← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 180

Sashe 35

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga daya bangaren Abdul yace "What is wrong with you these days Khaleesat?

Me yake damun ki?" Tunanin abinda zata ce masa ta fara yi, tayi shiru gabanta na faduwa, ita ta ma rasa me yasa take
in daga kiransa kwanan nan, kawai a zuciyarta take jin bata son waya da shi, Jay ya daga kai ya kalleta jin tayi shiru ga waya
are a kunnenta, amsar wayar yayi ta zaro ido tana kallonsa da mamaki with fear, ya sa wayar handsfree ya rage volume sannan ya ajiye saman table ya ci gaba da cin abincinsa, a fusace Abdul yace "Wai baki ji na ne, or is something wrong with you?" A hankali Khaleesat tace "Ina jin ka mana, na mance wayar ne a gidansu Safiyyah, i just got it now" Sounding so provoked yace "Ni zaki raina ma hankali?

Ke ce zaki bar wayarki tun jiya gidansu Safiyyah?" Khaleesat ta wani kyabe baki ta kauda kai tace "Haka dai kawai bazan ki daga kiranka ba, me yasa baza ka min uxuri ba?" Abdul yace "Wait Khaleesat, where are you getting ur liver from these days?

Who is ur vendor?

Yaushe kika fara samun courage din mayar min da magana?" Khaleesat tace "Toh ni yanzu me nayi?

Nace maka wayar baya wajena and u are trying to create an issue out of nothing, Nan da few weeks fa za mu fara jarabawa, you are only adding more pressure to the one i am already in, ka dinga considering dina mana pls" Jay ya
an daga kai ya kalleta, sai kuma yayi murmushi ya dau ruwan gora ya bude yana sha, Abdul yace "A kanki aka fara jarabawa?

What is the big deal ah jarabawan da zaki yi?

Ko dai Safiyyah ce ke dora ki akan abinda bazai fisshe ki ba?

Safiyyah ce take zuga ki har kika fara samun courage din mayar min da magana ko?

Switch to video call now" Khaleesat taji gabanta ya fadi sosai, Jay dai murmushi kawai yake, a hankali Khaleesat tace "Ohk i will, amma kayi hakuri let me dress up first..." A mugun fusace yace "Ki bar shi" Yana fadin haka ya katse wayar, Khaleesat dai tayi shiru tana kallon wayar nata, Jay yace "Ki gama cin abinda zaki ci mu tafi Halysaah, it's pass magrib now zan je inyi sallah" Khaleesat ta daga idanuwanta tana kallonsa, yace "Ko ayi maki takeaway din abincin?" Ta sauke idonta bayan sun hada ido da Ajay da ya mike daga inda yake zaune, Jay ya juya ya
an kalli Ajay yace "Hey man, ka hada har nawa bills din" Ajay yaki kallon direction dinsa kai kace bai san sa ba ma, Jay ya kira daya daga ma'aikatan wajen ta karaso, ya sa tayi masu packaging abincin da Khaleesat bata ci ba, ita dai Khaleesat har sannan taki cewa komai kana ganinta kasan she is a bit disturb, Jay ya bi Ajay da kallo har ya fita daga Eatry din da baturiyar da suke tare, shi bai ma ta
a ganinta ba sai ranan duk kwashe kwashen Ajay ne, bayan ma'aikaciyar wajen ta gama packaging abincin, yana kallonta ya tambayeta bill dinsa, nan ta sanar masa Ajay ya hada har nasu ya biya, Khaleesat ta daga kai ta kalli waitress din jin abinda tace, Jay yace "Ok then" Mikewa yayi ya dau ledan abincin Halysaah yana kallonta, ta tashi ta dau wayarta, yana gaba tana biye da shi suka fita daga wajen cin abincin, Lyft din da Jay yayi masu order har ya iso, ya bude mata back seat yana jiran ta shiga, Khaleesat felt somehow hakan da yayi, don duk fitar da suke yi da Abdul bai ta
a mata haka ba, yawanci ma shi yake fara shiga sannan ta shiga, bayan ta shiga motar Housemate dinta ma ya shiga, sai da suka kusa gida wayarta ya fara vibrate, ta kasa duba me kiranta sanin kila bazai wuce Abdul ba, Jay dake danna wayarsa ya kalleta yace "Kiran ki ake ai" Bata ce masa komai ba ta kalli screen din wayar sai taga Safiyyah ce ke kiranta, ta daga da sauri ta kai kunne tace "Hello Sophie" Safiyyah tace "Am at the door, nayi knocking shiru" Khaleesat ta
an saci kallon Jay, sai kuma a hankali tace "Ohk na
an fita ne amma ina hanya yanzu" Da mamaki Safiyyah tace "Kin fita?

Ban gane kin fita ba, Ina kika je?" Khaleesat tayi shiru, Safiyyah tace "Ko da Housemate din ki?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Hmmm i see, to in dai baku kusa dawowa ba bari inyi tafiyata kawai" Da sauri Khaleesat tace "Aa ki jirani am on my way" Tana fadin haka ta katse wayar, ajiyar zuciya ta sauke don tayi tunanin Abdul ne ya kira Safiyyah shine ta kirata, after some minutes suka isa gida, ta bude side dinta ta sauka daga Uber din, Jay ma ya sauka, Apartment dinsu ta nufa, ta
an rage pace dinta ganin kamar motar Mustapha a vicinity din, shi dai Housemate dinta na biye da ita a baya, sai ga Safiyyah ta fito daga motar Mustapha, da murmushi fuskarta ta nufesu ta gaida Jay, ya tsaya ya amsa mata sannan ya wuce cikin gida, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Toh ki gaida ya Mustapha, dama girki na tsaya maki na zata har yanzu bakya iya tashi" Khaleesat ta kirkiro murmushi tace "Ohk bari in gaishesa" Zagawa tayi zuwa side din Mustapha taga yanda ya bi Jay da kallo har Jay ya shiga cikin gida, gaishesa tayi kanta a kasa, ya kalleta yace "Who is he Khaleesat?" A hankali Khaleesat tace "Housemate dina ne" Mustapha ya kalli Safiyyah yace "There was a time da kika ce min mace ce Housemate dinta?" Safiyyah tace "Eh wallahi the lady packed out shine shi ya shigo, ai bai wani dade sosai da dawowa apartment din ba" Mustapha ya kalli Khaleesat yace "Me yasa zaki dinga zama gida daya da namiji da sunan Co-living Khaleesat, why not come stay together with ur frnd Safiyyah in my house?" Safiyyah ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki, sai kace ya gama kwatar mata 'yan ci gun shegiyar matarsa balle ya kwatar ma ita da kawarta, ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana wasa da veil dinta, Mustapha yace "Wani yare ne Housemate din naki?" Caraf Safiyyah tayi tace "He is from Tanzania, yaren can kasar yake yi, beside shi baya ma wani zama a gidan once a while yake zuwa yayi karatu kawai" Mustapha ya wani kalleta yace "Ke na tambaya?" Gefe ta koma bata sake cewa komai ba, Mustapha yace "Daga ina ku ke da daddaren nan Khaleesat?" Khaleesat tace "I was sick tun da safe shine muka je ya siya min abinci yanzu" Mustapha dai sai kallonta yake, after some seconds yace "I will talk to my wife, sai ki dawo nan gidana kiyi zamanki tare da Safiyyah har ku gama Exams, i think the exam is by the corner...." Khaleesat tayi murmushi kawai bata basa amsa ba, Safiyyah tace "Mu je in kai maki abincin da na kawo maki ciki" Bude bayan motar tayi ta ciro abincin, Khaleesat tayi ma Mustapha sai da safe sannan suka wuce apartment dinta tare da Safiyyah, nan parlor Safiyyah ta ajiye abincin tayi kasa da murya tana washe baki tace "Ban gane wannan fitar da ku ke yi da Housemate dinki ba Khaleesat?

Ina ku ka je?" Khaleesat tace "Abinci fa muka je ya siya min, kuma ba wai lapiyata lau muka je ya siya min abincin ba" Khaleesat ta ajiye ledan abincin hannunta ta zauna gefen kujera tare da sauke boyayyen ajiyar zuciya, Safiyyah dake washe baki tana ma Khaleesat wani kallo tace "To ya aka yi yasan baki da lafiya, kuma how did he know what was wrong with you?" Khaleesat tace "Kinga Sophie wnn ba shine damuwata ba yanzu, muna gidan cin abinci Abdul ya kirani" Safiyyah ta wani yatsine fuska tace "So?

Da ya kiraki sai aka yi yaya?" Cike da damuwa Khaleesat ta bata labarin yanda aka yi da kuma call dinsa da ta ki picking tun jiya, Safiyyah tace "Haba, to ko ke fa da kika fara kokarin kwatar ma kanki 'yan ci, ni sai nake ga kamar Housemate din nan naki ne ke baki Liver kike wasu abubuwa yanzu, banda haka yaushe har kika yi bakin gaya ma Abdul magana haka" Tana dariya ta kare maganar, Khaleesat ta dinga hararanta ganin ta ma maida abun joke, Safiyyah tace "In ni ce ke ma bazan kirasa ba wallahi, gwara kawai komai ya ruguje kowa ya huta" Khaleesat tace "Kin manta abinda yayi kwanaki kawai muka gansa kamar an jefosa Sophie?
Chapter 35 · 0% Book details