← Book details Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 180

Sashe 143

Halysaah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashin kunyan da ka saba yi min zaka yi a nan ma?" Ajay yace "Whatever, all i know is that u can't just be appearing in here without notice tare da wasu mutane can kina inconveniencing din mu kina sa mana ido" Wani murmushi kawai tayi ta kalli Khaleesat sannan ta juya ta fita daga dakin, gaba daya jikin Khaleesat yayi sanyi ta kasa motsi a inda take, after few seconds ta sauka daga kan gadon tana kallon Ajay da ya kafe ma dressing mirror ido yasan fitar da tayi Abba zata je ta kira, cikin sanyin murya Khaleesat tace "Why will u speak to her that way Ya Junaid?" Ya dakatar da ita fuska daure yace "Ba ruwanki Malama, kin san ta ne?" Khaleesat ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, ya juya ya fice daga dakin yana birkita gashin kansa, ga wani zafi da yake ji, where is he even going to start explaining this to his dad for the second time, gashi Jay baya gidan just him and the lady in the house, wani bayani zai yi ma Abba da zai yarda da shi?
angarensa ya nufa ya zauna gefen gado ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, in mahaifiyarsa ce ai sai dai su kashe su rufe tare da ita without her involving his dad in this issue, infact baza ma ta so wani yaji ba, he felt soo emotional, Aunty na komawa downstairs ta zauna kan kujera ta jawo jakarta ta ciro wayarta, Hajiya Usaina dake kallonta tace "Ya naga ranki a bace Fulani?" Aunty tayi wani murmushin takaici tace "Bari dai inyi waya da mai martaba tukunna Usaina" Tana fadin haka ta tafi dakin da take sauka ta tarar da jakadiyarta a ciki tana ta faman goge goge duk da dakin fess yake, zata fita Aunty ta mata alamar ta ci gaba da abinda take, sannan ta zauna kan kujera tayi dialing number mai martaba tana girgiza kafa at the same time tana fatan Allah ya sa ya samu damar daga kiran don zuwa yanxu dai tasan yana
angarensa shi kadai, ai ko babu jimawa ya daga kiran, bayan sun gaisa cikin ladabi da kwantar da murya tace "Allah ya taimake ka ya ja zamaninka, mun iso Maryland babu dadewa yanxu" Daga daya bangaren yace "To maa sha Allah fulani..." Ta kara yin kasa da murya tace "Amma Allah ya ja zamaninka ban ji dadin abinda na zo na tarar a gidan nan ba" Shiru Mai martaba yayi bayan yaji me tace, don tana fadin haka babu abinda ya fado masa sai abinda ya gani dakin Ajay kwanaki da ya sauka Baltimore, Jin Mai martaba yayi shiru Aunty tace "Ko kana tare da baki ne ranka shi dade babu sararin mu yi magana?" Calmly Abba yace "Ina sauraron ki" Aunty ta gyara zama tace "Mace na zo na tarar a dakin Yarima cikin wani yanayi mara dadin fade, hankalina yayi matukar tashi ranka shi dade, na dimauce ba kadan ba da abinda idona ya gane min, ban ji dadin hakan ba ko kadan wallahi, kuma da alama ba wannan bane karo na farko, ya saba yin hakan, Allah Ubangiji ya shirya mana su kawai" Mai martaba yayi shiru don sosai yaji abinda ta fada ya dake sa don har sai da ya jingina kansa da kujeran da yake zaune, tayi kasa da murya tace "Amma ba komai ranka shi dade kar hakan ya sa kaji babu dadi a ranka ko kuma ka damu, in sha Allahu idan na dawo sai mu san abun yi, mu san inda za mu billo ma lamarin don baza mu zuba ido a ci gaba a haka ba, kaga wannan big slap to our faces ne idan aka samu labarin abinda yake yi a kasar nan, hakan zai zubar mana da reputation din masarautarmu ne kawai, shi yasa kwanaki nace maka a samu yarinya me hankali da nutsuwa er manya a aura masa ko da kuwa ba er gidan sarauta bace, sai naga kamar hakan bai gamshe ka ba tunda baka ba maganar tawa muhimmanci ba na lura baka son yi masa dole ne, ni kuma abinda yasa na kawo wannan shawaran shi ne saboda shi Yarima ba kula yan matan yake ba a gida Nigeria" Cikin nutsuwa mai martaba yace "Bangaren nasa kika je?" Aunty ta
an fara kame kame tace "Ehh can na je ranka shi dade, gani nayi tunda muka shigo gidan ga dai motarsa amma shiru bamu gan sa ba, da yake kwanaki ai ya
an yi zazzabi saboda weather sai nayi tunanin to ko baya jin dadi ne, sai na karasa bangaren nasa, shi ne fa idona yayi mummunan gamon nan" Mai martaba yace "If possible try conversing with the lady u saw ki ji er wace jaha ce a Nigeria, ina son sanin background dinta, just Converse with her Fulani...." Aunty tayi shiru bayan taji me Mai martaba yace, can tace "Ranka shi dade ai ba er Nigeria bace matar, baturiya ce fa, kuma irin tsofaffin turawan nan, da kyar ma in bata haifesa ba" Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace "Na fahimta" Aunty tace "Yanxu dai idan na dawo za mu tsara komai ur Highness, ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu anyi na karshe, we will put a stop to this soon, kuma ko makusantan ka na fada don Allah kar ka gaya ma wannan magana, don ba magana bace da ya kamata ace ya fita" Mai martaba was quite, don tunanin da yake yi ma shi daban, daga karshe Aunty tayi masa sallama ya katse wayar, tana kallon jakadiyarta dake zaune kasa tayi murmushi tace "Mace na samu a dakin ba
i, amma ban san tun yaushe take zaune gidan ba ya dai ce min jiya ta zo gidan, sannan babu cin mutuncin da ya mance bai min ba" Jakadiya ta kara bajewa a kasa tace "Ja'iri, gaskiya ya kamata wannan karan ki dau mummunan mataki akan sa ranki shi dade kar ki dau lamarin da wasa, abubuwan da yake maki sun isa haka, duk baya ganin mutuncin ki kuma wannan abu na saka ni damuwa uwar gijiyata, yanxu dai kamata yayi ki kira daya daga ma'aikatan gidan ku kebe ki tambayesa ki ji tun yaushe ya ajiye yarinyar a gidan nan..." Aunty tayi wani murmushi tace "Kin kawo shawara kuwa...." Mikewa tayi ta fita daga dakin Jakadiya na jero mata kirari....

Bayan wani lokaci Ajay ya fito dakinsa ya tafi dakin da Khaleesat take, without looking at her yace "Ina jiran ki downstairs" Daga haka ya fita daga dakin, har zai sauka kasa ganin su Aunty a parlon ga uban kayan ciye ciyen da aka baje masu a tsakar parlon, sai kawai ya tsaya a corridor, a hankali Khaleesat ta mike tsaye ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fito, yana jin alamar ta fito ba tare da ya juya ba yace "Mu je, kuma ban ce ki ce zaki gaida kowa Downstairs ba" Daga haka ya fara sauka kasa tana biye da shi a baya jiki a sanyaya, tun da suka sauko Aunty da kawarta da Afrah ke kallon Khaleesat, Ajay dai ko kallonsu bai yi ba ya nufi kofa Khaleesat na biye da shi ita ma bata yarda ta kalli direction din su ba, gun motarsa taga ya nufa ya bude ya shiga, ta karaso gun motar ganin bata shigo ba ya daure fuska yace "Baza ki shigo ba?" A hankali ta bude seat din ta shiga, yana kallonta yace "Haka kika fito baki dauko komai ba?" Tayi shiru, sai kuma tace "Ai baka ce min in dau komai ba" Tsaki ya ja ya bude motar ya fita ya koma cikin gidan, ita dai ta bi sa da kallo, dakin da take ya koma ya dau laptop dinta da charger sai wayarta shima da Chargern sa sannan ya fita daga dakin yayi locking kofar yanda ba wanda zai bude ya sauka downstairs, nan ma su Aunty suka bi sa da kallo, Afrah kamar idanuwanta za su bi sa har compound din....

Har Ajay ya isa apartment din Khaleesat bai ce mata komai ba, ita ma dai tayi shiru da tunani iri iri a ranta, kana ganinta kasan duk a sanyaye take, bayan sun sauka motar ya nufi entrance din shiga apartment din ya ciro makullin a aljihunsa ya bude ya shiga parlon, ta bi bayansa.

Jay na zaune gaban mai martaba kansa a kasa yana jin duk abinda yake cewa, Cikin nutsuwa mai martaba ya ci gaba da cewa "I am so disappointed in you Ahmad, kana kallon abinda
an uwan ka ke yi amma ka kasa gaya min, i am really disappointed, even if you can't tell me directly there are other ways to approach me and i will understand you, to yanxu kana tunanin rufa masa asiri kake yi yana aikata sabo kenan?" Jay ya dago kansa a hankali, after few seconds murya can kasa yace "Abba ba abinda ku ke tunani bane, i promise you Junaid is doing nothing that is against the teaching of Islam, ba ma shi da lokacin da yake kula mata balle har yayi wani doguwar mu'amala da su, ka yarda da ni Abba bazan maka karya ba" Mai martaba dake kallonsa yace "Na je Maryland na ga mace a dakinsa, Auntynku ta je jiya and same thing happened, ta yaya zan yarda da maganar ka Ahmad?
Chapter 143 · 0% Book details