ba ta nufi kofar apartment dinta ta bude da makulli ta shiga ciki, bata kulle kofar ba ta tsaya jikin window ta
an bude labule kadan tana lekawa taga ko ya tafi, haska inda ta zauna taga yana yi da wayarsa, ta zaro ido ta juyo hijab dinta da sauri sai taga bata yi stain ba, ta sake kallonsa taga ya gama haske haskensa ya kashe fitilar wayan, ta ma san kilan ya gane me yasa tace zata dawo gida, turo baki tayi saboda kunyan da taji, tana ta tsaye jikin window har bayan minti biyar bata ga yayi Reverse ba, ita kuma so take taga tafiyarsa sannan ta kulle kofarta da makulli don saboda zuwan da yayi daxu ya bar mata kofa a bude Aymaan ya fado mata gida kamar barawo, bude motar taga yayi after almost 10 mins ya fito, sai da taga ya nufo kofar apartment din sannan ta ruga sama da sauri ta shige dakinta...

Ko da Khaleesat ta shiga bandaki taga hatta kayan jikinta ma bai yi stain ba, pad din da ta siyo tun daga Nigeria ta dauka a cikin akwatinta, bayan ta gama gyara jikinta ta fito ta canza kaya sannan ta saka rigar sanyinta ta kwanta, wajen karfe dayan dare Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa a firgice duk da bata dade tana baccin ba ta mike zaune zuciyarta na bugawa, mafarki tayi wai Aymaan ya zo yana ta bubbuga mata kofa, dama kuma har tayi bacci hankalinta na kan kofar parlor ko ya tafi ya kulle mata kofar ko a bude ya bar mata oho, a hankali ta sauka daga kan gadon ta bude dakinta ta fita corridor tana leka downstairs, kwance ta gansa kan kujera idonsa a lumshe ya maida wutan parlon zuwa dim light, a hankali ta sauka downstairs din yanda bazata yi making sound ba, after some seconds ta koma sama ta dauko masa duvet, tana dawowa parlon ya bude ido, ta koma baya tana kame kame tace "Duvet ne, naga akwai sanyi sosai yau...." Ya nuna kansa yace "I should use ur duvet?

Me?

Ke da kika iya shiga daki duk
ura da datti comfortably ki kwanta shi ne zaki kawo min duvet din ki i should use saboda nayi hauka, ai duk macen da zata iya zama comfortably cikin daki me datti da
ura without cleaning it, kuma ta dinga yawo a gida babu takalmi a kafarta to babu kalan kazantar da bazata aikata ba, shi yasa taku ta zo daya da Jay, bird of the same feathers, ba gwara in kwanta sanyi ya kasheni ba da inyi amfani da abinda ya fito daga dakin ki, kujeran nan ma don sabbin furnitures ne yasa na kwanta" Khaleesat ta wani kallesa, sai kuma ta juya ta koma sama da duvet din, kuma sabo ne ko amfani da shi bata ta
a ba a ledansa ma ta ciro yanxu, can kasan ranta ta dinga ce ma kanta Allah ya kara mata, tsaki ta ja bayan ta shiga daki ta kulle kofarta da makulli tayi kwanciyarta.

Washegari wajen karfe bakwai Khaleesat ta fito daga dakinta, bata gansa a parlon ba, hakan yasa ta sauka downstairs ta tafi kofar ta murda taji a kulle, ta leka garage taga babu motarsa, tabe baki tayi ta wuce kitchen don dama da yunwa ta kwana, sai wajen karfe goma ta gama duk abinda take ta bar gidan zuwa school, har suka gama lectures bata sake fuska ba ranan, tun Safiyyah na jan ta da magana har ta gaji ta kyaleta, bayan sun fito department Safiyyah na kallonta tace "Is there any problem Khaleesat?

Naga gaba daya yau mood dinki babu kyau" A takaice Khaleesat tace "Nothing" Safiyyah tace "Ke dai ki gaya min gaskiya, kila ma haushina kike ji ban sani ba ma" Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace "Saboda me bazan ji haushin ki ba Sophie?

Kawai kin ja
an iska mara kamun kai ya shigo rayuwata ina zaman zamana, you caused me all this wallahi" Safiyyah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Wai Aymaan?

Wallahi ban san
an iska bane Khaleesat, kin ji na rantse, na zata yana da kamun kai ne yanda nake ganinsa sumi sumi a department" Khaleesat tace "To jiya wajen karfe shidda na yamma sai gashi a apartment dina unfortunately na bar kofa a bude kawai ya fado min cikin parlor kansa tsaye" Bude baki Safiyyah tayi tana kallon Khaleesat ko kiftawa babu with shock, a hankali tace "Apartment din ki kuma Khaleesat?
Chapter 138 · 0% Book details