← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 180

Sashe 67

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shin kunada labarin MG
s Beauty Lounge zai bu
e a ranar Litinin, 2nd June 2025
daidai lokacin Sallah!

Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
s Beauty Lounge ya bu
e da kwalliya, tsafta da
amshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai
aukar ido
Wanke
afafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-turai, humra, incense da
amshi masu da
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba
kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.

Zo ki ji da
in wanke
afa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da
amshi
komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki
ki ji da
in sauyin MG
s Beauty Lounge.

Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
*Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga me kasuwar garin Dutse Hajiya Aunty Zahrah da Hajjaju Sadiya Chamo Ex in-law, Hajiya Nafeesah Mom twins da Ummu Zainab Maman Ramla, Aunty Maryam Dan Ladi nasidi kema na gaisheki da katon murya, Hajiya Zainurah Boss Lady, Hajiya Jumare da Hajiya Asmy me kayan amare, Oum Nabeelah, Mardiyyah, Uwar Janan, Halysah Garba
i hail you all with respect yan Palace*
Manyan Membobin _
Khaleesat's Citadel_
*Su Meenah parrot
, Oum Noor, Nafeesah Jawwad, Rukayya, Fidomashi, Siyam, M manal, Mrs Barrister, Shanono Esq, Ummilos, Na'imatu, Zulaiha, Ummu Abdrhm, Khaleesat Haiydar is saying a big thank you to you all for ur support always, Allah ya bar min ku*
HALYSAAH 33
Aunty Farida ta numfasa a hankali tace "Da yake Abdul shi kadai ne namiji gun mahaifinsa, mahaifin ya dauki son duniya ya dora masa kuma bai jin maganar kowa sai nasa, duk abinda Abdul yake so shi mahaifinsa ke so, bayan yaga Khaleesat a kotu babu tantama zuwa yayi ya samu uban ya nuna yana sonta zai kuma aureta, wannan dalili yasa babu bata lokaci suka janye kara a kotu suka bar maganar miliyan dari da sharadin Malam Ali zai ba Abdul auren er sa Khaleesat, mu dai har yau bamu san ko da wata yarjejeniya da aka yi a kotun ba ko babu, mun dai san an janye kara kawai kuma duk muka yi farin ciki sosai da hakan, burin mu kawai Malam Ali ya dawo gare mu ko da bazai tsinana mu da komai ba amma mu dinga ganinsa a tare da mu a matsayin kantangar gida, balle duk mun san yayi ma iyalansa hidima dai dai gwargwado ya kuma kyautata masu yanda ya kamata, jarabawa ce kawai ta fada masa, bana mantawa Khaleesat ta shiga damuwa sosai a lkcn tana ta koke koke wai ita bata son Abdul tun ma bata san kalansa ba bata gansa ba tace bata sonsa bazata iya aurensa ba, mu kam idonmu duk ya rufe da son ganin an wanke Malam Ali daga laifin da ake zarginsa da shi, ni da uwarta muka yi ta bata baki muna kwantar mata da hankali muka ce ko tafi son a maida mahaifinta prison ne, ko don mahaifinta bazata hakura ba ta amince da bukatar Abdul na son aurenta don case din ya mutu gaba daya, gashi tun bayan dawowar Malam Ali yayi ta rashin lafiya ko kudin kai sa asibiti babu, duba da hakan ne ma yasa muka yi ta karfafa ma Khaleesat gwiwa muna bata baki, a haka dai muka samu muka lallabata ta fara hakura, nan kishiyoyin Ummanta suka fito da ba
in cikinsu da hassada a fili tunda su ma ai suna da 'ya ya mata sa'annin Khaleesat da ma wa enda suka girmeta amma shine Abdul zai ce sai Khaleesat, nan fa duk suka hau gaba sosai da yayata saboda
an mai kudi ya ga Khaleesat yace yana so, ranan farko da Abdul ya fara zuwa unguwan cewa yayi shi bazai shigo da motarsa layin ba ta fito bakin titi ta samesa, gashi daga gidan zuwa bakin titi akwai tafiya sosai, haka nan uwar ta lallabata ta shirya ta saka nikab dinta kannenta biyu suka rakata har bakin titin ta samesa, a ranan kuma ya bata babban waya ya kuma hadata da dubu hamsin, ba ma ita ta amsa ba don nuna masa tayi bata so shine ya ba kannenta yayi tafiyarsa, da kudin aka samu aka biya mata waec dinta tunda ba mu da yanda za mu yi, a kaf tarihi ban ta
a jin wanda yake neman yarinya da isa da gadara da walakanci kamar Abdul ba, for almost 2 months in Abdul zai zo unguwan mu sai dai dole ta fito titi ta samesa shi bazai shiga layin da motarsa ba, watarana ne ya kira bata da lafiya shine da ya tashi zuwa dubata da yamma ya shigo layin a karo na farko tunda ya fara zuwa gurin ta, daga nan kuma ya dena cewa ta fito bakin titi in ya zo sai dai ya karasa ciki da motarsa, ya kai ya kawo har cikin gida yana shigowa, tun a wannan lokacin Abdul baya raga ma Khaleesat, fadan yau daban na gobe daban, bashi da fahimta bashi da uxuri, ga nuna isa da gadara abinda yace yake so dole shi zata yi, haka nan yarinyar nan ke hakuri da halinsa duk don saboda mahaifinta, rana daddaya ne baya sa ta kuka, sai dai ni da uwarta mu yi ta bata hakuri muna ganin duk me sauki ne tunda har yana sonta kuma yaji zai aureta ya zauna da ita wataran zata canza sa da kanta, ni dai a sanda na fara sarewa da lamarin Abdul jikina yayi sanyi shine watarana da ya daga hannu ya mareta har sai da shatin yatsunsa ya kwanta fuskarta, mu dai har yau bata gaya mana me tayi masa da yayi mata haka ba don a cikin motarsa hakan ya faru, nan jikin uwarta ma ya fara sanyi kan lamarin har ta samu Mai gidanta ta gaya masa amma Malam Ali yayi ta kakkarewa har da cewa duk wanda ma ya kara tada maganar Allah ya isa, ana haka har ya biya mata jamb ya kai ta da kansa ta zana don fara jami'a tunda waec dinta ya fito kuma sakamakonta yayi kyau sosai, kawai rana daya kwatsam ubansa ya kira mahaifinta wai ga abinda Abdul yace yake so, wato zai tura Khaleesat Amurka tayi karatu a can, duk kawaicin da yayata take wannan karan sai da ta nuna bata amince da hakan ba, don ana ta bin su a yanda suke so ba hakan ke nufin bamu da ta cewa akan lamarin Khaleesat ba, ba Yayata ba har kakar Khaleesat Nenne ta nuna rashin amincewarta a wannan bukatar tasu, babu ta yanda za a dau yarinya karama haka da ko mallakan hankalinta bata gama yi ba ace za a tura ta har Amurka da sunan karatu, in haka ne kawai a daura auren mana sai ya kai ta duk inda ma zai kai ta tayi karatu, in ko ba haka ba babu inda er ta zata je da sunan karatu sai dai duk abinda zai faru ya faru, a nan dai laifin Mahaifin Khaleesat ne da ya dau tsoron duniya ya dora ma Abdul da mahaifinsa ba kuma tsoron komai ba sai tsoron kar su sake maidasa inda ya baro wato prison, dama tunda ya baro can ya dawo gashi nan gashin nan dai kamar ya
an samu matsala a kwakwalwarsa, yau lafiya gobe akasin haka, ya dawo kamar ba Malam Ali ba, a lokacin duk ya gigice yayi ta bala'i wai ina ne ba a tura yaro karatu a zamanin yanxu, yarinya me shekara sha bakwai ce za ace ma yarinya, inda yake shiga ba nan yake fita ba, hakan ya zame masu bacin rai sosai da mahaifiyar Khaleesat har sai da ta bar gidan ta koma gidan Mahaifiyarsa warce ita ma yaki sauraronta, haka nan Malam Ali ya dau Khaleesat ya damka ma Abdul ba tare da amincewar uwarta ba ya kai ta karatu Amurka, Shiru Aunty Farida tayi tana kallon su Ajay dake kallonta duk suna sauraronta, a hankali tace "Tun daga sannan shi yake sponsoring komai nata a Amurka, cin ta da shan ta, da suturanta komai dai shi ne, sai san da ya ga dama ne yake bari ta zo hutu Nigeria, mu tsakaninmu da ita dama sai sanda muka ganta ko kuma muyi magana ta WhatsApp, gashi yaki a daura auren nasu wai sai ta gama karatun wanda wnn ne ke kara daga mana hankali, a haka ake ta rayuwar bamu da kwanciyar hankali, a ko da yaushe fatanmu shine ayi ayi auren don duk wasu iyaye nagari baza a same su da kwanciyar hankali ba ace yau er su budurwa bata gabansu, kusan kullum sai uwarta ta zubda hawaye kan wannan lamari sanadiyar hakan har sai da hawan jini ya kamata, ace bata da iko da er ta sai dai abinda Abdul da ubansa suka tsara gashi mai gidanta ya dau tsoron duniya ya dora masu sai jan sa suke kamar rakumi da akala.... ko wata biyu ba ayi ba ranan yayata ta kirani take sanar min sun kawo kudin auren Khaleesat, duk muka yi farin ciki sosai da hakan, muka yi fatan Allah ya sa hakan alkhairi ne a rayuwar Khaleesat tunda mu ma mun fi son ayi auren kowa ma ya huta, kawai ranan juma'an nan da ta wuce sai ga kiran yayata wai an daura auren Khaleesat da Abdul, nace mata ban gane ba, Khaleesat din ta dawo ne?

Sannan dama ana daura aure haka ba shiri?
Chapter 67 · 0% Book details