← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 180

Sashe 25

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

How did he convince you har kika bi sa zuwa restaurant?" Khaleesat ta tabe baki tace "Toh meye kuma a kasa?

Daga dai ya kai ni restaurant mu ci abinci?

Kinsan yaushe rabon da inci abincin kirki a gidan?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "He notice i haven't been eating shi ne yasa har ya kai ni restaurant" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai kece da dora ma kanki abinda Allah bai dora maki ba kawata, akan Abdul din da naga yayi updating status da jersey jiya alamar har ya koma Nigeria ya ci gaba da harkokin gabansa ke kina nan kina neman kashe kanki, wallahi in zaki ajiye lamarin gayen nan a gefe da zai fi maki alkhairi a rayuwarki, very very heartless guy with no conscience, dubi tsabar zuciyarsa ta dutse ne ya gwammace ya kara siyan ticket yayi juyawarsa ya koma Nigeria, Allah ma yasa yayi maki ya jiki zuwan da yayi" Khaleesat dai tayi shiru tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta daga kafada tace "Ga dai Housemate din nan naki duka duka yaushe har ma ku ka san juna?

Amma ya gane kina cikin damuwa har da kai ki restaurant for dinner, to this is how a caring and understanding Boyfriend and a Gentleman should be" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Ni babban damuwata kar ya sake dawowa kasar ban sani ba Sophie, ce masa nayi Housemate dina frnd din Nancy ne fa, kinsan bai san Nancy bata gidan ba ai har yanzu, to kar ya sake dawowa unexpectedly ya gansa" Safiyyah tace "Abinda zai faru kawai kiransa zaki yi ta yi har sanda ya ga daman daga kiranki, ki basa hakuri ki samu ku shirya, in har ku ka shirya duk wani movement dinsa zaki dinga sani, yanzun ma ai don baku communicating ne all this while shi yasa kawai ya taho kamar an jefosa, banda haka ai duk sanda zai zo yana gaya maki" Khaleesat tace "Haka ne, amma kin san irin zuciyarsa wallahi zan iya kiransa sau goma ma bazai daga ba, ko na masa magana ta WhatsApp bazai yi reply ba" a sanyaye ta kare maganar, Safiyya tace "Bari in kirasa ta wayana yana picking zan ce ya kirani, daga nan in ya kira sai in baki wayar ku yi settling dispute din karyan ku" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, amma tasan hakan kadai shi ne way out, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara kiran Abdul, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa sai gashi ya daga, sallama tayi masa ta gaishesa tace "Pls in ba damuwa ka kirani" Katse kiran yayi sai gashi ya kira tayi picking sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amshi wayar gabanta na faduwa ta kai kunne, Safiyyah ta tashi ta bar ta a wajen ta koma wani waje ta zauna, a hankali Khaleesat tace "Don Allah kayi hakuri ka saurareni..." Shiru yayi da yaji muryarta, nan da nan hawaye ya cika
idonta muryarta na rawa tace "Pls kayi hakuri da abinda ya faru, i promise you hakan bazai sake faruwa ba" Yace "Dama akwai abinda ya faru ne?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "I am asking you, akwai abinda ya faru ne dama?" Ta sunkuyar da kanta tace "Don Allah kayi hakuri, i am truly sorry plss" Yace "Look i am super busy now, idan kin shirya gaya min abinda ya faru kike ban hakuri sai ki kirani ta layin ki anjima" Cikin sanyin murya tace "Toh Nagode" Katse wayar yayi, ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta kyabe baki ta dawo kusa da ita ta zauna tace "Ya ku ka yi da shi?" Khaleesat ta ja tsaki tana tattara reading material dinta tace "An gaya masa banda ina tsoron kar ya dawo without notice ni zan sake magana da shi ta waya ne" Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat tana tunanin yaushe bakinta ya fara budewa haka akan Abdul ne wai, Dariya Safiyya tayi tace "Shi Abdul din naki Khalee?" Khaleesat ta ki bata amsa, har ranta ita fa yanzu tana jin bazata iya ci gaba da tolerating abubuwan Abdul ba, ita kanta bata san daga inda wannan liver din yake zuwa mata ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru but she is not tolerating anymore.

Wajen karfe biyu ta koma gida, bayan tayi wanka tayi sallah ta sauya kayanta ta kwanta, sai bayan da tayi la'asar ta shiga kitchen ta jingina da cabinet tana tunanin abinda zata girka, tuwo taji take son ci, kawai daga karshe tayi deciding tayi tuwon since tana da duk ingredients din girka tuwon, kan kace me ta gama girka tuwo da miyar kuka with enough obstacles a ciki, ta gama goge gogen kitchen din sannan ta fito parlor wajen karfe biyar, dai dai shigowar Housemate dinta gidan, ita dai tana tsaye kusa da kitchen, ya juya ya kalleta bayan ya kulle kofar parlon yace "Good evening Halysaah" Tace "Good evening" Yace "What are you cooking with such a nice Aroma" Tace "Tuwo ne" Ya karaso cikin parlon yace "Really, it's been long na ci tuwo fa" Tana kallonsa tace "In kawo maka?" Ya dan buda ido yace "Ok thank you" Juyawa tayi ta koma kitchen din, ya zauna saman kujera hoping ba da yawa zata saka masa ba, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo parlon da plate dauke da tuwo with a diff bowl of soup, tun da ta duka ta ajiye abincin yake kallon bowl din miyan babu ko kiftawa, can dai ya daga kai ya kalleta yace "Wani miya ne wannan Halysaah?" Ta koma gefe tace "Miyar kuka ce" Lkci daya yayi ya
e yana shafa kansa yace "Wow, but bana cin irin miyan, i thought vegetable soup ne, baki yi stew ba?" Ta wani kallesa, a takaice tace "Babu, kuma kayi tasting miyan ne kafin kace baka cin irin sa?" Ya jingina da kujera ya sauke ajiyar zuciya yace "Na ma ci abinci few minutes ago fa" Dukawa tayi ta dau bowl din ta mika masa miyan tace "Taste it first before concluding" Ya dan kalleta yana murmushin dole yace "Ok, where is the spoon?" Tace "Shi ba a cin sa da cokali ai, da hannu zaka sha" Yayi shiru sai kuma yace "Then bari in wanke hannu" Yana fadin haka ya mike, ta koma gefe don basa hanya sannan ta bi sa da kallo har ya tafi bandakin dake parlorn ya wanke hannu sai gashi ya dawo, bayan ya zauna ta mika masa miyan tana kallonsa, shi dai bai yarda ya hada ido da ita ba, tun da ya kai finger ya lasa miyan ya kai baki ya kasa dago kai, ita dai kallonsa kawai take bata ko kiftawa, can dai yana murmushi da kyar ya dago yace "It's sooo nice amma na ci abinci wallahi Halysaah" Duk da dariyar da ya bata ta dake tace "To ai tunda ka sa na zuba sai ka ci ko kadan ne cause i am not throwing it away" Bata jira cewarsa ba ta juye masa miyan a kan tuwon dake plate ta dau plate din ta mika masa tana kallonsa, he was totally speechless and confuse at the same time, tana kallonsa da kyau tace "Karba" Ya kai hannu a hankali ya amsa plate din tuwon, in ya debi tuwon sai ya dangwala miyar kamar yana tsoronsa sannan ya kai baki, sosai ya bata dariya amma fa bata yi ba, instead sai murmushi take, sau uku yana diban tuwon yana ci kuma har sannan yaki yarda su hada ido da ita, kana ganinsa kasan da kyar yake cin abincin, his facial expression says it all, wayarsa ne ya fara vibrate, ya ajiye tuwon da sauri ya fiddo wayar yana kallon screen, sai kuma ya kalleta yace "This is an urgent call Halysaah bari in shiga daki in daga" Kasa basa amsa tayi don kar ma tayi dariyar da take dannewa, ya mike ya nufi dakinsa da sauri don ko jiran jin abinda zata ce bai yi ba, tana ji ya sa ma kofar dakin makulli bayan ya shiga, sai a sannan ta zauna gefen kujera ta rike kanta tana dariya, after some minutes ta mike ta dau plate din tuwon still smiling ta wuce dakinta.
Chapter 25 · 0% Book details