Sashe 43
Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mahaukaci ne fa gayen kuma zai iya dawowa at anytime, it's already dark now" Jay yace "Nasani, but bazan iya barin ta ita kadai gidan nan ba" AJ yace "Are you her family member or something?" Jay yace "Kai da ka taho nan family member dinka ce?" AJ yace "Look Jay, Billah bazan bari ka zauna a gidan nan ba, koma wani taimako zaka mata kayi mata ni babu ruwana amma baza ka zauna a gidan nan ba, i can't risk leaving you here even for 1 second" Jay that was quiet for a while yace "Toh ka tafi, zan biyoka a baya" AJ yace "Kafata kafar ka Malam, kaji nayi rantsuwa bazan bar ka gidan nan ba, dubi kullin da ya dinga maka babu abinda ka tabuka sai sake baki kayi kana kallonsa" A hankali Jay yace "So kake mu hade masa at the end mu zo mu yi abinda za ayi da an sani, ai gwara da na kyalesa kawai kai ba gashi ka basa kashi yanda ya kamata ba, beside in muka ce zamu dokesa tare hakan zai sa mu gigita yarinyar ne" AJ yace "Aa haukatar da ita za mu yi ba gigita ta ba, pls do what ever you want to do ka fito mu tafi gida, ni yunwa ma nake ji" Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Wait for me outside then" Yana fadin haka ya juya ya koma dakinsa da Khaleesat take, AJ kuma ya fice daga parlon ya tsaya nan bakin kofa yana jiransa, bayan Jay ya bude dakin da makulli sai da yayi knocking sannan ya shiga ciki, tsaye ya ganta jikin bangon dakin hawaye na sauka idonta tana shessheka, ya tafi can jikin window ya tsaya yana kallonta, ita dai ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali, Calmly yace "Halysaah" Ta kasa daga kai ta kallesa, yace "Tell me how did you get to know this guy?
A ina ku ka hadu?
For how long ku ke tare da shi, kuma who is he?
Iyayenki sun san da alakar ku?" Sai a sannan ta daga kai wasu hawayen na sauka idonta tana kallonsa, ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "Where are ur reading material?
Suna dakin ki ne?" Kai ta gyada masa kawai, yace "Mu je ki dauka" A tare suka tafi dakinta, bayan yaga inda reading materials din nata suke ya karasa ya dauka har da laptop dinta, ya kalleta yace "Ina wayarki fa?" A hankali tace "Ya fada ruwa" Shiru yayi sai kuma yace "To mu je" Ta
an yi jim tana kallonsa, yace "Mu je mana" ba musu ta nufi kofa ya bi bayanta bayan sun fita ya kullo kofar, ita dai duk a tsorace take sai zare ido take tana ganin kamar Abdul zai sake dawowa gidan at anytime, ganin a tsorace take Jay ya shiga gaba yace "Follow me" Bin bayansa ta dinga yi hawaye na sauka idonta har suka fita daga parlon, har sannan Ajay na tsaye waje, ya juya ya kallesu, Jay ya nufi motarsa ganin Khaleesat ta tsaya yace "Mu je mana Halysaah" tana tafiya a hankali ta ci gaba da bin sa, back seat ya bude ya ajiye laptop dinta da sauran reading material dinta ya kulle sannan ya bude mata front seat, ta sauke idonta ta shiga motar ya kulle, yana kallon direction din AJ yaga har ya nufi gun motarsa ya shiga, zagawa yayi ya shiga driver seat ya tada motar, tuni AJ yayi zoom off, Jay ya bi bayansa.
A hankali Khaleesat ta sauko daga motar tana kallon Jay da shi ma ya sauka ya bude back seat ya dauko laptop dinta da takardu ya kulle motar yace "Mu je" Sauke idonta tayi ta fara bin sa a baya walking slowly har suka shiga parlon gidan, ya nuna mata kujera yana kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta zauna, ya ajiye laptop da takardunta dake hannunsa sannan ya wuce sama, ta bi sa da kallo hawaye na taruwa idonta, sai kuma ta fara kuka a hankali tana jin kanta na sara mata, Jay ya tafi dakin AJ yana bude kofar dakin yaji yana wanka a bandaki, hakan yasa ya tsaya bakin kofar dakin don baya son issue, yana ta tsaye da tunani iri iri a ransa har AJ ya fito bandakin, AJ na ganinsa ya dakata da goge gashin kansa da karamin towel yace "Me kake nema a nan kuma?" Jay yace "Ban sani ba" Sai kuma ya karasa cikin dakin that was extra clean, kan kujera ya zauna without looking at AJ yace "We need to talk AJ" Ajay yace "Shi ne sai ka shigo min daki?" Jay yace "Zauna mu yi magana"
an tsaki AJ ya ja yana ci gaba da goge gashinsa yace "Ina jin ka ba sai na zauna ba" Jay yace "I think my Housemate will stay here for a day or 2, before she sort her self out" AJ yace "As per you are her family member or who?
Bata da iyaye ne?
Ko nan din hotel ne?" Jay yace "Ban sani ba" AJ yace "No i am just asking a harmless question, like naga dai ba daga sama ta fado ba, kuma ba kai ka kawota America ba balle kace zaka samar mata solution, who are you to her?
Yayanta ko Ubanta?
Wanda muka mata ma Allah ya bamu lada, come off it Jawwad" Jay yace "Ai ba permission din ka na shigo nema ba Junaid, kawai sanar maka nake yarinyar nan zata yi kwana daya zuwa biyu a gidan nan kafin komai yayi settle" AJ yace "Toh ni na haifeka da zaka shigo ka gaya min zaka kawo yarinya tayi kwana biyu gidan nan?
Ai sai dai ka kira su Abba ka gaya masu, beside the house is very big with multiple rooms to accommodate her, so ni ina ruwana, i just pray u don't have to explain ur self one day" Jay ya mike ya fice daga dakin banging the door behind him, AJ ya tabe baki yana feshe jikinsa da turaren jiki.
Bangaren masu aikin gidan Jay ya nufa bayan ya sauko downstairs, ya basu umarnin da zai basu sannan ya dawo babban parlon gidan, Khaleesat dai na zaune ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da ta fada, ganin komai take kamar a mafarki, sai in taji tana da ta sanin abinda ya faru amma da ta tuna raping dinta Abdul yayi niyyar yi da Ajay bai zo ba sai taji ta nemi da ta sanin ta rasa, amma fa bata da nutsuwa bata da kwanciyar hankali, she was just restless and sick, bata san kuma me zai faru next ba a rayuwarta, muryar Jay ne ya dawo da ita daga tunanin da take ta gyara zama tana kallonsa a sanyaye, ya zauna kujeran dake kallon wanda take zaune yace "Bana son ki sa ma kanki damuwa Halysaah, ki kwantar da hankalinki pls kin ga kina da jarabawa a gabanki" Khaleesat ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara sauka idonta, Yace "Kin yi sallah?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk za a kawo maki abinci sai ki ci kafin mu yi magana" Ta girgiza masa kai tace "Bana jin yunwa" Yace "No, sai kin ci abinci ko ba yawa" Dai dai nan kukun gidan wanda bature ne ya taho da abinci zai kai dinning Area, Jay ya masa umarnin ya kawo parlon sanin abincin AJ na kan dinning din, dawowa kukun yayi Jay ya nuna masa inda zai ajiye abincin, nan ya jerasu a kasan lallausan Centre carpet, ya koma ya dauko sauran, bayan ya ajiye komai ya tafi Jay ya mike yana kallonta yace "Ki sauko ki ci abinci, let me pray" Ta gyada masa kai kawai, ya wuce sama sannan ta sauko kasa a hankali tana duba abincin da aka kawo mata taga duk abincin jajaye ne gashi abincinsu da yawa ita ba iya ci tayi ba duk shekarun da tayi a kasar su.