Sashe 60
Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Washegari karfe tara Gaje ta shigo gidan, tun daga bakin kofa ta fara ba Maman Fu'ad labarin abinda ke faruwa tace "Sadiyah wajen karfe goma suka zo nemanta a gidana wallahi jiya har da shi Awdul din, ni dai jikina sai rawa yake don tare yake da yan sanda, yanxu haka daga can Mariri nake, uwarta na can hankalinta a tashe ko bacci bata yi ba sai koke koke, uban kuma yace da hadin bakin uwar Khaleesat ta gudu, babu kalan tijaran da Awdul bai yi ba jiya, keee abun dai babu kyau, ni dai hankalina ya tashi sosai, ina tsoron kar a gano ni na ajiyeta Awdul ya hadani da hukuma, shine na zo kawai ta shirya tayi hakuri ta koma gida duk abinda Allah yayi dai dai ne" Khaleesat dake jin duk abinda Gaje ke cewa ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah kar ki ce masu ina nan Baaba Gaje, wallahi har duka zai iya min" Maman Fu'ad dai na tsaye da atamfar mutane da zata yanka ta hau kan keke ta kasa cewa komai sai zazzare ido take, ita ma tsoro take kar daga karshe ace ai a gidanta aka boye Khaleesat, ta ina zata fara ma Baban Fu'ad bayani in aka zo tafiya da ita gashi bai gari, Gaje tace "Toh ya kike so inyi Khaleesah, Awdul fa ya maida maganar nan babban magana wallahi, wai kin tozartasa a cikin mutane jiya kin sa an tafi caji opis da shi, ba ki da kowa da zai tsaya maki a lamarin nan sai Allah, Malam Ali na can kamar zai haukace shi ma ya saka uwarki a gaba sai ta fito dake" Khaleesat ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kukan, Gaje ta make hannun Fu'ad dake ta jan yakunannen gyalenta sannan ta ja kujeran tsugunno ta zauna ta rafka uban tagumi tace "Ni dai ban san kuma yanda zan maki ba Khaleesah, ina talaka da ni Awdul yasa a daureni wa zai cece ni, sai ma Kinga kallon da yake min jiya kamar bai yarda da ni ba" Khaleesat ta dago da kyar tana kallon Baaba Gaje hawaye na sauka idonta, Baaba Gaje dai zai zazzare ido take tace "Ni ban ma yarda bai sa CID unguwar nan su kula da shige da fice na ba, yanxu hka sai da na zaga kamar zan je Yan kaba sannan na taho gidan nan" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Don Allah Baaba Gaje ki min alfarman dauko min jakana a can gidanmu" Baaba Gaje ta gwalo ido tace "Wani jakar?" Khaleesat tace "Karamin jakata, akwai wayata a ciki zanyi amfani da shi" Baaba Gaje tace "Um um Khaleesat, ta yaya zan dauko jaka ana gani na da rana tsaka?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Karamin jaka ne bai da girma, ko a gyalenki zaki iya boyewa don girman Allah ki rufa min asiri ki taimakeni Baba Gaje ki dauko min, har da kudi cikin jakan, zaki ga jakar kusa da akwatina a gefen katifar Umman mu" Maman Fu'ad dai sai baza ido take taji Khaleesat zata bar gidanta amma shiru bata ji ba, can dai tace "To ke ina kika nufa daga gidan nan yanzu?" Khaleesat na share hawayenta a hankali tace "Idan ta dauko min jakar zan san inda zan je in sha Allah" Maman Fu'ad ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, faridan ma bazata kira ba kar daga karshe a gane ita ta ajiye Khaleesat a gidanta ta shiga uku, Da kyar Baba Gaje ta yarda zuwa Mariri dauko jakan don duk a tsorace take, shi ma sai da Maman Fu'ad ta saka baki tunda taji ance in dai aka dauko jaka to za a bar gidanta, shi sa tayi ta lallaba Gaje taje Mariri dauko jakar, bayan kusan awa daya sai ga Gaje da jakar ta kudundunosa a gyalenta, Khaleesat ta amsa jakar ta bude ta ciro wayar Jay dake ciki, ta ga dollars din da ya bata suna ciki har sannan, Call log ta shiga sai kuma ta kalli Maman Fu'ad tace "Don Allah ki ara min wayarki bani da Sim card a nawa" Maman Fu'ad tace "Ai ko babu kati, tunda ga wayar Gaje bari in bada dari biyu a siyo sai ki saka a nata wayar ki kira" Nan duk dubara Maman Fu'ad tayi kar a ga Khaleesat tayi kira da wayarta idan bincike yayi bincike, Gaje ta mika ma Khaleesat wayarta ta fita ta amso mata katin dari biyun da Maman Fu'ad ta dauko ta bada, Khaleesat na saka katin ta fara dialing number Jay, ta kira yafi sau biyar sai dai kiran ya dawo mata alamar bai je ba, bata hakura ba still tayi ta kira baya shiga bata san ko katin ne yayi kadan ba kuma Number sa na Nigeria yake using a can din ma, wasu sabbin hawayen suka fara sauka idonta ta sake shiga call log din wayar tana scrolling slowly, number AJ ta gani shi ma Nigeria Line dinsa, ta
an yi jim tana kallon number, sai kuma tayi dialing tana share hawayen dake zuba idonta, ringing ya fara yi har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan yayi picking, muryarta na rawa tace "Good Afternoon" Shiru yayi, kafin yace "Wacece?" Ta sauke idonta tace "Ni ce" Yace "Ke wa?" Da kyar tace "Plss i want to speak to you" Kawai ta fashe da kuka uncontrollably, shiru yayi for almost 15 seconds, can yace "What happened?" Tana kuka tace "I need to speak to you pls" Ya kara yin wani shirun, can yace "Where are you?" Tace "Hotoro" He still kept quiet for some seconds kafin yace "Address" Katse wayar Khaleesat tayi ta tambayi Maman Fu'ad address din unguwan, Maman Fu'ad ta gaya mata sannan ta tura masa ta message, Gaje dake zaune kan kujera tace "Wanene wannan din da kika kira?" Ita dai Khaleesat tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Baba Gaje tace "Gashi idon naki sai kara ja yake yi, wallahi makantar da ke kawai yayi niyyar yi matsiyacin nan" Bayan kusan 35 mins wayar Gaje ya fara ring, Gaje ta mika ma Khaleesat da sauri tace "Ko wanda kika kira ne?" Khaleesat ta amsa tana kallon wayar taga AJ ne ke kira, dagawa tayi yace "I am outside" Khaleesat ta ajiye wayar sannan ta kalli Maman Fu'ad tace "Aunty don Allah kina da Nikab?" Maman Fu'ad tace "Yaushe rabona da Nikab, bani da shi yanzu kam" Khaleesat ta mike tana rike da handbag dinta da wayar Jay ta fita daga gidan, not far away from the house yayi parking, yana jingine jikin motar ya rungume hannunsa looking at a different direction, tana tafiya a hankali ta nufesa tana kallonsa, tana isowa kusa da shi ya juya jin Footstep, ya gyara tsayuwarsa ya dinga kallon idonta babu ko kiftawa, she tried her best na ganin bata fashe da kukan da ya taho mata ba amma ta kasa daurewa ta hade kanta da jikin motar ta fara kuka har da shessheka.
*Thanks for ur patient, and thank you all for checking up on me*
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
kema k
na cikin matan da kullum sedai su bawa miji abinci??
Ko kema kullum lunchbox na yaranki shinkafa ce?