← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 180

Sashe 45

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har karfe dayan dare Khaleesat bata ji ko digon bacci ya zo mata ba, tana dai kwance tayi lamo cikin duvet, her heart is soo heavy, har wani zafi take jin yake mata, ga wani zazzabin da taji ya lullubeta, tun da Jay ya bar ta take kuka, gani take kamar duniyar ya tsaya mata ne cak, ta ma rasa wani kalan tunani zata yi, abubuwan da suka faru daxu suka dinga dawo mata abun sai yake mata kamar mafarki, she wish mafarkin ne ma kawai, yanzu babban tashin hankalinta bata san me zai faru a Nigeria ba, bata san next step din Abdul ba, bata san me zai ma iyayenta ba, duk wannan tunanin ya hadu yayi distabilizing dinta, zazzabin da take ji ya karu sosai, tana son tashi taje tayi alwala tayi sallah ko zata samu sukuni amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake mata ga ciwon kai kamar kanta zai fashe, da taji azaban yayi mata yawa kamar zata kira Housemate dinta ta tambayesa maganin ciwon kai amma ta fasa don bata san ko bacci yake ba, haka tayi ta juye juye jikinta yayi zafi sosai, yanda taga rana haka taga daren nan that was soo long to her, bacci ko na barawo bai dauketa ba, jin vibration din da wayarsa yayi yasa tayi karfin halin jawowa tana kallon screen taga alarm ne na karfe biyar, ta kashe alarm din tana son tashi don tayi sallah amma ta kasa, daga karshe dai haka tayi karfin hali ta daure ta tafi bandaki ta dauro alwalan, tana idar da sallan taji zazzabin da yafi na baya ya lullubeta gaba daya, kwanciya tayi saman gado ta rufe har kanta da duvet din.

Wajen karfe takwas na safe Jay yayi knocking kofar dakinta, tana ji amma ta kasa amsawa, sau uku yana knocking jin bata amsa ba sai ya kira wayarsa dake wajenta nan ma tana kallon kiran amma ta kasa daga hannu ma ta dau wayar, sai da ya katse sannan ya bude kofar dakin da sallama ya shiga, yana kallonta da mamaki ya nufeta yace "Are you Okay Halysaah?" Kai kawai ta girgiza masa, ya duka kusa da ita yace "Baki da lafiya ne?

Why didn't you call my line?" Hawaye ya gani idonta, yace "Haba Halysaah, ba nace kar ki sa ma kanki damuwa ba?

Did you want to hurt ur self?" Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya fita daga dakin, after some minutes ya dawo da Hot chocolate ya ajiye mata yace "Ki daure ki sha pls, let me get you medicine" Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo ya ga bata tashi ba still, duk yanda yayi da ita ta tashi ta sha shayin ya bata magani taki tashi, gaba daya ya ma rasa yanda zai yi da ita, can ya kara dukawa kusa da ita yace "Did you have ur frnd safiyyah's number offhand?" Da kyar ta girgiza masa kai, yace "U have her IG handle?

Is she active on IG?" Bata ce masa komai ba don ta ma kasa maganan, he look confuse at this point, can dai yace "To zaki iya daurewa ki tashi mu tafi asibiti?" Ta girgiza masa kai, mikewa yayi kawai ya fita daga dakin, downstairs ya sauka don AJ na dinning yana breakfast ga Legend dinsa zaune
an nesa da shi a dinning area din, Jay ya nufesa looking confuse yace "AJ, the girl is seriously sick fa" AJ dake sipping tea dinsa yace "Which girl?" Jay ya masa wani kallo yace "Please be serious AJ, wallahi bata da lafiya sosai" AJ yace "To yanzu daukar ta zaka yi ka kai ta Hospital kenan..." Jay yace "How?? ko tashi fa bata iya yi, plss ko zaka mata allura ta
an samu relieve tukun?" A hankali AJ ya ajiye Mug din hannunsa yana kallon Jay baya ko kiftawa, can ya matsar da shayin gabansa yace "Amma dai don Allah me yasa ka raina ni haka ne Jay?

Me nayi maka?

Kai me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni?" On a serious note Ajay ke masa tambayoyin nan looking at him and waiting for his answer, Jay yace "Da gaske fa you are Heartless Junaid, ince maka yarinya ko tashi bata iya yi?

Why are you like this pls?" AJ yace "But like seriously kai uban me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni?

Baka fi ni zama likita ba?

Wato ni ne
an iska ko?" Juyawa Jay yayi ya bar wajen ya koma sama, yana bude kofar dakin ya ganta duke kusa da kofar bandaki, ya karasa kusa da ita da sauri ganin yanda ta galabaita yace "Did you throw up?" Kai kawai ta gyada masa tana maida numfashi, gun da ya ajiye hot chocolate din ya tafi ya dauko mata yace "Pls ki sha ko kadan ne sai in baki magani" Ta girgiza masa kai, yace "C'mon Halysaah, kadan fa za ki sha" Yana rike da cup din don kar ya sakar mata ta zubar, a haka ta kurbi shayin kadan, sai da yasa ta kara sha sannan ya ajiye shayin ya dauko magani, tana ganin maganin ta fara girgiza masa kai da sauri don har taji wani aman zai taho mata, bude kofar dakin aka yi Jay ya juya, AJ ya gani tsaye bakin kofar yana kallonsu, Jay bai sake kallon inda yake ba ya maida dubansa kan Khaleesat yace "Pls ki daure ki sha Halysaah, ko baki son ki samu relieve?" Kara girgiza masa kai tayi hawaye ya fara sauka idonta, lallabata Jay ya fara yi akan ta sha maganin, AJ ya wani hade rai yace "Kee baza ki amshi maganin da ake baki ba?

Wa zaki ba wahala?" Jay yace "Ba ruwanka pls AJ, get out" Ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba tana fama da kanta, Jay bai sake takurata kan ta sha maganin ba ya mike yace "Toh ki daure ki hau kan gado ki kwanta, i am coming now" Ta gyada masa kai, ya juya ya nufi kofa, ko kallon Ajay bai yi ba ya fita daga dakin, AJ ya tabe baki ya juya ya koma downstairs.

Haka nan Jay ya hado alluran da za mata don saukar mata da zazzabin, sai da ta ga ya dawo dakin sannan ta daure ta koma saman gadon tana ganin jiri ta kwanta, ya tsaya gefen gadon yana rike da alluran yana kallonta, ta marairaice ta girgiza masa kai kawai alamar bata so, ya kwantar da murya yace "To ya kike son in maki Halysaah?

Kin ki shan magani" wayarsa dake aljihunsa ya ciro jin yana ringing ganin Salem ke kiransa ya ajiye alluran hannunsa yace "I am coming Halysaah" Fita yayi daga dakin, ya sauka downstairs ya tarar da Salem zaune parlor, bayan sun gaisa Salem yace "Slide dina nake son zaka duba min Jay" Shi dai AJ na zaune yana kallon kwallo ga Legend a gefensa, Jay yace "Ohk, but tunda ka zo pls zaka yi injecting Housemate dita she is sick" Salem yace "Ayya, shi sa ta kira jiya, Allah ya bata lafiya, tana can gidan nata ne?" Jay yace "No, she is upstairs, mu je in nuna maka dakin da take" A tare suka wuce sama, AJ dai kallonsa kawai yake a TV kamar bai san suna parlon ba, Jay bai shiga dakin ba bayan ya nuna ma Salem ya dawo downstairs ya zauna, Khaleesat bata yi ma Salem wani musu ba don ba ma ta da wannan strength din duk da yanda bata son allura haka nan ta bari ya mata, tsabar zazzabin dake jikinta ko zafin shigar alluran bata wani ji ba, Salem yayi mata Allah ya sauwake sannan ya fita daga dakin ya koma downstairs, Jay yace "Thank you, bari in duba maka" Sai bay
an kusan minti talatin Jay ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tayi bacci, ya sauke ajiyar zuciya ya karasa kusa da gadon ya kai hannu kusa da goshinta sai dai bai ta
a ta ba, nan yaji temperature dinta ya fara sauka, juyawa yayi ya dau sauran shayin da ta bari ya fita daga dakin.....
Chapter 45 · 0% Book details