← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 180

Sashe 14

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bazai yiwu ba, ko ana haka ne?" Khaleesat dake sauraronsu ta girgiza kai tana
an murmushi tace "Da sauran lokaci bamu fara ba tukun" Aunty Farida tace "To yanzu dai tun kan wani munafukin yasan kina garin nan mu shiga uku yaushe za ki koma Khaleesah?" Khaleesat ta daga kai a hankali tace "Cikin satin nan in sha Allah" Aunty Farida tace "Toh inji dai Abdul din ya rage abubuwan nan nasa da yake maki?" Khaleesat ta ajiye masu abincin a gabansu kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Babu abinda ya fasa, ni na gaji da halinsa ma yanzu" Umma ta daga kai tana kallonta, Aunty Farida ma kallonta take don bata ta
a cewa ta gaji da halin Abdul ba, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya ta fara cin abincin gabanta tace "Na dai gaya maki babu me canza maki shi sai ke da kanki, ke macece ya kamata ace zuwa yanzu kinsan wanene Abdul kinsan kuma yanda zaki zauna da shi" Mikewa Khaleesat tayi without saying anything don ita yanzu taji ko zancen nasa ma bata so har cikin ranta, tun shekaranjiya da yayi fushi har yau bai kirata ba ita kuma as far as tayi masa miss calls har biyu to bata ji zata iya sake kiransa ba unlike before da ta dinga kiransa kenan ko da bazai daga ba, ko kuma tayi ta masa magana ta WhatsApp, to yanzu kam bata ji zata iya ba.....
07087865788
*Still on free pages*
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
7.....

Kwanan Khaleesat hudu yau a garin kano, kuma har a sannan babu wanda yasan da zuwanta a cikin yan gidansu, ko nan da can bata fita a gidan Baaba Gaje don ma kar tsautsayi ya sa ta hadu da daya daga cikin yan gidan nasu, a kwanaki hudun nan sau biyu Ummanta da Aunty Farida suka zo gidan Baaba Gaje dominta, zuwa sannan Umma ta warware gaba daya tafiyarta ya dawo normal, tun kwanaki biyu da suka wuce ta gama amsan treatment dinta a hospital sai magunguna da take sha kawai, har zuwa ranan kuma Abdul bai kira Khaleesat ba, ita kuwa kawai taji ko a jikinta da ya kira da kar ya kira, there wasn't an atom of disturbance a tattare da ita, ko ta WhatsApp bata yi gigin yi masa magana ba Unlike before da bazata iya hakuri ba sai ta masa, tana bakin murhu tana dafa shinkafa da wake ga turmi gabanta tana
aka yajin da za ayi amfani da shi wajen cin shinkafa da waken, Su Ummanta da Baaba Gaje kuma na can uwar
aka, tunanin yanda zata fara shirye shiryen komawa USA take don suna da wani presentation nan da kwana uku, daxu da safe ta duba available flight da farashinsu online and she is hoping in ta canza dollars din da Housemate dinta ya bata zai isheta ta koma, Khaleesat ta bar da
an yajin da take yi bayan taji Aunty Farida na kwalo mata kira, mikewa tayi ta wuce dakin tana amsawa, tun da ta zo gidan Baaba Gaje ta sakar mata aikin komai, hatta jikokinta ita ke masu wanka kan su tafi makaranta, ita taga kamar har ta
an yi duhu tsabar girki cikin rana da take yi tun zuwanta, Aunty Farida tace "Ana kiran wayarki" nan da nan mood din Khaleesat ya canza ta karasa gun wayar without much interest, duk tunaninta Abdul ne cause she isn't expecting any call from anybody, Number mutumin da ya tarbeta a Airport din Lagos ta gani a gaban Screen din wayarta, ta dinga kallon number bata ko kiftawa, duk da bata yi saving ba amma ta gane nasa ne, daukar wayar tayi ta fita daga dakin ta koma bakin murhun sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yayi ya gaisheta da ladabi, tace "Ina yini?" Yace "Alhamdulillahi Hajiya, ya jama'ar gidan?" Tace "Alhamdulillah" Yace "To maa sha Allah, dama na bugo ne inji ko zaki kara kwanaki nawa nan gaba kan ki koma America?" Khaleesat tayi shiru trying to understand why he is asking her that, yace "Hello?" Tace "Ina jin ka, ban gane tambayar bane" Calmly yace "Aa so nake in san ranan da zaki koma ne Hajiya, in ya kama ayi rescheduling din ticket dinki sai ayi hakan in sha Allah" Khaleesat was speechless, a ranta tace Ticket kuma?

Kasa cewa komai tayi with surprise, taji ta ma kasa ci gaba da tsayuwa, jin ya sake cewa "Hello" ta kifta ido da kyar ta duka kusa da turmin da take daka yaji tace "Ina ji" Yace "Ina ga a bari duk sanda kika shirya zaki nemeni ta waya ko Hajiya?" Sauke idonta tayi kasa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, cikin sanyayyen murya tace "Ranan Lahadi nake son zan koma idan Allah ya yarda" Yace "To Maa sha Allah, dama booking din ranan aka maki da zaki taho, flight din karfe daya ne, za ku tashi ta Airport din Abuja in sha Allah" Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai, yace "Sai kin ji ni in sha Allah Hajiya" A hankali Khaleesat tace "Nagode" Khaleesat na zaune dakin Baaba Gaje tana jujjuya shinkafa da waken dake gabanta da cokali, gaba daya ta kasa cin abincin, ita kanta ta rasa dalili, ko tsabar yanda jikinta yayi sanyi ne tun bayan da suka yi waya da mutumin daxu da ya sanar mata da ticket dinta na komawa America sannan tana gama aikin da take ta bude WhatsApp taga ya aiko mata da Flight Ticket dinta which was also business Class kamar dai yanda ta zo, this made her so weak, gaba daya ta ma rasa gane feeling din dake ranta a lokacin, bata taba tunanin Housemate din nata zai mata ticket din komawa ba, Duk Ummanta na lura da sauyawanta lkci guda, Aunty Farida ta gama shafa powder din da take zata leka gidan wata kawarta Maman Fu'ad a nan hotoron, ta dau jakarta da mayafi tana kallon yayarta tace "To sai na dawo Umma" Umma tace "Amma kar ki dade don Allah Farida" Aunty Farida tace "Haba ai yamma tayi bazan zauna ba Umma" Daga haka ta fita daga dakin tayi ma Baaba Gaje dake waje tare da bakuwarta sallama sannan ta fita daga gidan, Umma ta daga kai tana kallon Khaleesat tace "Menene kika saka abinci a gaba kika kasa ci Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon kyakkyawan fuskar Ummanta, babu wanda zai ce Umma ce ta haifeta sai dai ma yayi tunanin yayarta ce don kama suke ba na wasa ba kamar an tsaga
ara, Khaleesat tayi murmushin yake ta kai shinkafa da waken baki tace "Babu komai fa Umma" Umma tace "Yaushe za ki koma?

Kuma yaya za ayi da batun kudin jirgi?

Har yanzu Abdul din bai san kina nan ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Umma ai nace baya nan kuma ba a samunsa ta waya, ranan lahadi zan koma in sha Allah" Umma tace "Ranan Lahadi?

To ina za ki samu kudin komawa?" Khaleesat ta gyara zamanta tace "Makocin nawa ai tare ya biya min na zuwa da dawowa" Kallonta Umma ta dinga yi da alamar tuhuma ga mamaki kwance fuskarta, Khaleesat taki yarda ta bari su hada ido sai tura abincin gabanta take, Umma tace "Khaleesah" Da kyar Khaleesat ta daga kai gabanta na faduwa, Umma tace "Meye tsakaninki da wannan mutumi da ya biya maki kudin jirgin zuwa har da na komawa?" Khaleesat ta hadiye sauran shinkafar da ya makale a throat dinta da kyar tace "Wallahi Umma babu komai, makocina ne kawai shi, kuma don yaga yanda na daga hankali baki da lafiya shi ne yasa yayi hakan, ni kaina sai bayan da ya biya min na sani, amma ki yarda dani Umma babu komai tsakanina da shi" Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Ummanta ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru, bayan some seconds tace "Toh shikenan, amma dai kinsan in Abdul ya samu labarin nan da matsala ko?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba, jin Umma tayi shiru alamar ta fada duniyar tunani Khaleesat ta daga kai a hankali tace "To ai Umma babu wanda yasan na zo kano har yanzu, don haka bazai sani ba" Umma ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "To gudun kada hakan ya sake faruwa kar ki sake yarda ko wata mu'amula ta hadaki da shi makocin naki Khaleesat, ki rufa mana asiri" Khaleesat bata ce komai ba sai kuma ta jawo handbag dinta ta ciro dala dubu dayan da Housemate dinta ya bata ta nuna ma Umma cikin sanyin murya tace "Wannan ma shi ya bani da zan taho" Umma ta dinga kallon kudin duk da bata san ko nawa bane ta dai ce "Ki kula don Allah Khaleesat kar ki ja mana magana kin dai san wanene Abdul kin san kuma waye Babanki" Khaleesat dai tayi shiru, tasan Umma bata san har nawa bane Dollars din in an canza zuwa Naira, ita dai tayi shiru bata gaya mata ba kar ta kara daga mata hankali.

Washegari da wuri Khaleesat ta shirya ta saka Nikab dinta ta fita don zata je canza dollar din nata ta dan yi siyayya, bayan ta canza dalolin taga har ya wuce yanda take tunani a Naira, nan ta fara zuwa inda zata siyi waya, ta siya ma Ummanta da Aunty Farida sabbin wayar Android iri daya na dubu dari da hamsin each, Ganin Baaba Gaje ma bata da waya kuma ba iya amfani da Android zata yi ba ta siya mata karamar waya na dubu ashirin, daga nan ta karasa kasuwa tayi siyayyar yan abubuwan da zata koma USA da shi, ta siya ma siblings dinta twins mata sabbin school bag da schl shoe da socks, ta siya masu atamfofi kala uku each da mayafai da takalma masu kyau da inner wears, jikokin Baaba Gaje ma ta siya masu takalma da inner wears gaba dayansu, pharmacy ta shiga da takardan da aka rubuta magungunan Ummanta ta siya mata na wata biyu duk da tsadar magungunan, kusan Azahar ta koma gidan Baaba Gaje ta tarar su Ummanta basu zo ba.
Chapter 14 · 0% Book details