← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 180

Sashe 118

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don ma kun samu masu hakuri da kawaici da wasu ne idan ba a zo da motar yan sanda an tafi da ku ba ku ce bani ba, wannan ai rashin gaskiya ne da rashin tsoron Allah kiri kiri, duk kun yi mukus da bakin ku za ku cinye miliyan goma ga banza ta samu" Aunty Farida ta juya tana kallon Mama Zubaida, sai kuma ta nufeta tana cewa "Zubaida idan ban zubar maki da hakora a gidan nan yau ba ki ce bani ba, don kaza kazan ki akwai tsinannen da ya sako bakin ki?

Uwarki muka yi ma rashin gaskiya ko ubanki?" Mama Zubaida tayi wani shewa tana tafe hannu tace "To yau kika saba Farida?

Ai ke fitsararriya ce dama mara mutunci mara kunya shi yasa ga ki har yau duk kyan ki kin rasa mashinshini sai dai kiyi tuwo tuwo a garin legas kina hadawa da karuwanci, waye bai san wannan ba?" Aunty Farida zata cakumo Mama Zubaida Mama Shatu ta shige tsakaninsu tace "Ke yanxu Farida Zubaida sa'arki ce zaki dinga zaginta haka ta uwa ta uba don kawai tana kishiyar yayarki?

Daga dai ta fadi gaskiya banda
an Adam baya son gaskiya?" Aunty Farida tayi wani wurgi da Mama Shatu sai ga ta a kasa timmm, tuni Mama Zubaida ta shige dakinta ta kulle kofarta da sakata tana cewa "Haka kawai ki shafa min bakin jini irin na ku?

Allah ya sauwake in yi dambe dake Farida, ku je can ku ji da rashin sa'ar ku a rayuwa, ku kenan daga wannan iftila'in sai wannan bala'in, ko wani fitinar duniya a kan ku ya kare, daga wannan sai wannan, Allah kadai yasan laifin da ku ka tafka a kasar ku, kilan ma ta zina aka sami ke da yayar taki, ga bakin jini da rashin sa'ar ku ya shafi Malam ya talauce" Da kafa Aunty Farida ta hambare uban miyan da Mama Zubaida ke yi na abincin siyarwanta, miyar duk suka malale kasa, shinkafar ma dake cikin kwando ta kifar da shi a kasa tana zagin Mama Zubaida ta uwa ta uba, Mama Shatu ganin yanda aka yi watsi da kayan sana'an Mama Zubaida ya sa ta ja bakinta tayi shiru ta tafi gun nata miyan ta zauna tana cewa "Hakuri kawai za kiyi Farida, hakan ba dadi kam" Momy ta rike ha
a tace "Alhamdulillahi da na yi iya bakin kokarina na ganin ban hada iri da gayyar tsiya ba, ku kuga wannan tsiya haka kamar 'yar tasha, ga talauci ga tashanci, Abdul ya so ja mana abun fade a dangi Allah ya takaita min abun, kuma ba dai kun ce kudade na banki ba, to zuwa yau da daddare in ga alert din Miliyan goma, in kuwa ba haka ba gobe da sassafe za ku gan ni a gidan nan ba kuma zuwan lumana zan yi ba, ai shi ramin karya kurarre ne, kuma ko kwabo daya yayi ciwon kai a kudaden nan wallahi sai an daure er ku..." Momy na kai wa nan ta bude handbag dinta ta ciro takarda dauke da account details dinta ta jefa ma Khaleesat sannan ja tawagarta suka yi waje tana cewa "Haka kawai Meemah zata ja min bala'i ta hada
ashi da wannan iri na fitina, irin tsiya, to kiyi dambe da ita ki ce kin yi dambe da wa?

Kina ganin yarinya kamar mahaukaciya, A'a wallahi Allah ya maki tsari" A haka duk suka fita daga compound din, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma komawa dakinta tayi tayi tagumi ranta ba dadi, ita kam ta gode Allah da jarabawa iri iri, daga wannan sai wannan, Khaleesat ta dau takardan da Momy ta jefa mata ta juya ta shiga dakin Umma hawaye na zuba idonta, Aunty Farida kuwa bata fasa zage su Mama Zubaida da Mama Shatu a tsakar gida ba, Mama Zubaida taki fitowa kuma taki tanka Aunty Farida, Mama Shatu kuwa tayi tsit kamar bata san da wa Aunty Farida take ba, daga karshe bayan Aunty Farida tayi masu wankin babban bargo ta shige dakin Umma tana huci, Umma ta daga kai tana kallonta tace "Yanxu ban isa ince ki bari ki bari ba Farida?" Aunty Farida ko tanka Umma bata yi ba ta dau Hijab dinta ta saka tana kallon Khaleesat tace "Ki tashi ki shirya mu tafi bankin" Mikewa Khaleesat tayi tana goge idonta ta dau hijab dinta ta saka, a haka suka kama hanyar banki da Aunty Farida, amma suna isa bankin suka tarar an tashi aiki sai ran Monday don karfe hudu har da rabi a lokacin, Aunty Farida na kallon Khaleesat bayan sun fito bankin tace "Goben karfe nawa ne tafiyar naku?" A hankali Khaleesat tace "Flight din karfe daya zuwa Abuja, daga Abuja kuma jirgin yamma ne" Aunty Farida tace "Kuma bazai yiwu a daga tafiyar ba Khaleesat?

Kinga banki dole fa sai Monday idan Allah ya kai mu" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, ita kanta she is just confuse bata san yanda zata yi ba.

A haka suka koma gida kusan karfe biyar da rabi, Umma na kallonsu tace "An tashi a banki ko?" Aunty Farida bata ce komai ba ta cire hijab dinta ta nemi waje ta zauna, Khaleesat ta zauna tana kallon Umma tace "Banki sai ranan litinin, sun tashi yau" Umma tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Kema kin san bai amshi kudinsa ba me yasa zaki yi shiru har na sati daya Khaleesat?

Yanxu da kinyi magana tun yaushe za a san yanda za ayi a cire kudin a mayar masa kayansa, yanxu rashin mutuncin da suka zo suka mana makota na ji ina amfanin sa?" Aunty Farida tace "A'a ta min maganan kudin fa ranan Alhamis, a lkcn ma tayi zaton yau ne tafiyar ashe gobe ne, kuma kema kinsan Khaleesat bazata ta
a ko biyar a kudin nan ba tunda ba nata bane, kawai dai dama matsiyata ne yan iska daga Abdul din har iyayensa" A hankali Khaleesat tace "In ma an cire kudin an basu bazan iya tafiya babu kudi a account din ba, don baza a bari in shiga kasar ba, they wilk see i am not financially capable idan babu kudi a account dina, shi yasa ma ya bar kudin a account din all this years" Aunty Farida tayi shiru
don bata ma san me zata ce ba, haka ma Umma da ta rafka tagumi tun shigowarsu, after a while a hankali Umma tace "Ni tsorona kar su dawo goben da suka ce bamu san kuma da me za su zo mana ba" Aunty Farida ta mike tace "Sai su zo su amshi babu tunda su yan iska ne" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, Umma na kallonta a hankali tace "Kiyi hakuri Jiddah, wataran duk hakan zai zama labari, Allah ya bamu ikon cin jarabawan mu, in ma kin koma makarantar in ma baki koma ba duk yanda Allah yayi dai dai ne" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata ta mike ta dau tsintsiya zata yi gyaran dakin Umma tana goge hawayen dake sauka idonta....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
Read my book "HALYSAAH" on ArewaBooks, Platform available: "app only" :: https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
HALYSAAH 56
Khaleesat har ta fara bacci wajen karfe goma da rabi Aunty Farida ta tasheta tana mika mata sabuwar wayarta dake vibrate, mikewa tayi zaune tana gyara hulan kanta ta amshi wayar taga Safiyyah ce ke kiranta,
agawa tayi ta kai kunne, daga daya bangaren Safiyyah tace "Ko har kin fara bacci ne" Khaleesat tace "Um, da wuri na kwanta ne" Safiyyah tace "Ayya sorry for waking you up, dama Housemate din ki ne yace in tambayeki wani account zai maki funding, cause nasan definitely Abdul ya amshi kudinsa dake account din ki ko?" Khaleesat tayi shiru ta kasa ce ma Safiyyah komai, har sai da Safiyyah tace "Hello" a hankali Khaleesat tace "Ina jin ki Sophie" Safiyyah tace "To naji kin yi shiru" Khaleesat ta daga kai ta kalli Aunty Farida dake kallonta, goge hawayen dake makale idonta tayi cikin sanyin murya tace "Daxu Mom dinsa suka zo za su amshi kudin, ni kuma bazan iya transfer ba kuma bani da Atm card, shi ne ta ajiye min account number wai in tura masu kudin yau, and today is Friday, mun je banki sun tashi, yanxu tace zata dawo gobe da safe idan ban tura mata kudin ba" Safiyyah dake ta sauraron Khaleesat cikin bacin rai tace "Allah ya sauwake, ke kiji wani tsiya don girman Allah, akan miliyan tara ne ko goma uwar ta kamo hanyar gidan ku da kanta?

Can you imagine fa?

A'a gaskiya sai yanxu nake sake tabbatar da su Abdul were once poor in this life, all of a sudden kawai Allah ya basu arziki sama ta ka, nobody can change this my perspective wallahi, banda tsiya meye kuma miliyan Goma a irin yanda suke show casing arzikinsu, what is 10M to them? wannan ai abun kunya ne a garesu, Ke kuma maimakon ki kirani tun daxu ki gaya min shi ne kika yi shiru?

Yanxu ba don Housemate dinki yayi reason cewar dole sai da sufficient fund a account dinki za ki iya tafiya ba da shiru zaki yi kenan sai gobe da za mu tafi ki gaya min?
Chapter 118 · 0% Book details